47- Saleem Da Saleemah

606 53 12
                                    

Sosai Mahboobah ta ji dadin yanda abubuwan suka kasance a Hukunyi, ta jinjina wa iyayen Ameerah matuka, domin kuwa ba kowa ba ne zai iya wannan halaccin da suka yi.

Mami ta mike ta musu sallama cewa za ta tafi yamma ta yi. "Hajia Mariya ba za ki jira Ishraq din ya tafi da ke ba?" Mommy ta fada cikin fara'a.

"A'a Maman Fareedah ban san ranar tafiyar wannan ba. Kuma yana iya cewa asibiti zai wuce daga nan, kar in shiga hakkinsa. Bari kawai in hau keke napep in tafi."

Mommy ta bata rai ta ce "Gaskiya ba za ki hau keke napep ba Hajiya, bari Aliyu ya zo ya mayar da ke, na san sun kusa gamawa."

"Me za su gama Mommy?" Fareedah ta tambaye ta.

"Idon matambayi."

Ta kwakkwabe baki, "Wayyo Allah Mommy bakar magana ma za ki yi min ko?"

"Iyyyeeee...lallai ma Reedah. Shagwaba nake ganin kina yi fa. An dai sha kunya." Mahboobah ce ta yi wannan maganar tana gatsine mata baki.

"Eh din ina ruwan wata, ai dai kowa ya san auta da shagwaba." Ta fada tana kara turo baki.

"Ga dai Baby Hoodah nan na kallon ki, na tabbata a ranta cewa take su Inna Reedah an ji kunya."

Dariya suka dauka su duka dakin, har da Haneefa da Saleemah da ke daidai shigowa. Suka gaishe da Mommy da Mami sannan suka tambaya ya mai jiki.

"Ni na yi fushi tunda sai yanzu za ku dawo."

Saleemah ta hau kan gadon kusa da ita, "Afwan yarinyar kirki, ga mu nan ai mun zo."

Mommy ta kira Aliyu cewa ya zo ya mayar da Mami gida ya amsa da to. Fareedah da Mommy suka taka mata har gaban motar Aliyu, ta musu sallama, Mommy ta kara yi mata godiya sosai sannan Aliyu ya ja motar suka tafi.

Noor na tare da Ishraq bayan an gama daurin aure su Doctor Ashraf sun tafi aka kira shi a waya da wata lamba. Bayan ya dauka cikin tashin hankali aka shaida mishi cewa matarshi ce ta bada wannan lambar ta ce mijinta ne a kira shi, sun tafka mummunan hatsarin mota a kan hanyar Mando, yanzu haka suna General hospital ma.

A kidime Noor ke ambatan sunan Allah kafin ya yanke wayar Ishraq na tambayarshi lafiya, ya shaida masa kamar yanda aka fada masa yanzu.

Tare suka kama hanyar zuwa asibitin, suka nufi accident and emergency, a can suka tarar da Sameerah kwance jina-jina, fuskarta duk jini. Salati Noor ke yi yana kallon yanda idonta guda yake a kumbure, gudan kuma a bude tana zubar da hawaye.

"Sannu Meerah, ashe tsautsayin da ya auku kenan." Kai ta jinjina masa tana jin wata irin nadama da tsoro na lullube ta. Lallai duniyar nan abun tsoro ce, mutum ba a bakin komai yake ba. Ko kadan ba ta kasance a cikin mata masu biyyar aure ba, ba ta taba damuwa da sai ta nemi izinin mijinta ba kafin ta fita, da Noor da banza duk daya suke a wurinta. Yau ga yanda rayuwa ta yi da ita nan, kafarta karaya uku, hannunta kuwa ba a ma san adadi ba, an yi X-Ray an dai ga karaya da yawa.

"Sameerah me ya kai ki hanyar Mando?" Ya tambaye ta yana gyada kanshi.

"Ka yi hakuri Noor..." kawai ta iya fadi da kyar, tana jin yanda hakoranta ke mata nauyi, komai nata ma jin shi take ba daidai ba, ciwo duk jikinta.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now