148

5.8K 302 1
                                    

Bangaren xuhura kuwa tun lokacin da umma ta kirata ta kasa samun nutsuwa, ynda faduwar gaba ke riskarta akai akai ta soma kwankwanto akan sadiq dinta kada dai wani abu ya samesane

duk ynda takira umma bata samu ta gwada layin faruq ma baya shiga, hr wannan lokacin idan ta kira number sadiq yana ringing baa daukaba, ta furxar da iska da qarfi daga bakinta jikinta ya soma rawa anya xata iya gani likita kuwa baxataje gida taga meke faruwa ba

noooo ai sadiq babban mutum ne tanada tabbacin duk abinda zai samesa dole xata gani a t.v ko jaridu, sannan ynda takeson haihuwarnan baxata iya komawa ba dan ganin likitan ma wuyane....da haka ta daina xancen sadiq sai dai tunaninsa nanan maqale a xuciyarta.

ummie fa馃

tun sanda aka shigo dasu emergency bata farfado ba sai lokacin da akewa sadiq theater cire bullet din dake jikinsa

ba ynda likitocin basuyiba akan a fitarda ita daga dakin taqi ynda ta kafe take kuka yasanya dr.bakori yace abarta

duk aikin da ake masa hannunta na maqale danashi, lokaci daya duk tafita hayyacinta idanunta sun kumbura ga jiriake damunta, suna haka suka soma ganin jini na fita bakinsa da hancinsa

duk wani qoqari nasu sun gaxa,hr wani weakness sukeji game da patient dinnasu bama kamar merah dake aikin yana sharar kwallah

yaya sadiq karka mutu,katashi ni xn ramama,xn harbesu su xasu mutu bakaiba,pls yaya sadiq.....ta fashe da kuka mai tsanani,lokacin ne numfashinsa na sauka merah ya fashe da kuka yafito hryake sanardasu

ganin dr.merah yafita yana kuka yasanyata bude idanuwanta sosai taf da hawaye tana kallon sadiq ta juya tana kallon dr.john frank, taga duk sun sunkuyarda kansu qasa, dr.bakori ma hawaye yake lokacin dayaja xani ya rufamasa hr fuskarsa,

me hakan ke nufi ta soma tmbyr kanta, ai taga ko a film ne akayi mutuwa haka ake masa a rufe fuskarsa da xani, ta bude idanu sosai tana kallon gawar da likitocin dake tsaye gurin

noooo ta fada da qarfi bayan ta fisge xanin da sukayi masa rufa dashi

yaya bai mutu ba,baxai mutu, yaya katashi sugani sunaso su kasheka,basu sonka nikadaice ke sonka,yaya katashi ni xan ramama ni xn kashesu pls yaya karka mutu, ta maida kanta qirjinsa tana kuka sosai mai narkarda xuciya

dai dai wannan lokacin ta soma jin nishinsa,ya soma tari sosai likitocin sukaxo da gudu cike da mamaki, ta dago tana kallonsa kafin ta maida kallonta ga likitocin tana fadin

yayana bai mutuba baxai mutu yabarniba idan ya mutu nima xn mutu,

tana gani suka sa masa oxygen, sukaje suka kira dr.merah cewa numfashin patient din yadawo

kamar a mafarki yaji ya juya da gudu xuwa dakin.......

Gen.umar yaja hannun faruq yana fadin
muje mu roqi Allah ya bawa sadiq lfy wannan shikadaine taimakon da xamu iya masa.

*10:00am*

Farfadowarsa kenan dr.merah na tare dashi, ummy na kishingide barci ya dauketa

ahankali ya soma furta ummie ummie, merah ya riqa hannunsa yana masa sannu

kamar a mafarki tajiyo muryarsa yana kiranta,da sauri ta tashi tana kallonsa

batasan sanda dariya na subulcemataba,ya juyo yana kallonta, da gudu ta fita dakin tana kiran umma...umma

sanda tafito mutane birjik sunyi cirko cirko wurin musamman duk yawancinsu soja ne kuma da bindigoginsu,

abinda yafaru baxai taba gushewa a idanuntaba,iya rudewa ta rude da ganin sojoji a wurin abinda batayi tsammaninba, ta saki ihu da qarfi tadawo cikin dakin duk ta rude, umma ta jiyo ihunta sai ta biyota da sauri

sadiq na kwance baxai iya tashiba amma ji yake kamar ya tashi ya rungumeta yaji dalilin raxanarta

umma ta riqo kafadarta tana fadin
x ok ummie bafa abinda xasu miki tariqa hannunta suka shiga ciki hr lokacin jikinta rawa yake ta tsorata ainun bata taba ganin yawan sojojin datagani tsaye a wurinba sai dai tagansu a t.v

umma tasaki hannun ummie taje ta rungume sadiq cike da farinciki,sai adduo'i take tofa masa ta jima ciki tare dashi kafin su general da momy da faruq su shigo, suma sun dan jima sosai aciki kana sauran manya manyan dasuke aiki tare suka soma shigowa.......

sadiq yayi mamaki ya kumayi matuqar murna da ganin wasu daga cikin abokansa, duk wannan abin da ake ummy na riqe da hannunsa tana murxawa kamar ynda taga yanayi mata,

bayan sun rage su biyu kadaine ya dubeta ynda ta dage tana murxa masa hannu

ummie me kikeyi haka?

tace yaya ina murxamane kamar ynda kakemin,ai naga kana sone? baisan sanda murmushi ya subulcemasa  ba yana kallonta cike da birgewa

tor ai ahankali akeyi bada qarfi ba ummie..

tayi murmushi tana kallonsa
tace tor yaya....tafara murxawa ahankali tana dariya.

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now