91-100

6.9K 266 0
                                    

Iya rudewa ta rude musamman datayi toxali da captain jabir idan baxaku mantashiba wanda ya taba tsoratata a hanya, fuskarsa baxata taba gushe mataba shikuma tunani yake inama yasan fuskar

kururuwar da xuhura keyi ya sanya sadiq nufar ta da kyar saboda azabar ciwon da kansa ke masa ya masa nauyi hrda stress k xamunsa

ya dago fuskarta goshin ya kumbura sundum sai dai bai fashe ba,
yace meyasa meki haka, da hannu ta nuna masa ummy dutsi ta jefeni dashi

juyowar da xaiyi tuni ummy ta rude ta saki kuka ta nufi talatu da gudu ta qanqameta tana kuka

sadiq yayi masu alama da hannu kan su fice kana ya saki xuhura yaje ya karbi ummy hannu talatu yayi part dinsu da ita tana kuka tana kiran

_mama save me plss_ talatu tace keni banajin abinda kike fadi ke komai sai kinsa turawa aciki tafice ko kadan bata kalli xuhura ba

yana isa dakinta da ita ya direta hade da rufe qofar
yau sai kin gayamin uban da yace kitabamin mata
tace tor wayace ta jima ciwo ai rama ma nayi
ya zaro mata ido ransa a bace
yace nasaki ne?ke yar mitsitsiya dake hr kin isa ki tare min fada, matata sa'ar kice ko kuma keta fasawa jiki

tace yaya inada qarfi duba馃挭馃徑aikak baka imata shiyasa baka rama ba

ya juya a fusace ya dauko charger yana nadewa,aikuwa idanunta sukayi raurau bata ankaraba taji saukar ta a bayanta,ta saki wani ihu hade da riqe bayanta
yaya kayi haquri,yaya fitsari....duk ta rikice ta soma kiciniyar cire sket dinta

yace kika cireshi anan sai na qaramaki goma

ta duqa qasa hade da hada hannuwanta tana roqonsa馃憦馃徏
pls yaya baxan sakeba, innallaha ma'as sabirin, yaya fitsari....ta tashi da sauri ta zage sket din tayi toilet da gudu, yana tsaye ta fito ya juya ya fice ta qaraso ta dauki sket dinta tana sanyawa tana kuka
sai nagayawa umma ta ramamin,shima yaya mugune,ta share hawayenta tafito falon lokacin anfara kiran magrib,

talatu tace kiyi sallah maganinki kenan, ta tunxure bakinta tashige cikin labule ta boye ita baxatayi sallar ba tunda yaya ya daketa,tana kallo talatu ta shige dakinta ta sauko taje ta dauko ice-cream dinta ta zauna tana sha

saukowar talatu ta tsuramata ido
tace ummy bakiyi sallah ba,maza kitashi, tatashi tana tunxure tunxure ta fice....,

dawowarsa daga masallaci yayi daidai da saukowarta bayan tagama sallah, hannunta a baki ta sadda kanta qasa batason kallonsa ta sauko

tanaji talatu nayi masa fada akan yaje ga matarsa xaman aure sai ana haquri da mata.....

ummy na takure cikin kujera tana jinsu, hannunta a bakinta,shi duk hankalinsa naga ummy ynda ko kallonsa batayi kenan fushi takeyi dashi,ya dauke dubanshi gareta lokacin da talatu ta nufi kitchen
[7:38AM, 7/15/2016] Pherty馃帳馃懐: ta juyo tana kallonsa fuska a marairaice,duk taji ba dadi tunda bata kwance a jikinsa kamar ynda tasaba,jikinsa yariga ya xamemata garkuwa,tayi narai narai da idanu sanda suka hada ido,yayi saurin dauke kansa daga gareta

talatu tace ke ummy kixo kici abinci....ta soma share hawayen fuskarta ni bana ci.....sadiq ya juyo yana kallonta kuka take marar sauti tana share hawayen da rigarta

tace kekika sani, sadikku anan xn kawo maka naka ne,ya gyada kai yana kallonta,kasa jurewa tayi ta tashi ta langabar da kanta tana kallonsa shima ta gefen ido yake kallonta,a hankali take tfy kamar mai tsoronsa hrta iso inda yake ta fada jikinsa

yaya kayi haquri
ya sauke ajiyar xuciya hade da rungumota a jikinsa.....ummi ta zama wani bangare na xuciyarsa

bayan sun gama cin abinci ya tashi ya nufi sashen xuhura, tayi kuka idanunta hr sun kumbura tayi tsananin nadamar abinda tayi, yana tsaye qofar dakinta yana kallonta itama shi take kallo,kafin ya juya zai bar dakin ta taso da sauri

sadiq.....ta kira sunansa,bai amsaba bai kuma waiwayoba illah tsayuwa da yayi, ta iso da sauri ta bayanshi ta rungumeshi tana kuka mai tsuma xuciya hr cikin ransa yakejinsa,

hr qasa ta durqusa tana roqonsa abinka da mata da miji ance sai Allah,nan da nan xuciyarsa nayi laushi ya juyo da ita ya rungumeta aikuwa ta qanqameshi kamar xata koma cikinsa

da kyar ya iya saisaita riqon da tayimasa
yace kije kiyi wanka xuhura.....a raunane tace kaifa,yace nima ynxu xnyi,tace baka haqura ba kenan,yaja haanunta suka fice.

*

Washe gari bayan dawowar ummy daga skul,uniform kawai tacire ta dauki tedy dinta ta fito harabar gidan inda take wasa,

ta ajiyeta a qasa taje ta debo flowers da duwatsu tana jerawa anan qasa, xaune tayi dirshan tana wasar tana surutunta duk ita kadai,shima sadiq dawowarsa kenan sai dai baibari sun haduba saboda uniform dake jikinsa

ganin zuhura tayi tafito da sauri ummy ta tashi xata gudu
tace ke ummy! ta juyo tana kallonta
tace kinsha ice-cream yau,da sauri ta girgixa kanta tana kakkabe hannuwanta da qasa
tace meyasa baki shaba? cikin shagwaba
tace yaya bai siyomin ba
tace kinaso kisha, da sauri ta gyada kai tana kallonta
tace tor xoki gani,ba tsoro ummy ta matso xuhura ta riqe hannunta
tace kije dakin yaya ynxu xn nuna miki ki shiga ki bude drawers ki kwaso duka kudin kixo muje mu siya kinji
tace tor riqemin babyta
tace a'a kije da ita, tajata ta kaita dakin sadiq ta nufi dakinta da sauri lokacin sadiq ya soma balle aninin rigarsa

tace cwt karka cire uniform din akwai matsala, ya juyo yana kallonta fuskarsa da alamar tmby
yace wacce matsala kuma?
cikin yanayin tsoro tace kamar naga mutum ya shiga dakinka indai ba barawo bane, yayi hanyar fita tace ga bindigarka kaje da ita bakasan wane irin mutum bane daka shiga dakin ka rumtse ido kawai kasaki bullet

yayi murmushi yace angayamaki a banxa ake harbi,akwai abinda zai tsoratanine tor amma ina duka sergent dindake gidannan sai ya fice kai tsaye dakin ya nufa xuhura ta kashe kunne taji tashin bindiga

tsaye yayi cike da mamaki ganin ummy durqushe bakin drawersa sai surutu take
yaya ya xama barawo,ina yasami kudi sai nagayawa umma,ta kalli tedy dinta tace kiyi shiru inje insiyo maki ice-cream da kayan wasa,musiyo mota inkai momy asibiti abokin yaya ya gyara mata qafafunta........duka kudin ta kwashe ta xuba a rigarta komai bata bariba da kyarma ta tashi kamar xata fadi,ta rasa ynda xata dauki tedy

tace karkiyi kuka inje indawo in d.......mgnrta ta maqale lokacinda idanunta na sarqe danashi,yana tsaye cikin uniform dinsa ya xuba mata idanuwa,lokaci daya ta saki rigar duka kudin suka xube qasa,numfashinta na soma sarqewa sanda tayi tozali da bindigar dake hannunsa

ya soma taku ya tunkarota,ta rumtse idanunta cikin tashin hankali da tsoro jikinta hr rawa yake

wata irin faduwar gaba ta risketa lokacin dataji yaja kunnenta,tsananin tsoro da firgici yasa numfashinta daukewa,bai fahimci hakan ba sai da yaga ta fadi ragwaf kanta ya bigi bedside.............

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now