131-140

6.8K 274 4
                                    

Umma tabishi da kallo har ya xauna,

tace son ina xuwa haka da wannan kwalliya ansha kyau haka ko xakaje daurin aurene?

yace umma wane daurin aure kuma nida nake ango amaryata zaa bani yau xamu koma abuja.

cikin rashin fahimta ummi ta dago tana kallonsa kafin ta maida kallon taga umma dan jin mexatace

umma tace amma son.......yayi saurin katseta cikin wani yanayi _is a promise umma kada kisaba pls nayi maki biyayya kiyi haquri plssss_ taja numfashi tana kallon ummy

tace kije ki shirya ku tafi Allah ya kaiku lfy

cikin rashin fahimta
ummy tace umma bafa nice amaryarba ni qanwarsace fa,

tace ke *MATAR SADIQ* ce ummy ai ba shaqiqinkibane akwai aure tsakaninku tun kina yarinya, ta saki wani ihu a dimauce bayan ta xaro idanuwanta tana kallonta tace umma ni, yaushe akayi haka,ni banason auren

wani baqinciki ya tasowa sadiq a xuciya ya tsura mata ido ynda take kuka kamar ranta yaji haushin abin kamar wacce aka hada da maqiyinta duk shaquwarsu da kulawarsu duk ta manta a ynxu

cikin kuka take roqon umma,
umma ba soyayya tsakaninmu sai shaquwa, bayan soyayyar jini ba wadda ke tsakaninmu,umma kiraba auren ko kuma kice wasa kikemin,

umma ta riqo hannunta a sanyaye hankalinta atashe abinda tayi gudu kenan

tace xauna inbaki lbr ummy bakisan komai akan aurenkiba cos lojacin kina yarinya shima sadiq bashi yace yanasoba nina hadaku saboda wani qudiri nawa.......(hrta bata lbrn komai da yarintarta da kafuwarda tayi akan sadiq din馃)

shima sadiq sai jikinsa yayi sanyi baisan komai akan ummi ba sai yau sai yaji wani sonta na qara darsuwa a xuciyarsa amma fuskarsa na nuna alamar bacin rai ga kalaman ummi

tace umma wannan yarintace umma bansan kainaba umma, meyasa akamin aure aka auramin mai mata umma, matarsa muguwace umma ni banason auren ta tashi ta fice da gudu tana kuka umman tabi bayanta

a daki tasami mominta ta sadda kai tana kallonta
tace momy kinasona kika bari akamin auren yarinta aka auramin yaya sadiq kunaso ku bata xumuncinmune umma meyasa kika yarda meyasa kika bari aka auraminshi

ta dora kanta a cinyoyinta tana wani irin kuka gwani ban tausayi kukane mai tsuma xuciya hr momin jikinta yayi sanyi dai dai lokacin umma ta shigo

momi ta dafata
tace ummy kina tuhumarmu da yimaki auren da bakiso,auren dan uwanki,kiyi haquri alheri muke nufinku dashi baxaki ganeba sai nan gaba idan kin gano gatan da mukayiwa rayuwarki

cikin kuka tace kuyimin alfarma umma da momy, shima yaya sadiq ba sona yakeba kamar yanda kukace auren hadine kuka mana, matarsa bata sona,umma tagayamin nasha duka gunta,banida raayin auren mai mata momy bantaba wannan mafarkinba, sannan a yanda yaya sadiq keson xuhura baxai tabamin irin sontaba,matarshi tabgirmeni umma tafini sanin aure da abinda keciki,umma idan naje na xauna da ita xata kasheni ku sauyamin wani mijin amma ba yaya sadiq ba ta cigaba da kuka

momy tace kiyi auren BIYAYYA ba SOYAYYA ba,kiga wacce irin riba xaki samu acikinsa,idan mun san babu riba baxamu baki jarin ba

umma tace ummy kowacce mace dakika gani da kissarta aka haifeta sanna kowacce da yadda Allah ya halicceta sai dai ra'ayi da aqida sun banbanta amma fa duk sunansu daya MACE  kuma abinda ke cikin wannan shike cikin wancan ba wadda tafi wata a matantakarta sai dai ko qaxama da marar tsabta ballaatana ke ummi kina da tsabta wayewarki ba daya da zuhura ba kuma a ynxu xuhura bata isa tasamaki hannunba kinada gata gaba da baya munfisonki akaata baxamu bari ki cutuba

ba abinda ke birge namiji kamar HANKALI da CIWON KAI wannan ma ya isa ya kwatomaki girma a gun mijinki _maintain ur own qualities ummina kada kiji tsoron kishiya_

Namiji dan reno ne ummy, kuma kulawar MATA yakeso shi xai kwato maki soyayyarsa a zuciyarsa, kitashi ki shirya ki goge hawayenki bakida matsala da aurenki da sadiq idan kuma akwai kiyi gaggawar sanardani ki cire tsoron xuhura a xuciyarki,kema macece kamar ita.....ta tashi ta fice

ummy ta share hawayen fuskarta duk taji umma tacire mata _inferiority complex_ hartaji xata jure duk wani hali da xata tsinci kanta a gidan koda ace batason sadiq din shima bayason(kowa yagayamata sadiq din baya sonta馃)

abu dayane ya tsaya mata a zuciya

_kulawar MATA yake neman ta tuno furucin umma na qarshe_

wace irin kulawa umma kenufi nabashi, _he is old enough ya kula da kansa_ wanka xn mishi ko pampers xn cire masa?goyonshi xnyi ko feader xn bashi馃 bansan wacce irin kulawa take nufi ba....(kuji ummi da wani xnce tunda ya reniki kema dole ki rainesa lol)

ta shafe hawayenta da bayan hannunta bnda girki dataji ana fada anayiwa miji in xaa kasheta batasan wata extra kulawa ta dabaa da mace keyiwa mijiba sannan bata iya shishigi da cusa kai inda tasan batada kwarjini kuma bata da  yaqinin yanasonta ko baya ya sonta,momy ta katse mata tunani

momy tace kiyimin alqawari xaki xauna lfy da mijinki,kiyimin alqawari xakiyi mishi biyayya,kiyi min alqawari xaki jure kibashi soyayya kamar ynda yake sonki,duk abinda yayi maki kiyi haquri kibarshi kiyi masa uxuri ummy,sakayyarki na wurin ALLAH..!

ummy ta gyada kai tana murmushin yaqe xuciyarta sai xafi take tace

_i promise you umma_ ta juya tafice da sauri tana hawaye.
[9:41PM, 7/18/2016] Pherty馃帳馃懐: sanda tafito hr an gama hada kayanta ana shiga dasu booth, duk girman nan na ummy batabar wasa da tedy ba cos tanasonta a xuciyarta olways xaka sameta da manya manyan tedy ta jera a dakinta, tajevdakinta tasamu duka umma tayi mata parking dinsu ta dauko hijabinta ta sanya tafito hr lokacin hawayene ke xuba idanunta

a harabar gida umma ta dubeta
tace ummy kukan bai isa bane danan da can duk dayane kisa aranki ba aure kikajeba zama kikaje gidan yayanki

cikin kuka tace tor umma baxaa jeda talatu bane?

umma tayi murmushi tace ynxu da da ba daya bane ummy, amma idan kin kwana biyu talatu xataxo kinji,

ta gyada kai ta juya tana kallon momy kafin ta juya da sauri taje ta shiga motar gidan baya inda taga sadiq din ya shiga cos driversa xai ja motar, tunda tashiga motar tamaida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai kamar ranta, hr motar ta daga tabar gidan.

*
sunyi nisa sosai a tfyrsu amma bata daina kukanba abin na qarawa sadiq haushi a xuciyarsa ynda sukayi sabo da juna ta waya da chrtng amma ace ummi ke gudunsa haka

ya saqala hannunsa cikin hannunta yana murxa ahankali, nan take jikinta ya dauki rawa jin reaction dinta ya canxa abinda bata saba bane,ahankali tasoma rage sautin kukanta sai dai taqi karbe hannunta daga nasa batasan daliliba,

yana riqe da hannunta hr suka iso a harabar gidan sukayi parking, fitowarta daga cikin motar yayi dai dai da dagawar labulen xuhura tana rege, sai da gabanta yafadi da ganin sadiq dinta da zuqeqiyar budurwa haka musamman dataga ana shigarda kayanta dayan sashen, tor wacece wannan kardai sadiq dinta wani aure ya qara gabanta yayi mummunan faduwa ta fito da sauri

qasa qasa yake kallon ummy,kije ga sashenki can,akwai yarinya qarama daxata tayaki xama saboda kewa,kici abinci kiyi wanka komai kike buqata akwai a gidan,idan nasami lokaci anjima zan shigo ya juya yafice tabishi da kallo,inma yasamu lokaci kenan ita tasan wulaqanci iri iri xata gani itama ranta abace ta nufi sashen....

kicibis sukayi karo da juna a falo jikinta hr rawa yake

tace sannu da dawowa ya hanya?
ya amsa da lfy yana dubanta, lfy kike kuwa?
tace wacece na ganku kunxo tare ynxu,ya ware idanunsa sosai yana mata duban mamaki
yace ummy ce
wacce ummin ta tambaya a tsorace saura kadan ta fadi
yace *MATAR SADIQ* ya juya yafice tayi xaune dirshan xaiga xufa na karyomata kamar maishirin haihuwa

ummice ta koma haka, yaushema tadawo batada lbrn dawowarta, chabdi ashe akwai xama dan wlhy sai tabar gidan, nikadai nakeda sadiq, sadiq nawane kuma nikadaice *matar sadiq*........

ummi fa馃.......
ku biyo pherty danjin ya zaman xuhura da ummi xai kasance a gidan sadiq,wacece *matar sadiq* acikinsu?

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now