158

5.9K 273 0
                                    


$un dade suna rigima da ita kafin ya soma dariya yana tsokanarta,

ta bata fuska tayi shigewarta tana fadin
xngayawa umma ne dan baxan yardaba....

Tun daga lokacin sadiq ke qara kulawa da matansa gwargwadon iyawarsa, kowacce yana qoqarin nuna mata matsayinta a zuciyarsa da kuma abinda take dauke dashi a jikinta,

Alhamdulillah gwargwado xuhura na qoqarin sanya ummi a jiki da nuna mata ynda xata tafiyar da rayuwarta saboda taga ummin akwai qurciya sosai a tare da ita at d age of 17.

duk sanda xasu fita tare haka yake hadasu yaje suyi siyayyar kayan jarirai kowa duk abinda takeso xata dauka, baitaba tirsasa masu akan sai sun dauki abu iri dayaba sai dai kowacce ta dauki xabinta ya biya.....

cikinsu nada wata biyar umma ta aikowa ummi talatu dan kula da ita,cikin ya rinjayi qibar ummi sosai ga kumburi da qafafunta da jikinta keyi, amma xuhura komai normal, shiyasa yake tausayawa ummin yake sanyata gaba suje exercise wani sa'in hrda kuka take masa ita baxata iya daukar kantaba baxata iya tashiba,sai ya kama mata.....

sanda cikakkansu nakai wata tara su umma da momy suka dawo gidan, ba sonkai suke kula da xuhura kamar ynda suke kula da ummi, komai tare suke masu na kayan kwadayi haka irin namai ciki, itama xuhura hrta saba da xama tare dasu, sai dai duk wanda ya kalli ummi sai tabashi tausayi saboda cikin ya rinjayi jikinta anyimata scanning abu dayane aciki,

ga wahala da take wurin tashi ko xama, komai bata iyawa sai anmata, idanma awo xasuje yana dauke da jakarta ya riqa hannunta xuhura na bayansu tana masu dariya, abincima bata samu taci sosai...shiyasa duk sanda suka kebe sai tayi masa kuka

ita batason cikin suje a cire, bataso ta mutu ynxu, duk ynda yakeson yin dariya xai gimtse saboda da gske take mgnr hr cikin xuciyarta

gobe xamuje asibitin sai acire a sanyamin tunda ummi bataso a ynxu, ta soma share hawayen fuskarta tana qoqarin kwanciya, ya kama mata ta kwanta tana kallonsa
tace yaya hrda cikin baxan qarayiba, baisan sanda dariya ta subulce masa ba, ya sunkuyo a hankalin yana kallonta kafin ya rada mata wani abu a kunne(secret馃槣)

ta dubeshi da murmushi xatayi mgn, ya dora yatsansa a bakinta yana fadin kiyi shiru ummie, sirrine bana son pherty taji ballantana ta watsawa fans dinta馃槖

tace yaya yau baxakayimin tausa bane?
yace ai ban mantaba ummie ynxu xn maki.......

*2 days*

Wayewar safiyar xuhura ta soma tashi da naquda, bata nunaba saida abin yaci tura ta kasa motsa ko qafafunta,

ganin ynda xuhura ke juye juye tana hawaye ya tsorata ummie,ba abinda ya qara tsoratata kamar jinin dataga na xubarwa xuhura shiyasa suna isowa asibitin mararta na riqe ta kasa tfy, ciwo ya taso mata gadan gadan sai ta saki qara jitayi kamar xata mutu....,

iya rudewa sadiq ya rude, matansa biyu a labour.....

sai faman xirga xirga yake jikinsa hr rawa yake, safa da marwa yake acikin asibitin hannayensa duka biyu goye a bayansa, bnda addu'oi dayake ba abindake fitowa bakinsa

suma haka iyayen mata ba wadda tayi qarfin halin xama duk suna a tsayene..., binni binni faruq ke bugo waya yaji ko an sauka duk amsa dayace ba wadda ta sauka,

kusan rabin awa kafin merah ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa

sadiq ya nufi wurinsa da sauri
yana fadin hr ynxu ba wadda ta saukane,

merah ya miqa masa wata farar takarda akan yasa hannu dole sai anyiwa daya c.s baxata iya haihuwa da kajtaba saboda yaron cikinta bai xaune ynda yakamata,

baisan ko waceceba acikinsu amma jikinsa a sanyaye ya sanya hannu, merah ya juya da sauri

umma tace dama nasan ummi baxata iya haihuwar wannan ciki ba saboda girmansa ya Allah ka tada kafadunsu ka saukesu lfy,

wannan karon sadiq ya kasa tsayuwa saboda qafafunsa dake rawa hr jiru yake gani saboda fargaba ga wani weakness dayakeji

sun shafe kusan awa biyu hr lokacin ba wani information daga likitocin akan
masu haihuwa

suna tsaye wata nurse ta fito
wai sadiq yaxo inji dr.merah, jikinsa hr rawa yake ya shiga labour room, ga mamakinsa yaga ummi ta haihu da kanta lfy ana gyarata...

merah yaja hannuwansa hr inda xuhura take kwance anyi mata c.s anfitar da diya mace

jikinsa yayi sanyi ynda yaji numfashin xuhura ke fita sosai da sauri ga hawaye na xuba a idanuwanta ya dubi merah yana fadin

bangane ba miye dalilin kirana alhali baku gama gyarataba kada dai xakucemin wata matsalace

ta riqo hannun sadiq tana kallonsa
ninace su kiraia sadiq......ya juya yana kallonta
tace mutuwa xnyi sadiq, baxan tashiba naji ajikina, naso na rayu dakai da ya'ta kamar ynda nayi buri amma Allah bai cikamin ba,haka rayuwa take kana naka Allah na nashi ba wanda yasan gaibu ko yasan gobe, Alhamdulillahi Allah ya cikamin daya daga cikin burina yabani haihuwa naga ya'ta sai dai baxan rayu da itaba......

iya rudewa sadiq ya rude, cikin tsawa
yace wai waye ya gayamiki ciwo mutuwane, meyasa kikeson tada hankalina,meyasa kikeson ki barni duk wadannan maganganun naki kiriqesu dan nasan xafin ciwone.....

tayi murmushi tana lumshe idanuwanta hawaye na kwaranya kamar da bakin kwarya
[12:13AM, 7/31/2016] Pherty馃帳馃懐: tace kabawa ummi ya'ta ta hada da nata ta riqe amana kagayamata ta riqemin ita amana ba riqon *Yar kishiyaba*, naso na reni nawa da nata amma Allah bai nufaba, ka sanyawa ya'ta sunana sadiq, kullum kagayamata inasonta kuma naso na rayu da ita, kai da ita da duk masoyana sumin addua..ta qara matse hannunsa cikin axabar ciwo da alamar fitar rai馃槶

ina sonka sadiq,ina sonka, ashe baxan rayuwa da sadiq dina ba, sadiq dina banawa bane na ummine, ashe ummi kadaice *MATAR SADIQ* banda ni xuhura, ashe duk kishina da fadana baxan rayu da sadiq dinaba....ta fashe da wani irin kuka mai narkar da xuciya馃槶(nima pherty ina gefe ina taya qawata kuka, sorry qawa dont mean to hurt you just to knw dat bakomai kake nema kasamu a duniyaba, ba kuma komai yake tabbata nakaba, illah wani rabon *AJALINE* haka kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.),

sadiq ya russuna ya sumabaci goshinta
'''"you will get well soon fatyma-xuhura, yarki kexaki kula da ita, xafin ciwo yakesaki irin wannan mgnr鈥︹€︹€''

ta girgixa kanta ta qare manne hannunsu
tace SADIQ-UMMIE馃槶

Sanda tafara gasping merah ya fito dashi da sauri yana kuka, kuka yake bilhaqqi kukan dana tsorata su umma sukayo kansa shima faruq din yaxo

tun kafin yayi magana momy na fara kuka tasan babu ummi,

faruq kuwa xubewa yayi qasa dan qafafunsa baxasu iya daukarsaba baisan yaxai kasanceba idan ummi ta mutu,

umma tace waye babu Abubakar, yaran ko iyayen?

a hankali ya furta xuhurace umma, na rasa xuhura umma, macen dana fara so a rayuwata shekara goma am with her,ban taba tunani mutuwa xata rabamu a ynxu ba,inasonta fiye da tunaninki,nafison ta rayu akan yarinyar da xata ba......umma tayi saurin toshe masa baki itama jikinta rawa yake takasa gasgastawa
tace kada kayi ixgili sadiq, k.......tayi shiru sakamakon numfashinsa dana dauke..... wayyo Allah xuhura馃槶 _R.I.P_

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now