AYUSHA

242 4 0
                                    

*ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢ

*~AYUSHA~* 👥

HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)

©️Fertymerh Xarah💞

1

Amin ya rabbi, ya faɗa a hankali yana kallonta cikin tausayawa, itama kallonsa tayi cikin murmushi tace,

Lafia wannan kallon haka?
Lafiyar ce ta kawo hakan, ya maida mata martani kafin ya riqo hannunta ya qara tausasa muryarsa kamar yana tsoron wani ya jiyo abinda yake faɗa,

Yace Nagode sosai da addu'ar da kike min a ko da yaushe, haka nima bana gajiya da yi maki addu'a Allah ya sauke ki lafiya naga kin haifa min mace irin ki mai haquri da yakana.

Tayi murmushi tare da faɗin mace kamar ni ko namiji kamar kai duka abin sone Allah ya bamu nagari mu basu tarbiya irin wacce xata xamo abin alfahari ko bayan rayuwar mu.

Hakane ke ɗin ta daban ce Halimatu, komai naki daban ne da sauran mata, ni xan tafi kasuwa ki tabbatar da kinci abinci kuma kin kwanta kin huta sosai idan akwai wata matsala ko kina jin wani abu ki kirani da sauri dan Allah.

Tace insha Allah, tana kallonsa ya shige motarsa ya bar harabar gidan, taja numfashi a hankali saboda qarfin haline kawai take kada ya fuskanci halin da take ciki ya tayar da hankali har yaƙi xuwa kasuwa yau, da kyar ta iya ɗaga qafafunta ta juya.

Kamar da wasa awa uku bayan fitar mijinta ciwo sai qara gaba yake, ta duba time ko yanxu akwai awa ɗaya xuwa biyu kafin dawowar sa anya xata iya jurewa kuwa, kodai xata ɗaga waya ne ta kirasa kamar yanda yace idan taji akwai matsala, ta dafe cikinta tare da rumtse idanunta cikin matsinanciyar ciwon mara.

*

Alhaji safiyar yau tunda ka fito kasuwa banda murmushi babu abinda fuskar ka ke nunawa a yau, anya wannan farincikin naka baya da nasaba da samun wani babban kyauta kuwa?

Kallonsa yayi kafin yace a duniyar nan akwai wata kyauta da tafi haihuwa kuwa, farinciki nake ji a kowane lokaci matata xata iya haihuwa saboda ta shigo watan haihuwar ta, kai shaidane shekarata goma da aure ban taba haihuwa ba sai wannan karon Allah ya dubemu to meyasa baxanyi farin ciki ba?

Malam Bala yace hakane banga laifin ka ba Allah ya baka ya'ya rayayyu, amma wannan abinci tun ɗaxu ka sanya aka karbo mana shi naci nawa kai kuma har yanxu baka ci ba.

Wlhy malam bala sam na manta da na sanya a karbo min abinci haka kawai bana jin yunwa nishaɗi kawai nake ji a yau kaga bari ma na kira madam naji ko ta samu taci abinci kasan idan bana kulawa ba damuwa tayi da cin abinci sosai ba.

Murmushi kawai malam bala yayi batare da yayi magana ba, inda sabo ya saba da halayyar abokin kasuwancin sa tun lokacin da mai ɗakinsa ta sami juna biyu.

Da kyar ta ɗauki wayar dake kusa da ita ganin wannan shine karo na uku da wayar tayi qara batare da ta dauka ba.

Lafiya ina ta kira wayar baki ɗaga ba, abinda kawai ta iya ji daga can bangaren, ta maida wayar ta ajiye saboda wani ciwo da take ji.

Hello ! hello !! hello !!! Kina ji, meya same ki, waye akan layin? Ya soma jero tambayoyi barkatai cikin kakkausar murya mai dauke da damuwa, xumbur ya tashi babu takalmi a qafarsa xai shiga mota malam bala yayi saurin tarosa.

Haba Alhaji ai ko menene ya faru ka tsaya kayi min bayani ba wai ka fice da sauri haka ba, menene ya ɗaga hankalin ka haka?

Yace nima ban sani ba amma jikina yana bani babu lfy, dan haka xanje na duba matata.

Yace to ai ko xakaje yanxu dole sai ka tsaya ka rufe store ɗinka.

Kai gaskiya malam bala baxan iya ba, ka taimaka ka kula min da yaran shagona idan lokaci yayi ka rufe min ka bawa ɗaya daga cikin su key ya zomin dashi gida, bai saurari malam bala ba ya shige motar.

Malam bala girgixa kansa kawai yayi yana kallon ikon Allah.

Subhanallah ya faɗa jikinsa na rawa ya isa gare ta, dama baki da lafiya shine baki sanar dani ba, ina kika ajiye kayan da kika tanada domin xuwa asibiti? Yatsa ta ɗaga da ƙyar ta nuna masa inda qaramar trolly da hanxari yaje ya ɗauka ya fita dashi xuwa mota.

Sai safa da marwa yake tun da suka xo asibiti ya kasa zama wuri ɗaya, ya kasa nutsuwa sai zufa ke karyo masa wanda baisan dalilin haka ba, wayarsa dake gaban aljihun rigarsa ta ɗauki qara, cikin hanxari ya ciro ya karata a kunnesa batare daya duba mai kiran nasa ba.

Assalamu Alaikum, aka faɗa a ɗayan bangaren, jin muryar da ta doki kunnensa ya saka shi ajiyar xuciya tare da faɗin Wa'alaikissalam.

Lafiya naji muryar ka kamar baka cikin nutsuwa, da kyar ya amsa masa da wallahi yaya halimatu ce ba lafiya tana ɗakin haihuwa awa biyu yanxu da mukaxo asibiti har yanxu babu wani labari.

Masha Allah ashe lokaci yayi, ba damuwa xakayi ba addu'a zaka mata Allah ya sauke ta lafiya ka kwantar da hankalin ka naji duk ka ɗaga hankali.

Yace ai dole ne yaya amma zanci gaba da yi mata addu'a kamar yanda ka faɗa.

Murmushi Alhaji Abdallah yayi kafin ya tsinke wayar yana kallon matarsa da yar'sa da suka kafe sa da ido alamar tambaya.

Halimatu tana asibiti ta kusa sauka insha Allah.

Ihu Annam ta saki cikin tsananin murna da jin daɗi tace yeeeh Abba dani xaa je sokoto naga sabon baby ɗin mu.

Mahaifiyarta ta tabe baki cikin halin ko in kula tace tunda qanwar uwar kice xata haihu ko, ba inda xakije sakarya.

Annam ta tunxuro baki tana kallon mahaifiyarta cikin jimami hali irin na mahaifiyarta batasan dalilin daya saka bata ƙaunar momin sokoto ba tunda ta girma ta taso take ganin wannan qiyayyar a idon mahaifiyarta.

Alhaji Abdallah inda sabo ya saba da hali irin na matarsa akan halimatu, shiyasa wannan furucin nata baiyi mamakinsa ba illah ya dubi Annam tare da faɗin.
Insha Allah tare xamu je,bara naje nayi mana booking jirgi xuwa gobe mugani.

*

Alhaji yazeed rungume da baby sai washe baki yake kamar bashi bane ɗaxu acikin damuwa, akai akai yake faɗin sannu Halimatu Allah shi maki albarka, ya sumbaci baby yafi a qirga, kamar wanda aka tsikara ya dubeta da sauri yana faɗin ni har yanxu bansan menene kika haifa ba saboda farinciki gayamin macece ko namiji.

Ta buɗe idanunta dake lumshe tana kallonsa,
Tace nima bansani ba, na ɗauka nurses sun sanar da kai ko menene?

Yace ai saboda zumuɗi ana sanar dani kin haihu na banko ƙofa na shigo ban tsaya sauraren me kika haifa ba amma bara na duba na gani....

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un menene wannan Sadiya?

Yanda ya kira sunan ta sadiya ya sakata saurin tashi xaune daga kwance da take, kallonsa take cikin mamaki da yanda taga jikinsa na rawa sai gumi ke feso masa, lafiya ta tambaya da wani yanayi na ban tsoro.

Jin ya kasa amsata ya sakata qarasa inda yake xaune tana kallon abunda ya firgita shi haka, wata bugawa xuciyarta tayi jikinta ya ɗauki karkarwa cikin yanayi na ban tsoro tare da nuna jinjirin da yatsa tana kallon mijinta....

Wannan wace irin halitta ce, ni bani na haifi wannan ba, ba ɗana bane wannan.

Tsarki ya tabbata ga wanda yayi wannan halitta, da ace tunda aka kawo ki ɗakin haihuwa na ɗaga daga bakin qofar nan, tabbas dana yarda an musanya maki yaro, amma tabbas ke kika haifi wannan halitta....sai ga hawaye sharrrrr na bin kuncinsa itama ta fashe da wani irin kuka a gigice to wannan jinjirin mace xaa kirashi ko namiji? Ma'ana akwai halittar mace da namiji a tare da jinjirin.

Arewabooks Pherty001
08169334980

For continuation

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 23, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now