21-30

7.5K 275 1
                                    

MATAR SADIQ*馃拺

*Na fertymerh xarah*馃挐

           21 to 30

      Da gudu tafito cikin gidan ta nufi inda baba kebawa flowers ruwa

tace baba itama tanajin yunwane
yace a'ah
tace tor meyasa kake bata ruwa?
yace saboda karta bushe,kuma tayi girma ta qara kyau idan baa bata mutuwa xatayi.

tace tor meyasa baa bata abinci?
yace ruwa kawai ake bata ummi
tace inta girma xatayi kamar umma
yace aa, wake hada shuka da mutum ummi
tayi shiru tana kallonsa yana cigaba da xuba mata ruwa,ta sanya hannunta a baki tafara tsotsa,ya juyo yana kallonta

yace bakibar shan hannu ba hr ynxu,ta cire hannun tana murmushi

yace haka xaki girma kinashan hannu kowa yaqi aurenki,ace waccan matar bansonta hannu takesha..

ta kyalkyace da dariya tana boye hannunta

yace idan kowa yace bayaso qila faruq ya taimaka yace inaso kotana shan hannu

tace aishi yanada matarsa anty bebi,tana da kyau tana bani chocolate

tor ai sai yayi ta biyu dake,ta soma dariya batare data fahimci abinda yake nufi ba

yace a'a wayaga su ummi angirma anxama manyan mata kuma *matar faruq* ta tunxure bakinta

ni *matar sadiq* ce
yace wane sadiq badai yallabai  ba, tayi shiru tana kallonsa
yace inaaa, waneke yarinya ai sadiq sai manya mata
tace baba in dauko paper ka rubutamin *matar sadiq*
yace aini bn iya boko ba ummi wannan sai ku,ta juya ta fice hade da sanya hannunta a bakinta

tana isa dakinta ta dauko pencil da paper ta nufi dakin faruq, ya fito yana shiryawa

yaya faruq yau xaka goyani?
yace ke yau axumi nakeyi karki dameni
tace tor waya tayarda kai sahur?yayi mata banxa
tace azumin ka nawa?
a taqaice yace hamsin,ta soma dariya tana fadin my own is hundred,nawa yafi nashi yawa馃槢
yace ke kixo ki fita pls karki qaramin ciwon kai,
tace tor rubutamin *matar sadiq* anan
yace baxan rubuta ba
tace pls yaya,
yace kije kijirani falo ina xuwa,ta juya ta fice

a falo ta xauna ta tsurawa t.v ido tana kallo hannunta a baki tana sha,yazo ya zauna kusa da ita,ta cire hannun hade da miqa masa takardar,ya karba ya rubuta mata matar faruq,ta karbi paper tana dubawa she is good in english,bata iya hausa sosai ba amma for her own understanding tunda ance sadiq dole *s* tayi appearing a rubutu amma bata gani ba,tayi rau da fuska kamar xatayi kuka tana kallonsa

tace ba haka bane,ya murtuqe fuskarsa
yace tunda ba haka bane sai ki rubuta yanda yake,ta cillar da paper sai ta fashe da kuka,irin kukan nan na yara mai sauti wanda yafito da umma da talatuwa a kitchen

tace kai dai faruq baka gajiya da sanya yarinyar nan kuka ban saniba ko dadin kukan kakeji

yace umma nifa bn mata komai ki tambayeta na daketa?

tace menene ummi?
tace wai nace ya rubutamin matar sadiq shine ya rubutamin wannan, umma ta dauki paper tana dubawa kafin taja tsaki

tace ance baa sonka basai kabar wannan naci ba,
talatu tace a'a hajiya da dai kin barta da ubangidana akan yallabai faruq yafi dacewa da ita.
faruq ya tashi yana fadin barsu talatu sunyi sugama yaya baxai sota ba yafi qarfinta, nima nafasa ynxu banasonta,inada budurwata tafita kyau da komai mema xnyi da wannan,

talatu ta fara dariya,umma ta dauketa da paper a hannu,ta karbi pencil hannunsa ta wuce tana fadin ummi dan tana choco baxaka kirata mummuna ba,tunda tace bataso baxaa mata dole ba,shaqiqinka da takeso shi xata aura.

faruq ya juya yana kallon talatu
yace wai taya xaa dauki yarinya with d age of 12 abawa mai 34, xaa fa cuci qurciyarta tunda ita ba rainon qauye bace,she x j.s2 now a barta ko skul ta qare..

talatu tace ni abinda na fahimta ummy batasan so ba,sadiq birgeta ne yayi dan taganshi mai kyau bayaga wannan baxaisa a aura mata shiba.

yace Allah ya sauwaqa.

*washe gari*

Tunda sassafe kafin tayi brkfst ta subuce batare da sanin masu gadin gidan ba ta fice hannunta dauke da paper da qaton prem na hoton sadiq xataje nemansa
[8:57PM, 6/19/2016] Pherty馃帳馃懐: Tfy take batare da tasan inda ta nufa ba,

duk wanda tagani xata nuna masa pic din wai tana nemansa,

da yawa mutane ke mata kallon mamaki yarinya da ita take neman wani,dan me baxaa turo wani ba,

yunwa na soma damunta sai ta rasa hanyar da xata koma gida tafara kuka tana tfy rungume da pic din da paper adai dai wannan lokacin talatu taje yimata wanka dakinta bata sameta ba sai ta sauko qasa bata nan,bata harabar gidan, taje dakin umma dataga batanan sai ta sanarwa umma ummy fa bata gidan

haba dai talatu,ina ummi xataje da safiyarnan,yama kike tunanin xata fita gidannan da securities haka wadda ke tsoron soja?

Wlhy hjy duk inda kike tunani batanan hr lambu naje,naduba dakin da suke wasar game batacan,

tace ki dubata dakin faruq mana, ta fita bada jimawa ba ta dawo hankalinta a tashe

shima tashinsa barci kenan bai gantaba kiyarda bata gidannan fa

umma ta fito da sauri tana kiran faruq, sanye da kayan barci ya sauko yana yatsina fuska

yace umma saboda wannan kwailar duk sai ku tada hankalinku dana jamaa

tace kai dai sakarai ne wlhy,kaje muje nemanta

ya xaro idanunsa
yace a ina kuma duk inda taje xata dawo

umma tafice ranta abace batare da tayi magana ba ganin haka yabi bayanta

sajan kabir tafara tmby
ummy ta fita kuwa?
yace banajin tafita bnga fitar kowa anan ba
tace tor bata gidannan dole tafita,
ya juya yana kallon qofar tabbas ta fita ga alamar bude gate nan

ya juyo a raunane hankalinsa a tashe
yace kiyimin afuwa kada yallabai yaji hjy wlhy bnsan fitar taba naxagaya bayi ne inajin shigata toilet ta fita,

hankalinta ya qara tashi
tace tor ina sauran securities din duk kutaru anan kafin nadawo tabbas idan ummi ta bata zakuyi xaman cell hr sai anganta,ranta a bace tace faruq ya dauko mota sufita...

duk ta firgice tafita hayyacinta idanunta hr sun kumbura daga gefe ta tsinkayo wani soja tsaye sanye da kayansa duk tsoronta da soja sai ta nufeshi tana kuka ta riqo hannunsa

gida!!! ummana!!! help me out pls,(captain jabir kenan yaron sadiq,tsayin da yake anan wurin sunyi waya da uban gidansa sadiq kan yaxo xasuje wani gari aiki shiyasa ransa yake a bace, )a fussace ya daka mata tsawar danayi matuqar gigitata

yace kijaye min kada na lallatsaki ynxu,gida nine ubanki ko nasan hanyar gidanku ne,idan iyayenki sun damu dake sufito nemanki mana, ya shiga motarsa yajata fuuuu a fusacce

saboda tsoro da kidimar tsawarsa sai da tasaki fitsari a wando馃槙,nan take taji tsana da tsoron soja sun qara darsuwa a xuciyarta taja ta xauna nan gurin hade da sanya hannunta a bakinta tana sha,

tana kallon ynda motoci ke gudu a titin da mutanen dake wucewa ba wnda yayi qoqarin taimakamata,tana nan xaune idanunta na fara lumshewa sai ta xube wurin tana barci abinta馃槀

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now