31-40

7K 302 1
                                    

MATAR SADIQ*馃拺

*Na fertymerh xarah*馃挐

         *31 to 40*

       Tana gurin kwance taji ancirata sama,ta bude idanunta da sauri hade da sanya kuka,wanni dattijo ne dauke da ita, yayi saurin ajiyeta yana fadin yar'nan badai fitsari kikayiba,mekikeyi anan?

cikin kuka ta soma magana
gida..gida....
yace inane gidanku?
ta juya gabas da yamma kudu da arewa tana kallon hanya kafin ta qara maida kallonta garesa tana girgixa kanta
yace baki sani ba?ta gyada kanta
yace baxan iya daukarki da fitsari a jikinki ba tunda rigarki ta sauko ga gwiwa kicire dogon wandon,da sauri tacire ta ajiye nan qasa,yace ki dauko abinki mana,ta girgixa kanta,

yace ai baxaa wulaqantarda suturaba,bara na samo leda,yanufi wani shago dake kusa ya karbo ledar juyowar da xaiyi sai yaga mota tayi parking guring,da sauri ta nufi motar sanda umma tafito taje ta rungumeta tana kuka,

ta dauketa hade da sanya hannunta qasan rigarta wayam babu pant aciki,a tsorace take kallonta

tace ina pant?waye yacire maki pant,me akayi maki?

ta nuna mata dogon wandon dake qasa
tace pant din yana ciki

tor wayace kicire?
dattijon ya sanya kayan cikin leda yana fadin fitsari tayi dasu shiyasa nace ta cire kuma taxo nan hanya ta kwanta tana barci,dan Allah adaina sakaci da yara musamman ya'mace baa san inda xasu fada ba

talatu ta karbi ledar tana godiya itama umma tayi godiya hade da qirgo kudi 10k tabashi ya soma godiya.ba kakkautawa abinda baiyi xato ba.

hr suka shiga motar faruq bai tankaba,umma tace meya fito dake ummi,meyasa zaki fito bakya gudun a saceki?

ta nuna mata pic din sadiq dake hannunta, iya quluwa ta qulu ranta yayi matuqar baci ta bata fuskarta tana kallonta

tace shi sadiq din xakije nema?abinki ya soma isana masu soyayyar gsky basuyi irin ynda kikayiba ballantana keda bakisan komai a soyayyarba,

ta fisge pic din ta ajiye agefenta kana ta amshi paper ta yaga

tace sabodashi kina neman xautar da rayuwarki ki tadamana hankali,tunda abin hakane xn daura maki aure dashi gobe sai kije can kitare anasa gidan,tashi kibarmin jikina shashashar banxar da batasan rarrashiba,

ta tashi daga jikinta tana irin kukannan na xuciya marar fitar da sauti kamar numfashinta xai dauke,talatu ta janyota xata rarrasheta ta fisge tana cigaba da kuka, uffan dai faruq baiceba hr suka iso gidan

securities dana taru suna jiranta bata tsaya saurarensuba tafice ranta a bace,itama ummi tafito motar ta jingina tana cigaba da kuka

talatu taxo ta dauketa da qarfi tana wuntsile wuntsile tana kuka ta haura da ita sama kai tsaye toilet ta nufa da ita tayi mata wanka ta shiryata hr lokacin kuka take idanunta duk sun kumbura tayi juyin duniya da ita kan tasha tea taqi,ta dauketa ta sauko da ita,umma na duba takardunta datake dubawa kullum

tace hajiya taqi karban tea kuma da alama tana jin yunwa,

tace ajiye tea din kiyi tfyrki karta sha dan kanta.

ta email umma ta tura yan uwa da abokan arxiki auren sadiq gobe,kana ta tura ta contacts dinta, ta dago tana kallonta ta rakube sai sheshsheqa takeyi hannun ma ta kasa sanyawa a baki tasha,sai taji tausayinta ya kamata musamman data tuna saboda yaronta take wannan,

tace xoo ummina *matar sadiq*
ta make kafada baxata jeba hawaye nacigaba da xubar mata

yi haquri gobe xnkaiki inda sadiq kihuta,ki tabbata dashi hr lokacin da xaki fara haifamin jikoki, nan ma taqi xuwa, ta tashi ta nufeta dan tasan halinta da kafuwa ta dauke ta ta rungumeta tana shafa bayanta

sorry sorry,umma tayi laifi tayiwa ummy fada,gashi hr kin janyowa kanki ciwon kai

tasamu da rarrashi da ban baki hrta bata tea din ta shanye kana ta dauko xani da niyar goyata talatu ta karbeta tana fadin

haba hjy inake ina goya ummi,kin tsufa baxaki iyaba
tace duka ummi nawa take batada jiki xn iya goyata xaxxabi naji ke neman rufeta

talatu tace bara na goyata idan tasha magani,sai tafita da ita...

*Abuja*

Tana kwance jikin sadiq lokacin da txt din umma ya shigo wayar sadiq

ta ware idanuwanta sosai tana kallon rubutun kamar idanunta basu gani sosai Auren Sadiq da Ummy Aysher

ta jefar da wayar bayan ta fashe da kuka mai tsanani

yace menene haka meyafaru
tace gobene aurenka fa gashi umma ta turo
[8:36PM, 6/21/2016] Pherty馃帳馃懐: ya dauki wayar ya duba kafin ya kira umma

yace barka da gida umma......
batare da ta amsa ba tace ina fatar kaga saqona nariga nagama sanarwa hr abokanka gobene daurin aure inkaga dama kaxo koba da kaiba xaa daura auren,kuma inaso a gyara mata dayan part din anan xata xauna hr lokacin da xata haifamin jikoki, sa'anan lefenta bn yafe masu ba dole kayisu kamar ynda kayi na xuhura, kudi xaka turo dasu aje dubai ayi mata ko kuma kai kaje ka hado mata da kanka zabi ya rage naka ta tsinke wayar,

kamar ya dora hannu aka yasaki ihu ya rasa ta inda xai fara rafrashin xuhura ko kuma xafin xuciyarsa,bai taba ganin irin wannan aurenba,tor wacece wannan Aysher da xaa aura masa?

Washe garin ranar kuwa kamar da bakin kwarya aka taru gidan dayake babban gidane duk da abin yaxo ba shiri haka aka daura auren ba ango, abokan ango sunyi mamakin wannan auren dan koda wasa sadiq bai taba gayamasu yana neman wata ba saboda sunsan ynda yake da xuhura, suka soma kiranshi a waya suna son su xolayesa wayarsa a kashe kuma gashi baixo auren ba hr aka gama aka watse

fannin ummi kuwa farinciki fal axuciyarta badan komai ba sai dan yau ana biki gidansu taga mutane da dama Allah ya sanya mata son jama'a gashi an sanyamata sabbin kaya

sai tabi umma dake fama da jamaa tana fadin
umma waye ya haihu?bikin wa akeyi?
tace bikinki
tace umma wannan bikin ne na sauka danayi kike qarayimin?
tace a'a wannan daban ne na aurenkine da sadiq
tace umma menene aure
tace kin xama *matar sadiq*

sai ta soma tsalle
tace umma yaushe xaixo muyi wasan ango da amarya inada tedy da kayan wasa

tace wannan ba abin damuwa bane ummi xakuyi wasa hr sai kin gaji anjima kadan xaku tafi keda talatu ita xata riqa kula dake.....

umma tayi kiran wayarsa bata samesa ba hakan na qara qullar da ita tunda ko auren bai xoba, da yamma tasa driver ya dauki ummy da talatu bayan sun cika booth din da kayansu

tace talatu ga amanar ya'ta kinsan ynda take gareni ki kula da ita sosai kuma kiyi haquri da ita saboda yarinyace ummi, ban yarda kibari sadiq ya kwana da ita ba hr sai xuwa wani lokaci ta mallaki hankalin kanta, sannan ban amince kije inda xuhura ko kibarta taje sashen xuhura ba haka kuma inaso kisamin ido kan takun sadiq idan yana kula da ita kamar ynda Allah yace kowane miji akan matarsa.

mgnr skul dinta kuma faruq yariga ya nema mata admission acan tun jiya nxtwk xata fara xuwa,uniform dinta na nan ciki,islamiya kuma ki bincika ko nawane kudinta sai ki sanardani Allah ya kiyaye ya kaiku lfy

tace amin hajiya insha Allah xn kiyaye xn kula da ummy kamar nina haifeta....

umma tayi murmushi bayan ta loda tedys din ummi bayan motar ta kalleta

tace my ummy is happy today xataje ta barni

cikin murmushi tace i will miss u umma,yaushe xamu dawo
tace in d nxt one month
ta soma dariya itama umma tayi dariya kafin ta rufe masu motar taja kadan tana daga masu hannu itama ummy ta leqo ta window tana daga mata hannu tana murmushi.

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now