159

5.9K 266 2
                                    

Ya salam! shine abinda dr.merah ya fada cikin rudewa kafin yayo kan sadiq, da sauri nurses sukayo kansa dan kaimasa taimakon gaggawa

bnda hawaye babu abinda umma da momy suke jikinsu yayi sanyi matuqar sanyi da mutuwar xuhura(am still crying too馃槶)

duk cikinsu ba wanda yabi takan ummie musamman da sukaji ta haihu lfy ta sami baby boy, sai talatu da bebi sukaje suka xauna da ita, sukuma sauran suna gurin gawar xuhura鈥︹€︹€?

tun dawowar ummie cikin hayyacinta take kuka, musamman da akaxo da yarinyar xuhura cewa zata hadasu subiyu ta shayar, taji mutuwar xuhura sosai hr cikin ranta, tana tuna irin xamansu da xuhura kuma hr a ranta taji ta yafemata kuma ta karbi yarinyar xata shayar da ita ta kula da ita kamar ynda xata kula da yaronta, xata basu tarbiya gwargwadon iya warta kamar ynda nata iyayen suka tarbiyantarda ita,

ta rungume jariran tana kuka sosai sun xame mata tagwaye.....

An bawa iyayen xuhura gawarta sukayi gida da ita inda daruruwan jamaa sukayi jana'ixarta, *kullu nafsin xa'iqatil mauti*

mijinta da mahaifinta suka sanyata a kabarinta suna masuyi mata adduar fatan alheri,yafiya, afuwa da adduar Allah yayi mata masauki da aljanna, Annabi yasan da zuwanta sukuma ya basu imanin jure rashinta...Allah kayi mana gafara amin馃槳

Abubakar sadiq ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya akan jana'ixar xuhura babu ko digon hawaye a idanunsa,

basusan shi kansa kukan na xuwa ne idan ansan abinda akeyi tor baisan me yakeyiba baisan halin da kwakwalwarshi ke cikiba
[7:17PM, 7/31/2016] Pherty馃帳馃懐: yasan dai kawai xuhuransa ta rasu sun kaita makwancinta, bayan wannan baisan komai ba baisan kansaba baisan a ina yakeba, sai da ya bude ido ya ganshi dakin ummie......

baya rintsawa yadda yaga rana haka yake ganin dare,, ya wuni yana karbar ta'aziyya yan uwa da abokan arxiki hr xuwa
kwana uku........

hr bayan gama ta'aziyar kwana uku bai sanya ummi a idanunsaba hassalima baisan meta haifa, diyar xuhurama baisan kalartaba baisan ya takeba gabaki daya jariran ba wanda ya sanya a idanunsa

da yawa iyayen xuhura da nashi da abokansa hr general kan xauna suna bashi haquri da ban baki akan ya haqura karya sanya damuwa a ransa

kalmar TO itace k茫wai yake binsu da ita saboda itace kalma mafi sauqin fada a bakinsa sai kuma bin kowa da ido, abinci bayaci kwanansa uku rabonsa da abinci, bayan ruwa dayake kwararawa cikinsa babu komai, umma tayi rarrashi hrda kuka tayi masa kafin ya amince yace tayi masa sinasir xai gwada yaga ko xai iyaci

ummi na tare da tagwayenta renonsu take haiqan talatu na kama mata, idan suna kuka tare sukeyi tare umma ke rarrashinsu hr lokacin nononta bai kawo ba sai ranar ta hudu da haihuwarta

sadiq na qoqarin fitowa dakinsa yaji umma na fadin

ynxu tunda sunkawo kibasu susha ummie

umma yaxanyi na dinga basu nono nifa ban iyaba,

momy tace tor ai ba iyawa bane, daga rigar kawai xaki kibasu susha bakiga ynda bebi takeyi bane da adnan...

idanunta sukayi rau rau ta dubi faruq
tace tor kadaina kallona,

yayi dariya sosai hade da yimata gwalo.kafin ya maida kansa gun adnan yana fadin muna nan tare xamu dinga ganin nonon a waje ma...

talatu tace kaidai mai dakina bakada xuciya,ummi sai wulaqanci take ma kaqi kakyaleta

yace nabari talatu ynxu kam nayi xuciya

ummi ta karbi yaron tafara bashi aikuwa da sauri ya capke ta kwala uban ihu bayan ta cire bakinsa daga nono umma xafi, Allah xai ciremin nono ta fara kuka

umma tace ai haquri xakiyi tunda farkone kowa da haka ya saba,ungo fara bata itada take macce maiyiwuwa baxakiji ciwo sosai ba

ta karbi yarinyar tana fadin, umma shi kibashi naki yasha

umma tace kefa naga alamar baxaki daina wauta ba nida bn haihuba ya xa'ayi nabawa yaro nono?

ummie tayi shiru tana bawa yarinyar nono tana rumtse idanunta saboda xafin da takeji...

sadiq na daki na jinsu, tausayin ummie ya cika xuciyarsa ummie baxata iya shayar da yaran duka biyu ba dole sai yaje asibiti an rubuta masu irin madarar da xasu dinga sha ynda xata sami sauqin shayardasu, sannan yasan baxata iya kula da yaranba, nanny xaije ya dauko guda biyu kowa da nata duk wata xai dinga biyansu, sai ya tashi ya fito

sanda ya fito daga dakin gefensu ma bai kalla ba baxai iya jurewa ba

faruq na ganin fitowarsa ya dauki jariran yasha gabansa, ya langabar da kansa yana kallonsa,

yaya dan Allah ka sanyawa xuciyarka haquri kodan jarirannan da hr ynxu baka daukaba basuji dumin mahaifinsuba, baka nuna masu gatan daka qudira xaka nuna masuba, duk xumudinka da murnarka akansu yau kana fushi dasu,miye laifinsu yaya.....

duk falon akayi shiru ana saurarensu cike da tausayawa, ummie kuwa hada kanta tayi a cinyarta tana kuka sosai kamar ranta...

bnda hawaye babu abinda ke xuba a idanun sadiq, ya subawa jariran ido sosai yana kallonsu, yarinyar gabaki daya xuhurace sak ba inda tabarta hr hsken fatarta,hancinsu bakinsu duk iri dayane,

ya juya yana kallon yaron ummie shikuma ba inda ya dauko ummi ko kadan duk sadiq dinne,kamar yayi kaki ya xubar, shima yaron hasken babansa ya dauko ga kamaninsa sosai akan yaron dakanshi kasan shiya haifesa

nan da nan yaji xuciyarsa na bugawa, yaji jariran sun birgeshi, yaji yana qara sonsu duk da tun kafin xuwansu duniya yake sonsu illah ninkawa da son nasu yayi a xuciyarsa......faruq ya katsesa

yaya karbi ya'yanka kasanya masu albarka kamar kowane uba...amma sadiq yaqi illah murxa hannayensa da yake sai qirjinshi dake takai kawo kamar xuciyar ta ballo qirjinsa ta fito

ya girgixa kansa ya juya ya fice.馃槳

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now