149

6.2K 294 1
                                    

Shigowar Dr.merah ta katse masu hira, nurses ne hudu a bayansu,ya dubi sadiq

Yace aminity xamu maidaka yanxu, alhamdulillah sauqi yazowa sadiq bature sai fatan raunukan su warke ka Sami qarfin jiki.

Sadiq yayi murmushi kawai yana kallon Ummi itama shi take kallo,

Nurses din suka jashi har lokacin Ummi na riqe da hannunsa suka fito ta qara qanqameshi jikinta na soma rawa ganin sojojin dake waje birjik

Ana fitowa dashi duk suka gyara tsayuwarsu hade da Sara Masa bayan sun qame lokaci daya,

Ya zame hannunsa daga na Ummi saboda da dayan hannun aka harbesa,ya daga masu hannu yana murmushi suka soma gaidashi da yimasa sannu,

Bai furta kalma ko dayaba illah murmushi dayake binsu dashi,

Mataimakinsa yunusa da general sukabi bayansu kafin su umma da faruq,ummie na jikin momy.

Sanda suka iso aminity bayan sun gama treating dinsa sun samasa drip nurses din suka fita.

General ya dubi yunusa(mataimakin sadiq)
Ya maganar wadannan yaran da suka kawo hari,sunyi magana kuwa?

Yunusa ya girgixa kansa yana fadin har ynxu yallabai mun galabaitar dasu fiye da tunaninka munyi masu m.p sun kasa magana inaji sai an hada da yimasu _electric cap_ tukunnah.

General yace ku azabtar dasu sosai harsai sunyi magana suna da taurin Kaine amma abinda mamaki da sukace turosu akayi tor waye wannan?

Yunusa yace Allah ne masanin gaibu amma kowaye yallabai yakamata idan aka kamashi a hukuntashi(ya dubi sadiq) sir. Baka suspecting wani abokin gaba ko kuma kayi fada da wani?.

Sadiq ya girgixa kansa yana fadin bana xargin kowa banyi fada da kowaba kuma ni banida abokin gaba '''but I don't know it may be maqiyane'''

General yace hakane '''sadiq is friendly xamuyi bincike mugane kowaye''' suka juya suka fice da yunusa.

Umma tace sadiq idan kasami lfy Allah ya tada kafadunka lfy xaka ajiye wannan aikin dake Neman kasheka ko yanxu banda Nisan kwana da yanxu muna nan muna sharba hawaye馃槃

Yayi murmushi yana fadin tor umma idan badaga wurin aikina bane fa?

Tace duk magana dayace sadiq ai nikam abar aikin kadawo ka kula da dukiyar mahaifinku ni ynxu na tsufa yakamata ace kun karbarmin yanxu baxan iyaba kula da gidaje,filaye da kamfaninka duk nice kun xubamin ido kaida faruq.

Sadiq yayi shiru kawai ya lumshe idanuwansa shikam baxai rabu da aikinsa da matsayinsaba,

Faruq yace niwai ina xuhura ne,bangantaba

Umma taja tsaki tana fadin inafa xaka ganta taje Neman duniya duk xai wuce business tajeyi sai anyi mgn tanuna tafikowa son mijinta

Sadiq yace umma batada lfyne taje ganin likita kuma merah yagayamin sunyi waya xataxo('''ya fadane dan yakareta kawai bayason tana baqin jini garesu amma shima yana cike da mamaki dan yasan dole ace taji ynxu.''')

Umma tabe baki kawai tayi, momy ta tashi tana fadin yakamata muje gida muyi wanka musami abinda mukaci kafin mudawo,suka tashi umma

Tace ke bebi sai ki tsaya xamuje da Ummi itama tayi wanka ta sauya kayan jikinta

Ummi tace ni umma baxan jeba kije da anty bebi nixan kula dashi

Umma tasaki baki tana fadin ke Ummi yaxaki iya kula dashi,kibari babba ya tsaya dashi mana.

Faruq yace kibarta mana umma mijintane tasan yanda xatayi dashi bebi kuma dole ta bimu gida saboda adnan.

Momy tace hakane suka juya suka five sunayimasa fatan alheri

Ummie tace umma nima kixomin da kayana anan xnyi wanka na sauya kayana.

Tace tor.

Yayi ajiyar xuciya idanunsa akanta itama shi take kallo

Yace Ummi xan shiga bandaki,kamani na tashi

Ta soma dariya sosai tana riqe baki
Lallai ma yaya,ni ina nake iya kamaka so kake na fadi nima naji ciwo?

But kefa kikace xaki iya kula dani kinsan bakya iyawa meyasa kika barsu suka tafi gabaki daya? Tayi shiru tana tunani kafin

'''Tace tor yaya let me call d nurse to help you, is her work.'''

Yace meyasa bayan gaki,ai ba aikinta bane aikinkine '''you are my wife not her i need ur own help''' idan baxan samu bane inkira faruq yaxo yanxu ya maidaki gida,nasan da xuhura na nan baxata qiyiminba.

Nan da nan ta bata fuska jin ya ambaci xuhura taji haushi sosai ta tunxure bakinta ta nufi waje tana fadin bari na kira nurse tacire drip din....yabita da kallo kawai bata jimaba sai gata tadawo da nurse tana tsaye hr lokacin bata saki fuskartaba shikuma ya xuba mata narkakkun idanuwansa yana kallonta komiye abin damuwa Dan yace xuhura? Nurse tacire tafita ta basu wuri.

taxo kamashi
taga taga....kica kica haka sukayi ko motsashi takasayi馃槀

shi dariyama take bashi,lallai ummi baxata iya jinyarsaba,ko qarfi bada,yanason yin dariya sosai, da kyar ya miqe yana dariya cikin xuciyarsa duk ta dauka itace ta miqar dashi sai haki da shessheka takeyi tana ajiyar xuciya hrda kiran waiiiiiiiii

baisan sanda dariya ta subulcemasa ya juyo yana kallonta ta riqe qugu alamar ta gaji, ganin ya nufi hanyar toilet taje ta riqasa , takaisa toilet din tafito tana sauke ajiyar xuciya,

ya girgixa kansa yana dariya qasa qasa.

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now