Auren sirri 08

214 14 4
                                    

🔐Auren Sirri🔐 8️⃣

King yace Maama (hakan ake kiran ta) naga kuna hira ne shiyasa naso kada na katse ku, cikin smiling maama tace da yake ma hiran akan kane mukeyi kaida Nadiya akan batun auren ku, mummyn ku ta kira ni jiya tace ya kamata azo a tsaida ranar biki tunda gashi zaka gama wannan school din saimu tattara mu tafi gida gaba daya tunda Allah Yasa 'yan kasa daya ne mu duka sai ayi bikin auren acan gaban en uwa da abokan arziki kuma ga Baban ku ( baban nadiya shi suke cewa baba) ya damu yana so ya aje aikin jakadancin nan hakanan yanaso ya huta wai ya gaji da yawon kasashen dunia. Tunda ta fara magana king yai kasa da kai cikin wani bala'in fargaba da tashin hankali, ta yaya ne mummy zata mashi haka? Meyasa? Meyasa?? Baisan duniyar da yake ba sai jin sister din shi Amal yayi tana jan hannun shi wai suje ya bata gift saboda ita da mummy sukai wannan shawarar kuma tasan abu ne da zai faranta mashi, aibata kai aya ba sai saukar mari taji tasss! Gaba dayan su falon suka saki baki suna kallon abinda ke faruwa.
Cikin wani irin madaukakin mamaki Amal ta dafe kuncin ta hawaye na zuba take kallon King ga baki bude amma ta gaza magana sai juyawa tayi da gudu dakin ta ta fada gado taci gaba da kuka. Gefen king kuma fuwww ya wuce nashi sashen, sauran mutanen falon kowa ya rasa ta cewa kafin maman nadiya taja ajiyar zucia ta kalli mummy gami da cewa a wani dalili king ya mari Amal? Meke faruwa ne? Cikin ajiyar zucia mummy tace saboda matsala ce babba ke kokarin kunno mana, maman nadiya tace kamar yaya kenan? Kai tsaye mummy ta basu labarin yanda sukai da king the other day randa nadiya tazo.
Tun kafin ta karashe nadiya ta fara kuka dan shagwaba sai tahau birgima bisa carpet tana zabga ihu wayyo Allana na shiga uku ni nadiya dama ashe rana irin ta yau zata iya zowa cikin rayuwa ta? Me ke shirin faruwa dani? King yana wa wata mugun so irin wanda ni nake mashi, wannan wace irin masifa ce? Da kyar maman ta tajata jikin ta tana lallashi gami da kwantar mata da hankali akan za'a samu mafita king bazai auri kowa ba sai ita ( kasancewar ta mai tsananin son diyar ta wadda bata ganin laifin ta) sauran sisters din king Amatullahi da Amira ma suka matso suna lallashin Nadiya akan ta cire wannan damuwar a ranta king nata ne ita daya, da wannan suka samu suka lallashi nadiya kafin sukai arangama zuwa dakin Amal dake kwance tana ta zabga kuka kasancewar ranar ta yau itace rana ta farko da aka taba dukan ta kuma dan uwanta da bata hada soyayyar shi da kowa ba cikin sauran en uwan nata shine ya mata haka, da kyar suka lallashi Amal sana suka bata labarin abinda ke faruwa, mummy na gama fada mata ta tashi da gudu tayi sashin king sai haki takeyi kasancewar ta yar lukuta, ta tarar da king ya dafe kai da duka hannayen shi.
Cikin sanyin murya tace brother am sorry, i didn't know... tin kafin ta ida king ya taso da azama ya rike ta shima yana bata hakuri akan marinta da yayi gami da cewa bansan meke damu na ba na sauke haushin maman nadiya a kan ki little sister, am very sorry for what i did, pls forgive me. Nan dai suka shirya kansu sana king ya dora mata da bayanin Ayisha, amal ta bata fuska gami da cewa shine duk tsayin lokacin nan ban cancanci sanin abinda kake ciki ba brother anya bani kadai ce nafi damuwa da lamarin ka ba? King ya kamo hannun Amal yana cewa little sister nasan ako wani yanayi kina baya na kina son abinda nake so ni dake soyayyyar juna da damuwa da halin da dayan mu ke ciki daga Allah ne, amma nayi la'akari ne da yanda gaba dayan ku kukai na'am da batun Nadiya shiyasa na kasa furta maki amma yanzu kiyi hakuri ki bani shawara yazamu bullowa lamarin? Amal tayi shiru da alamun tunani tare da ita kafin ta saki ajiyar zucia tace brother saifa munyi da gaske dan a gaskia su mummy sun shiryawa batun auren ku da Nadiya kuma indai baka so ka samu matsala dasu to mataki na farko da zamu dauka shine kada ka nuna baka so kaci gaba da binsu da yanda duk suka tsara kuma kayi hakuri ka auri nadiyar, king yai saurin sakin hannun amal gami da bata fuska ya nuna kofa yace get out pls amal, amal din tayi smiling tace a yanda kwakwalwarka ke ja nayi tunanin zaka tambaye ni dalilin baka wannan shawarar amma tunda bakai ba shikenan bari in tafi sadda duk ka bukace ni you know where to find me, har takai bakin kofa ta juyo ta mashi murmushi gami da cewa I knw that i do not need to tell u that ur secrets are safe with me, ta rufe kofar ta wuce cikin gida inda ta tarar dasu sun dawo falo sunci gaba da tsara yanda biki xai kasance da yanda zasu sa dole a bar batun Ayisha. Amal ta zauna ba tare data nuna rashin amincewa ba akaci gaba da tsare tsaren da ita, duk da cikin ranta tana hango tashin hankalin da za'ai da mummy nan gaba kadan amma data tuna abinda ta riga ta shirya sai taji bata da damuwa game da issue din.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now