Auren sirri 34

140 9 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣4️⃣
A kalla yau Iyalan Daddy sun samu kimanin wata hudu da dawowa Abuja, rayuwa suke mai cike da aminci da mutunta juna da kuma neman shawarar juna akan harkokin su na yau da kullum, bangaren Amira da Amatullahi kuwa sai sam barka, Ilimin addini ke shigar su ta ko ina yayin da tsoron Allah da Istigfari akan rayuwar da sukai baya ke ta yawo a kan su, yanzu ne suke jin su mutane ne, idan suka zauna suna hira sai suyi ta takaicin bata lokacin da sukai a rayuwar baya, Mamy kuwa ta dage iya yinta tsakani da Allah tana koyar da su abubuwa da yawa, duk wanda zai zo gidan Mamy a yanzu ya san da su Amira da Amatullahi, harta sister din Adnan  tasan da su saboda tana zuwa gidan Mamy.
Bangaren su Ayisha kuwa sai renom ciki ake yi, cikin yayi mata kyau duk kuwa da yana bata wahala, taki yarda kuma aje ayi scanning tace a ganin ta shishshigi ne wa Allah dan haka a bari har Allah Ya sauke ta lafia sana a san abinda ke cikin nata, King kuma ya goyi bayan ta, yanzu idan ba tayi da gaske ba ko spoon bata dauke wa wannan ita ce dokar King yace bai yarda yq dauki ta rika wahalar da kan ta ba, ita kuma takan yawan fada mashi mai ciki sai tana motsa jikin ta, amma sam bai yarda dan haka idan baya gidan ita ce keyin ayyukan ta amma da zarar ya dawo sai tayi tamkar batayi komai ba, gefe daya kuma ga kulawa ta surukai Ayisha na samu, a rana sai Mummy ta shigo gidan Ayisha so uku, tana tambayar ta ko da abinda take so, tun Ayishan na jin kunya harta saki harma idan mummy ta shigo sai Ayisha ta kama daria tana cewa mummy wai ba zaki dena wahalar mana da kan ki ba? Mummyn ma tayi daria tace ina fa zan dai na wahala ina shirin tarbar sabon ango ko kishiya, sana ta dora da cewa Ayisha jinin Mu'azzamu na ne fa kike dauke da shi a cikin ki? Anya kuwa kinsan matsayin Mu'azzam waje na? Sai suyi daria su duka, a haka rayuwar taci gaba da tafia har akai watannin.
Jingine bikin Amal da Muhammad akayi gefe sakamakon tafiyar gaggawa data taso wa Muhammad akan wani company da suke shirin budewa acan Turkey din, shiyasa ba'ayi bikin ba aka bari sai ya dawo to kuma tun yana tunanin abin ba zai wuce wata daya zuwa biyu ba yanzu gashi har ya tasamma wata na biyar, amma kusan duk sadda ya samu lokaci yana makale da Amal a waya suna hirar su.
Cikin Ayisha yayi wani irin girma da nauyi, kowa tausayin ta yake musamman yanzu da cikin ya tsufa haihuwa yau ko gobe, King ya samu Daddy yake masa tayin fita da Ayisha America haihuwa dan ta samu kulawa sosai ta likitoci kwararru, Daddyn bai musa ba yace toh amma ita dawa zata je ta zauna? King ya sosa kai yana niyyan fadin da shi amma ya kasa, daddy yayi kamar bai fahimci me king yake fada ba dan haka kai tsaye yace kaje ka shirya mata tafiyar haihuwar ita da er uwar ka Amal, idan ana bukatar karin mutane kana iya saka Amira ko Amatullahi, daddy yaci gaba da cewa saboda zata fi bukatar er uwarta mace kusa da ita kuma kai ga kasuwancin mu na nan ai kaga bai kamata kaje kayi zaune wata kasa ba ni ka bar ni da dawainiyar kasuwanci ba, mummy dake gefen daddy tace gaskia kam daddy kuma gani ma nima zan iya binsu, daddy ya harari mummy yace ni kuma ki barwa waye ni? Babu inda zaki ki bar yara suyi tafiyar, king dai haka ya baro gidan su ya shigo nasu gidan inda ya samu Ayisha kwance kamar ruwa, ita da kanta yanzu ko ce mata akai tayi aiki bata iyawa koda wasa, ta dago kai ta kalle shi kafin ta kokarta mikewa zaune, king yayi saurin taya ta zama yana cewa Ayish sannu sannu dai, Ayisha tayi murmushi tana shafo kan shi take cewa Mu'azzam yaron mummyn shi, king mijin Ayisha waye ya tabo mani kai? King yayi daria yace daddy ne ya hana ni in biki haihuwa wai zan bar mashi aiki da yawa anan gara su Amal su raka ki, Ayisha ta juyar da kanta tana kumshe dariya saboda tuni suke shirya yanda zasu tafi haihuwar nan tare amma lokaci daya daddy ya hana king, lura da dariyar da ayisha keyi yasa king ya mike yana cewa tunda na zama abin daria bari na bar maki gidan gaba daya, Ayisha tayi saurin kamo riko hannun sa tana cewa tuba nake Masoyi, amma abin ne ya bani dari saboda tuno yanda kaci burin muyi tafiyar nan tare amma lokaci daya daddy ya rusa, kuma idan ka duba zaka ga ba wai daddy yayi laifi bane yana duba tarin ayyukan da kukeyi a tare ne to idan k bar mashi shi daya taya zai fara? King yace ada bashi dayan bane yake yi ba? Ayisha tace ka dena maganar da kayi maganar yanzu da yasan dadin shigar ka harkar kasuwan cin, kai ne fa magajin daddy, king yayi daria yace gaki mai wasa daddy ko? Sukai daria su duka.
Bayan sati daya da maganar  Ayisha, Amal,Amira da Amatullahi suka daga zuwa America, kwanan su uku da zuwa nakuda ta kama Ayisha gadan gadan, akace ko wace mace da yanayin ta wajen haihuwa, ita dai Ayisha Alhamdulillah ta samu haihuwar da wuri bayan fara nakuda, yara biyu duk maza sak ba zaka raba kamannin su da Uban su ba, kasancewar kashe wayoyin su sukayi gaba daya dan haka basu samu sun kira mutanen gida ba sai washe gari da suka samu nutsuwa kowa ya dauki waya yana neman mutanen gida, Amira ta mamy tana mata albishir, Amal kuma king ta nema, yayin da Amatullahi ta kira Daddy, dan da nan labarin haihuwar ya baza dangi, kowa nata murna ana addu'ar Allah Ya taya babies.
Sai da sukai sati biyu bayan haihuwa sana suka shirya komawa gida dan ayi taron sunan, zumudi dai sun ganshi wajen mutanen gidan bayan dawowar su, nono kadai ke hada Ayisha da yaran amma komai Mummy tayi kane kane itace ke masu, baiwar Allah ko hutun kirki bata samu, sai kazarniya take da yaran, idan an mata magana takance wa'annan yaran sune namu, domin matan idan sun haihu yaran su ba namu bane na wani gidan ne, sai ayi daria kawai. Anyi taron suna duk da ba mutane da yawa bane sai en uwa da abokan arziki na kusa kusa, babu kunya king ya mayar da sunan shi ga babban wato Mu'azzam kuma da Mu'azzam din suke kiran shi, yayin da karamin ya mayar mashi da sunan Adnan kanin Ayisha wato ainahin sunan shi (Ahmad) saboda king yace bazai manta ba Adnan shine ya taya shi fafutukar neman soyayyar Ayisha lokacin suna London, shima kuma da adnan din suke kiran shi kawai dai sun kara da junior ne.
Watan su uku da dawowa Muhammad ya samu dawowa sakamakon kiran gaggawa daya samu na rashin lafiyar matar sa, ranar daya dawo ko gida bai karasa ta amsa kiran Ubangiji, Muhammad ya samu janazar ta, ya kuma yi mata addu'a sosai saboda yace matar kirki ce wacce ko wanne namiji zaiyi alfahari da samun ta matsayin mata.
Sati biyu da rasuwar ta aka daura auren shi da Amal, saboda rasuwar matar shi yasa ba'ayi wani biki ba, wanda ita Amal bikin bai dame ta ba kodon kasancewar ta likita mara son hayaniya ne? A satin bayan gama biki Muhammad ya tattara Amal da yaran shi biyu suka wuce Turkey da zama bayan sunyi sallama da mutanen gida, sai muce Allah Ya basu zaman lafia da zuriya dayyiba, Ameen.

Sanarwa! Sanarwa!!
Ina bada hakuri akan jimawar karashin Auren sirri, nayi rashin lafia ne ga ayyukan gida ga na Office ga hidimar rayuwa. Kuma idan baku manta ba a hashtag na fada cewar it's a short story, naso pages din ya kare a 20pages amma gashi ya kai har thirty something, In Sha Allah yanzu sora one page a karasa labarin. Amma ina maku albishir da cewar akwai sabon labari da zaizo bayan karashen Auren sirri mai suna HAKURI BABBAN JARI, littafin Samira Abdulkadir amma saboda kyawun littafin nayi niyyar rubuta maku shi a nan. Nagode

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now