Auren Sirri 21

137 17 4
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣1️⃣

Rabe ya fara sanda yana neman gudu, karaf Ahmad ya damke shi ya buga ga bango yaci gaba da kai mashi bugu tako ina yana neman halaka shi, saiga Rabe yana ihu, a lokacin Salma da Hady suka shigo a guje sukai kan Ahmad da Rabe suna shiga tsakani, Rabe dai tunda ya samu agajin Salma da Hady saiya ara na kare ya fice da gudun bala'i baya ko waiwaye, Hady ta hau tafa hannu tana cewa yau ni Hadiza me zan gani haka? Yanzu Maryam duk gudu na da Ahmad yayi ya kare kanki amma da abinda zaki saka mashi kenan? Kwarto? Sai suka hau sallallami, saika rantse da Allah basu suka shirya makircin ba idan ka gansu a lokacin.
Sai a lokacin Maryam ta samu damar yin kuka, wani tsananin fushi mai hade da kishi ya sake kama Ahmad yaji kamar ya kai mata duka amma sanin bazai iya ba saboda tsananin son da yake mata sai kawai ya hau buda bedside ya fiddo littafi ya yagi paper ya dauki biro nan take ya rattaba mata saki uku, yana gamawa ya mike ya isa har inda take ya kamo hannun ta ya damka mata ya juya da niyyar barin dakin, Ahmad ba zaka mani uzuri ka saurari bayani na ba? Ba zakai bincike ba akan abinda ya faru ka gano gaskia ba? Cewar Maryam data ga Ahmad na niyyar barin dakin, Ahmad din ya dakata ya jiyo ya kalle ta kafin ya furta babu wani binciken da zanyi bayan abinda ido na ya gane mani, ni kika cuta cikin abinda ya faru, ciki kuma sai kije ki kaiwa kwarton ki tunda Allah Yasa naji da kunne na cewar cikin wani ne ba nawa ba, daga haka Ahmad yasa kai yabar gidan gaba daya baiko kula Salma da Hady ba.
Saida suka tabbata Ahmad ya bar gidan gaba daya sana suka kwashe da wata irin daria, Hady ta tako zuwa wajen Maryam ta kwashe ta da maria ta kuma kwashe ta da mari kana tace wannan marin na bata man lokaci da kikayi ne saboda zaman da nayi Kaduna ba tare da nayi niyyar zaman ba amma dole kika sani zama saboda in bata tsakanin ki da Ahmad dan bana so ma zancan yaje gidan su, abu na gaba kuma na mare ki ne saboda naji zafin auran abin so na da kikayi kafin ni in aure shi harda samun shegen cikin da kikai kafin ni in haifa masa, Maryam ba'ayi wata diya mace da zan iya barwa Ahmad ba a halin yanzu dai bare ke kadan kada miya, babu boka ba Malaman zaure amma makircin Salma ma kadai ya ishe ki domin ita ta shirya komai.
Maryam ta kasa magana har suka gama zayyana mata komai kafin su kare daci mata mutunci akan saita hanzarta barin gidan tunda ga takardar da Ahmad ya bata nan ya tabbata ya sake ta saki ukku, suna daria cikin jin dadi suka bar gidan. Maryam bata san iya tsayin lokacin data dauka ba ta kasa kukan ma sai wani azabar zafi dake damun ta a kirji, babu abinda yafi daga hankalin ta irin Ahmad ya sake ta har saki uku.
Kwanan ta uku bata saka Ahmad a ido ba hakan ya tabbatar mata jira yake tabar gidan kafin ya dawo dan haka ta dauko er jikkar kayan ta ta hada wanda basu fi kala goma ba, ta kuma dauki kudaden da Ahmad ya tara mata tare da diary din ta sai pictures din da suke kan bedsides din dake dakin tabi ta kwashe su duka tana cikin tattarawa ne taci karo da envelope din da Ahmad ya dawo da ita ranar da abin ya faru, kasancewar nan ya zubar da ita da abincin daya dawo masu dashi kuma tun ranar bata iya koda gyaran dakin bane bare gidan gaba daya, result dinta ne daya ce zai biya ya anso mata, saita saka shi cikin jakar kayan ta kafin ta fice ta bar gidan, sai a lokacin kuka mai karfi ya taho mata data shiga taxi.
Mai taxi da yaga suna ta yawo bata ce ga inda zai kaita ba sai ya fara tambayar ta ina zai kaita, da kyar ta iya fada masa ya kaita wani hotel koma na ina ne, ya kaita ta biya shi ya wuce. Kwanan ta biyu a hotel baci ba sha sai da kyar take iya shan tea, da taga zama bazai mata ba saita mike wani yammaci ta shirya taje gidan su wata er ajin su da sukai shiri da ita kasancewar ta hanyar gidan su ne, yasa ta kalli gidan gata ga shi amma yafi karfin ta shige shi hakanan ta goge hawayen ta har suka isa gidan su Asiya. Bayan sun gaisa take mata maganar abinda ya kawo ta tana so a sama mata gidan aikatau amma ba'a kaduna ba, kasancewar tasan da batun mai samo aikin aikatau din tana zuwa gidan su Asiya sosai, Asiyar dai tayi mamakin jin hakan daga Maryam amma saita kauda mamakin ta tace kin kuwa ci sa'a dan tana dakin Maman mu yanzu haka kuma naji tana mata batun mai aiki take nema da zata je Lagos, kafin kace mi tuni suka aje magana akan gobe agent din zata kai Maryam gidan su masu neman mai aikin dan dama mai aikin kawai suke jira su koma Lagos din.
Da zata koma hotel din data sauka saida ta tabbata ta tsaya ta kofar gidan su ta kawo takarda ta baiwa wani yaro tace ya shiga ya kai yace ance Muhd za'a bai mawa sana ta kawo kudi ta bawa yaron, ya wuce da gudu yana murna.
Washe gari kamar yanda sukai alkawari da karfe sha daya a gidan su Asiya tayi mata kuma bata jima da shiga ba itama agent din ta shigo, gaisawa kawai sukayi tace mata ta tashi su wuce dan sun kira ta zasu wuce airport bada jimawa ba, Maryam tayi wa su Asiya sallama da maman ta sana ta kawo en kudi ta basu suka rabu cikin mutunci. Tunda suka shiga taxi batai magana ba sai agent din ce ke gargadin ta akan tayi wa uwayen gidan ta biyayya dan gidan masu kudi ne manyan mutane zata kaita, har suka isa gidan Maryam ko uffan bata ce ba dan abinda ke damun ta shi yake damun ta.
Babban gida kamar a kira shi unguwa guda saboda girman shi, babu abinda Maryam ta lura dashi saboda hankalin ta gaba daya baya kan komai, a falo suka tarar da masu gidan sun fiffido traveling bags ana fita dasu a mota, nan dai aka gaisa sama sama wata mata ta kawo kudi dako kirgasu batai ba ta baiwa agent din.
Maryam dai na zaune agent din ta bar gidan baki washe alamun yau tayi babban samu kenan, a zaton Maryam matar da ta sallami agent din itace mai gidan amma tun kafin aje ko ina suka jiyo taku daga saman bene, wata hamshakiyar matashiyar mata ce ke taku a hankali kamar ba zata taka ba harta sakko aka hau gaishe ta sai wani yatsina take tana tambayar an gama saka kayan a boot? Kuma an kawo mai aikin da aka ce an samu? Matar nan data sallami agent ta russuna cikin ladabi take cewa duk anyi ranki ya dade ga kuma er aikin da zaku tafi da ita nan gami da nuna Maryam wacce ta rusuna itana cikin ladabi tana gaishe da matar.
Matar ta dan kurawa Maryam ido kafin ya daga kafada alamun ko oho sai kuma tace shikenan mu zamu wuce Asabe da Allah a kula da gida kamar yanda aka saba, har bakin mota suka raka matar gidan ana mata Allah Ya kiyaye tana ansawa kai a dage, motoci biyu ne masu zuwa airport din, wacce matar gidan ta kira da Asabe tayi hanzarin nunawa maryam karamar motar tace taje ta shiga waccan. Private jet suka shiga ya daga dasu zuwa Lagos, Maryam dai a tsorace tace kamar tayi kuka saboda bata taba ganin jirgi ba bare ta shiga gashi kuma matar bata kula ta, tamayi kamar bata san cewa tare suke ba.
Tafiyar kusan awa daya ya kaisu saman jirgin Murtala Muhammad dake birnin na Lagos, nan ma wasu motocin ne har uku kuma duk manya suka zo tarar su, daga cikin mota daya wata yarinya er budurwa ta fito tayo a guje ta rungume matar da har yanzu maryam bata san sunan ta ba, sai a lokacin maryam taga hakoran matar ta wangale tana daria cikin jin dadi, tana shafawa yarinyar kai tana tambayar ta ya take? A haka suka shige mota daya sai maryam wani driver ya nuna mata wata mota cikin ukun dai, ta shige tana sakin ajiyar zucia jin sanyin ac.
Tafiya sosai sukai kafin suka isa Victoria Island, maryam dai kam a wannan karon ta saki baki galala tana kallon wani anguwa mai cike da tsari mai masifar kyau ga wasu irin gine gine masu kyau, komai sai ya rika bata sha'awa har suka isa gidan mai katon black gate, maryam ta baza ido sosai tana kallon cikin gidan har falon da ta tabbata yafi na kaduna wanda suka baro, sai a lokacin matar ta kalle ta ta danyi tsaki tace Linda zata zo ta kaiki dakin da zaki rika zama sana dalilin dauko ki da nayi shine mai gida na ne zai koma Italy da zama kuma yana bukatar mu tafi tare nida shi harda diyar mu Alima, nasa a nemo mani ke saboda zan bukaci in tafi da mai aiki daga gida Nigeria saboda kula da Alima da gyaran dakunan mu, idan ya dawo anjima zan fada masa an samo ki zuwa gobe Monday sai aje a nemi passport dinki sai a hada dake wajen tafiyar ina fatan kin gane? Maryam ta kada kai tace eh Hajia, matar tayi saurin cewa ba sunana Hajia bane suna na Halima anma mutanen gidan suna fada man Aunty dan haka suna nan anty ba hajia ba, bata jira cewar maryam ba matar tayi saman dakin ta ita da alima.
Maryam dai a ranta tace ko wace rayuwa kuma nasa kai na? Da dare bayan mai gidan ya dawo aka kira maryam tazo ta gaishe shi ya rika bin maryam da kallo a ranshi yana jinjina taya iyayen ta suka amince yarinya karama tabar gaban su zata tafi wata uwa dunia? Alh Ahmad ya danyi gajeran tsaki cike da haushin iyaye masu kai yara aikatau. Cikin kwana uku passport ya samu aka hau neman visar maryam kasancewar su sun samu tuni, itama bata jima ba aka samu sai suka yanki ticket sai Italy ranar wata Juma'a.
Rayuwar su a Italy gata nan dai ne dan a yini baifi maryam ta saka anty a ido sau daya ba har gara alima kafin ta wuce school ita ke hada mata abincin da aka koya mata saboda alimar da Alh Ahmad dan ita anty abincin gwangwani kawai take ci, sana tunda suka zo kullum kafar ta a waje ta tafi neman kudi kasancewar abinda ya maido su Italy da zama kenan wato kasuwancin Alh Ahmad da yayi karfi na ban mamaki, gaba daya bata san meke faruwa cikin gidan ta ba shiyasa hankalin ta baikai ga matashin cikin maryam daya fara fitowa ba.
Alh Ahmad ne ya lura kasancewar maryam din ke gyara mashi daki, itace abincin shi, itace wanke kananan kayan sa underwears, itace wanke toilet din shi, akai sa'a shi kuma abincin hausa sosai yake so dan haka baya missing abincin maryam, gashi babu ruwan shi babban mutum mai shekaru a kalla arba'in da wani abu amma ba girman kai, ga jan en aikin gidan da wasa da hira, yana kuma tambayar su ko suna da damuwa to a haka suka saba shida maryam da kuma alima dayake halin uban ta dauko yarinya yar shekara 13.
A hankali maryam ta fahimci da alh kabir da suke cewa abba da anty basa shiri sosai, kusan kowa harkar gaban shi yakeyi cikin su, dayake abinda babu ruwanta ne sai bata taba nuna ta fahimci da wani abu tsakanin su ba. Abba shiya fahimci maryam nada ciki duk da baida tabbas amma yasan ba haka suka zo da ita daga gida Nigeria ba dan haka yasa ta gaba suka isa asibiti a inda likita ya tabbatar mashi da tana da ciki na wata hudu da en kwanaki. Hankalin shi ya tashi kamar zaiyi kuka ya saka maryam gaba yana tambayar ta game da ciki, bata wani tsaya boye boye ba ta bashi labarin rayuwar ta, nan Abba ya nuna mata kuskuren abinda tayi gashu kuma ta kara aikata wani kuskuren na barin kasar ta gaba daya ma, maryam na kuka tana fadin tasan bata kyauta ba kuma kullum abinda tayi yana hunting dinta ta kasa samun nutsuwa ma. Nan dai Abba ya mata alkawarin zame mata uba ita da abinda zata haifa har Allah Ya maida su gida, ya kuma yi mata alkawarin zata koma school bayan ta haihu tunda tana da background dinta.
Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now