Auren Sirri 12

193 16 4
                                    

🔐Auren Sirri🔐 1️⃣2️⃣
Da tsananin fushi Maaman Nadia ta shiga gidan su King amma ganin da alamun gidan ma cikin tashin hankali yake yasa ta dan danne nata fushin ta kalli Mummy a sheke tace kinji irin kalaman cin fuskar da King yayiwa Nadia kuwa? Mummy ta saki huci tace bari kawai ni ya fara yiwa rashin kunya dan bakiji abinda yau King ya fada mani ba kan wannan yarinyar da mukai tunanin ya hakura da ita, nan ta zayyanawa Maama duk yanda sukayi, ita kuma Maaman ta fada mata yanda Nadia ta fada mata na yanda King din yaci mata fuska, sai duk sukayi shiru alamun neman mafita.
Amira dake zaune tana sauraren su tace Mummy da Maama mezai hana tunda gobe sukeyin final exam mu shirya mu duka da nufin munje taya King Murnar gama second degree dinshi inyaso saimu nemi ita yarinyar a boye ba tare daya sani ba sai ayi mata warning dinda zaisa dole ta rabu dashi, ko kuwa ya kuka gani ta karashe maganar ta da kallon Amatullahi, Amatullahi tace nima dai nayi wannan tunanin amma bansani ba ko Mummy zata amince ba shiyasa nayi shiru, Maama tayi karaf tace yo wani irin kin amincewa? Ai yama kamata mu nemi ganin yarinyar da tasa King yake kin Nadia saboda ita, nan dai sukai amanna da zuwan su school din amma ba tare da King ko Amal sun sani ba dan ma kada su rusa musu shirin su. To da wannan suka tashi.
Bangaren su Ayisha kuma ta sanawar Mamy duk yanda sukai da King kuma Mamyn ta kara mata karfin gwiwar ta bashi hadin kai yayiwa iyayen shi biyayya, ita kishiya indai ba mai mugun hali bace to abokiyar zama ce, suna cikin maganar Adnan ya shigo ya zauna, ganin wannan damar sai Mamy ta gyara murya tace musu su bata hankalin su dan zata gaya masu wani batu ne, jin hakan duk sai suka maida hankali gare ta. Mamy tayi kasa da kai tayi shiru kafin ta dago ta kalle su ta fara da bansan ma ta inda zan fara fada maku ba amma koma yayane nasan dole zan fada maku dan haka abinda nake nema wajen ku shine hadin kanku da goyon bayan ku har kullum a cikin abinda nayi hukunci, shin ko zan samu? Adnan ne ya kada kai alamun eh, ita kuma Ayisha tayi murmushi tace Mamy mu masu biyayya ne wa umurnin ki muddin ba sabon Ubangiji bane, koda muna so ko bama so zamu baki hadin kai da goyon baya In Sha Allahu dan haka ki fada mana koma meye mu munyi alkawarin maki biyayya cikin abinda kika umurce mu ko Adnan? Adnan din yace gaskia ne big sis.
Mamyn ta saki ajiyar zucia tace na yanke hukuncin jibi in Allah Ya kaimu zamu koma kasar mu ta haihuwa dan dama na taba fada maku mu ba en nan kasar bane, kaddarar zama anan ne yasa nazo nan har na haife ku duka dan haka yanzu ina so mu koma cikin iyaye da en uwan mu muyi rayuwa dasu kuma, nayi duk abinda zanyi na gama har aiki na aje dama gobe ne last day dina na zuwa aikin ke koma a gobe ne kuke gama exams Adnan kuma yana hutu ne to idan muka samu isa kasar mu sai a nema mashi school a can yaci gaba.
Cikin murmushi Ayisha tace a ranta 'ashe da rabon ganin wani namu? Ashe zamu samu gatan en uwa? Ashe kukan Mamy yazo karshe? Adnan ya katse ta da cewa Big Sis ni banda matsala ke fa? Zaki bar Uncle King, Mamy tace ai asalin su King ma en kasar mu ne dan haka daga karshe duk zamu hade a kasa daya saidai ko garin su ne ban sani ba ko zai zama daya da namu Allahu A'alamu. Ayisha tayi murmushi tace ni yanzu yanda za'awa King auren nan ai garama in danyi nesa dashi idan baya gani na wata kila zaifi amincewa ya bada hadin kai da auren dan haka har garama Amal nafi jin rabuwa da ita duk da inda rai da rabo wata rana zamu gana. Mamy tayi murmushi tace Allah Ya maku albarka hakika bana shakkar ku bana shayin ku, Ubangiji Ya baku wa'anda zasu maku biyayya har fiye da yanda kuke mani, ta karishe da fadin gobe in Allah Ya kaimu kafin ku fito exam zamu zo nida Adnan mu taho dake gida. Da wannan kowa ya wuce dakin shi, Ayisha tayi niyyan kiran King ta fada mashi amma sai tayi tunanin yanzu fa data fada mashi shikenan bazai sake samun nutsuwa ba ga exam da zasuyi gobe in Allah Ya kaimu sai kawai ta fasa da niyyar idan suka fito exam din zata fada mashi, da wannan itama ta kwanta bacci.
** **
Washe gari duk wani dalibi mai rubuta final paper idan ka kalli fuskar shi zaka tabbatar yana cikin farin ciki, ga turawa nan da wasu jinsin iri daban daban kowa cike yake da farin ciki suka shige zana jarabarwar su ta karshe, yayin da wasun su anzo musu taya su murnar gama jarabawa kafin school tayi bikin yaye dalibai, daga ciki harda Mamy da Adnan da suka ci ado na sosai suka zo taya Ayisha murna su kansu daka kallesu zaka tabbatar da annurin fuskar su. Mummy,Maama,Nadia,Amatullahi da Amira su kansu sun samu karasowa kamar yanda suka furta zasu zo domin ganin Hamshakiya Ayisha, mota biyu suka karaso. Amal kuma na can zaune inda suka saba zama idan sunzo tana sauraran fitowar su King da Ayisha domin taya su murna, a zaton ta a sace ta fito zuwa school ba tare da en gidan su sun sani ba saidai bata san suma suna nan school din ba.
Lokaci mai saurin tafiya tuni time ya shige suka gama cike da fatan nasara, suna fitowa kafin su karasa fita ne suka dan dakata yawancin dalibai ana taya juna murna. Haka King da Ayisha sun taya junan su murna kamar babu abinda yake damun su a haka suka karasa fitowa farfajiyar school din da nufin isa wajen Amal dake zaman jiran fitowar su suna tafe kn hanya King ya kalli Ayisha yace Babe ina da shawara idan zaki amince, Ayisha tace ina jin ka King ya akai ne? King baigi sanya ba ya furta mata abinda ke zuciyar shi yace 'A daren jiya na yanke shawarar in fada maki idan kin amince ni na kudiri aniyar auren ki ako wani hali dan haka koda en gidan mu da naki iyayen sunki amincewa da auren to mu gudu muje wani waje a daura mana auren mu sai mu dawo daga baya ko kuma muje muyi aure cikin sirri ba tare da sanin wanin su ba ciki kuwa harda Amal duk da nasan ba zata bamu matsala ba. Bata katse shi ba har yakai aya sana tana murmushi tace King na amince maka ka auri Nadia ka zauna da ita in yaso daga ni sai ka aure ni, dan haka ka dena tada hankalin ka har kana kawo irin wannan shawarwarin domin waje na kam babu daya da zan iya dauka inyi dan haka kayi hakuri mubi a hankali, kuma akwai maganar da nake so in fada maka, bata jira amsawar sa ba tace gobe idan Allah Ya kaimu zamu taf.... sai wata mummunar ingiza Ayisha taji an mata ta tafi taga taga zata fadi, cikin wani mugun hanzari King ya riko hannun ta ta fada jikin shi ya rungume ta sosai ba tare da yayi niyyar hakan ba, Mummy data kara so wajen ta matsar da Nadia tana cewa ai ba ingizawa kadai zaki mata ba kamata yayi ki rufe tsinanniya da duka, Maama kuma ta finciko hannun Ayisha tana fadin kinji man karuwar yarinya ko kunyar idon mu bakiyi zaki rungume shi a gaban mu? Nadia ma ta anshe to kiji ki kara ji King nawa ne ni daya kuma ni iyayan shi suka amince mawa da in aure shi bake jahila,kidahuma, dakikiya, karuwar tit... marin da King ya kwashe Nadia dashi ne yasa ta shiru ta dafe gurin tana kallon shi.
Cikin zafin nama da shammata Maaman Nadia ta kifawa Ayisha mari har biyu itama tana huci tana fadin babu tsinanniyar da za'a mari gudan jini na saboda ita in kyale ba kuma bakayi mani kyawun kai ba dabaka sa hannu ka hada dani ka mara ba dan marasa tarbiya, wai a maimakon Mummy taji haushin karshen kalaman Maama sai ma ta matso tana zuba nata ruwan bala'in wanda hakan yai daidai da karisowar Mamy, Adnan da Amal a lokaci guda, cikin sauri Mamy ta karasa ta kamo hannun Ayisha ba tare data furta komi ba sai Adnan da Amal ne keta huci kamar macizai. Kamar daga sama Mamy da Ayisha sukaji zancan Maman Nadia inda take cewa to haka yanzu naji magana ashe karuwanci ba koyo kikayi ba gado ne kikayi wajen uwar ki Maryam, to gara da Allah Ya kawo mu nan muka gani da idon mu dan munsan komai na karuwancin uwar ki da haihuwar ki da tayi da kanin ki data haifa duk a karuwanci. Mummy ta kama itama tana fadin kwarai kuwa idan maye yaci ya manta ai uwar da ba zata manta ba, Ke Maryam kin san mu kinsan asalin mu kin kuma san aure ya kawo nan ke kuwa fa ba yawon karuwanci ya fito dake ba har kika haifi yaran ki biyu? Cikin wata irin muguwar tsawa Mamy tace enough is enough, da da yanzu ba daya bane idan ada na kyale ku a yanzu daidai nike da ko wacce daga cikin su zanci mutuncin ku ne kamar yanda kuke mani kuma karuwanci aiba kai na farau ba kuma na tabbata ba za'a kare a kai na ba dan haka kuje kuyi ta fadin abinda kuka ga dama kuma King ne gaku ga shinan kuje ku dafa shi ku cinye ko ku aura masa duk matan duniyar nan, ai ban taba tunanin yaron ki bane da tuni na tsaida alakar su amma ko a yanzu ma ban makara ba daga yau yanda Ayisha tabar cikina haka ta bar King, Mamy taja hannun Ayisha da Adnan cikin tsananin fushi mai hade da tashin hankali zasu bar wajen.
King da yake tsaye kamar body guard sai ya rasa meke damun shi wasu irin taurari kawai yake gani a idon shi kamar zai fadi amma duk da haka sunan Ayisha yake kira yana fadin karta barshi karta tafi yana son ta, Amal tazo taja hannun shi ta tura shi mota ta tayar da motar zuwa gida amma basui nisa ba ta lura da yanayin King yana bukatar asibiti dan haka ta juya kan mota zuwa hospital.
  A cikin motar su Mamy ma an rasa wanda zai driving zuwa gida saboda gaba dayan su jikin su a sanyaye yake ita Mamy ma kuma takeyi na fitar hankali, yayin da Ayisha da Adnan ba zaka iya fadin halin da suke ciki ba gasu nan dai kamar gumaka sun ma rasa tunanin da zasuyi har awa daya ya wuce, ko kukan ne Mamy taji ya ishe ta oho ta dai goge hawayen ta taja motar cikin rashin karfin jiki suka bar school din zuwa gida.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now