Auren Sirri 25

153 15 3
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣5️⃣

Ahmad yace Maryam har bana son tuna baya, amma tunda ke ce dole zan fada maki.
Bayan rabuwa ta da ke kai tsaye Abuja na wuce gidan iyaye na, Allah Ne Ya kaini lafia ma dan tsananin gudun da nakeyi a lokacin nasan komai ma yana iya faruwa dani, kuma ba komai bane sai azabar zafin da zucia ta keyi saboda kishi. Sister na Aina'u wacce muke kira da Aina ita taga shigata side dina kamar ba'a hayyaci na ba dan haka sai kawai taje ta sanar wa Umman mu ga Yaya Ahmad can ya dawo amma tana tunanin ba lafia ba, babu bata lokaci Umman mu tazo tana buga mani kofa amma ko kasa tashi nayi bare in bude kofar, a takaice har dare ban bude kofa ba har Abban mu ya dawo shima aka sanar masa yazo yayi nashi ban bakin amma na kasa budewa. Saida na kwana uku cikin daki ni daya babu abinda nake ci da sha sai biscuits da drinks da ruwan dake daki na kafin a rana ta ukuAbba yasa aka zo aka bude kofar.
Kai tsaye hospital sukayi dani wai a duba kwakwalwata aga ko na samu tabin hankali? Bayan binciken likitocin suka tabbatar musu lafiyar kwakwalwata lau amma aje a duba jiki na ko anan nake da wani ciwo, nan ma aka tabbatar musu lafia ta lau amma da alamun zan iya samun hawan jini any moment saboda bana cikin nutsuwar zucia ta ga kuma bugun zuciya ta daya canja, hankalin iyaye na ya tashi kwarai suka hau roko na akan in fada musu damuwa ta ni kuma kai tsaye na fada musu ina son barin kasar ne zan koma America karo karatu.
Wallahi maryam cikin kwana uku komai ya kammala saboda da ni da Aina'u duka a America aka haife mu dan haka muna da Passport na can, ranar da zan tafi babu yanda Umma batai ba akan in fada mata damuwa ta, amma na kasa fada mata komai, har shigowar Hady data dawo daga Kaduna a lokacin ta tarar da batun tafiya ta wanda yasa ita kuma tayi dan karamin hauka tana ganin ga samu ga rashi, har daki na ta bini tana roko na akan kada in tafi kuma idan na matsa akan tafiyar to in yarda a daura mana aure koda daga baya ne sai ita ta biyo ni, wallahi yanda kika san da dutsi take magana domin bansan tana yi ba, kai ni bala'in haushin ta daya kama ni bansan sanda na wanke ta da mari ba, marin dana mata ne ya husata ta har ta fara fadaman maganganu cewar in har na duke ta saboda wannan figaggar maryam din to in shirya dukan ta har Allah Ya karar da numfashin mu domin so na yanzu ta fara ba kuma zata dena ba kuma tana rokon Allah Ya kara nesanta maryam da ni, yarinyar da tasa har nayi aure bada sanin iyayena ba aiba matar mutunci bace bare ma mai kawo katon namiji har gadon bacci na, maryam in takaice maki sai gani na zama wani bala'i taccen mutum na hau hadiza da duka saboda tuno mani da abinda ya faru da tayi, Umman mu datayi niyyar shigowa ta fasa saboda jin abinda hady ke fada sai ta dakata amma jin dukan dana hau hady dashi sai tayi saurin shigowa ta janye hady, sai ma ta hau masifa cewar in dai abinda taji hadyn ta fada da gaske ne to lallai in shirya auren hady gobe goben nan haka kuma in shirya tafiya da Hady America, tunda har zan iya yin aure ba tare da sanin su ba to lallai auren Hady ba zai zame mani matsala ba kuma dama can iskanci ne yasa naki auren tunda gashi nan nayi a wani waje, haka Abba ya dawo ta sanar mashi shima ya hau ni da fada ya kuma goyi bayan a fasa tafiyata yau har sai anyi auren mu da Hady sana mu tafi tare.
Washe gari inaji ina gani suka daura mana aure da Hady wacce keta murna yau ta auri wanda take so yayin da a rai na babu abinda nake sai tausaya mata saboda na so har ga Allah taje ta auri wanda ke son ta bani ba amma tunda ta matsa shikenan ita ta jiyo. Saida muka kara shafe kusan wata daya sana aka samu visar Hady tunda ita bata da passport din America, bayan mun sauka America nida Hady sai gaba daya na kauracewa flat din da Abba ya kama mana haya, Hady bata kara sakani a ido ba hakan yasa data gaji ta kira Umma tana kuka ta fada mata abinda kenan, Umma ta kira ta rika man fada hakan yasa dole na koma gidan amma karatun daya kawo ni sai na kasa yinsa gaba daya, babu dai wani zaman lafia tsakanin mu duk kuwa da iya kokarin da Hady takeyi dan ganin taja hankali na hakan kasa samuwa yayi.
Kullum babu abinda ke rai na sai maryam, nayi kewar ta iya kewa kuma ina bukatar ganin ta da jin muryar ta, amma sai mi? Dana tuna maryam sai kuma in tuna ganin namiji kwance bayan ta da nayi sai inji na tsani kai na kuma na tsani maryam, a haka Usman ya tarar damu America wani zuwa da sukayi shida mutanen gidan su, anan yake fada man rashin jin dadin shi na abinda na aikata dan tun sanda abun ya faru na sanar dashi kasancewar baya nan, dan haka sai zuwan su America ya rika yi man fada yana nuna mani rashin halaccin dana yi wa maryam yayin da nake kokarin nuna mashi abinda maryam din tayi. Usman yayi dariyar takaici yace Ahmad ba wai ina so in shiga tsakanin ka da er uwar ka kuma matar ka Hady ba amma let me ask u a question, do u trust hady and her friend back then? Nayi shiru ina tuna abinda ya faru farkon zuwan Hady kaduna, anan Usman yaci gaba da fada man lallai akwai wani lauje cikin nadi wanda idan na bincika to nadin zai kwance in fahimci gaskia, usman yaci gaba da fada man maryam yarinya ce karama da bata saba da kowa ba idan ba kai ba, yarinya ce mai tarbiya da take kuma duba iyayen ta kafin ta aikata wani abu, ni nasan tuni zasui mata wayau kafin su kafa abinda suke bukata dan haka kaje kayi bincike dai. Cikin sanyin jiki na tambayi usman taya zan bincika? Usman din ya bani shawarar inyi wa Hady rijiya lallai idan bata da gaskia to zata fada.
Haka kuwa akayi bayan tafiyar su Usman kai tsaye na fara confronting Hady na fada mata ita da salma suka shirya abinda ya faru tsakani na da Maryam, sai Hady ta fara kuka tana roko na in yafe mata tayi ne saboda tana so na kuma bata iya hada ni da wata macen, tun daga ranar hady ta kuma dena ganina saida nayi wata daya kafin in dawo gidan. Dana koma kuma sai muke zaune kadaran kadahan shima sakamakon shawarar usman ne akan kada in bari saboda tunanin abinda nayi wa maryam in kuma jefa kai na cikin bala'i domin hakkin Hady zaya iya kama ni. Abu na gaba shine buri na na siyasa ma saiya fita rai na saboda rashin maryam lallai ya tafiyar da abubuwa da yawa cikin rayuwa ta, hakanan a daddafe nayi karatun na gama sana muka shirya dawowa Nigeria. Muna dawowa na nufi kaduna saboda nayi sa'a usman yana kaduna anan ne mukaje gidan ku da nufin mu bada hakuri sai muka tarar da baki nan basu ma san inda kike ba, wannan ya kara dagula lissafi na harya shafi batun aikin da Abba ya sama mani amma ban taba zuwa ba, sai kawai ya yanke shawarar ya bani kudi in fara kasuwanci a hankali har in kware. A cikin kankanin lokaci Allah Yayi albarka cikin kasuwancin, nayi kudi sosai wanda hakan yasa hankalin Hady ke tashi dan gani takeyi saboda kudin da nayi koda ni ban bukaci inga baby na ba to iyaye na zasu bukaci gani saidai sabanin tunanin ta akai na ni ban taba tunanin ganin dan kai na ba idan ba cikin da maryam ke dauke dashi ba sai kuma ita maryam din, amma hasashen ta akan iyaye na ya tabbata domin bamuyi shekara goma da aure ba suka matsa akan in kara aure ko Allah Zaisa a dace in samu rabon haihuwa wani waje, kullum magana ta shine nifa ina da diya ko da a wajen maryam dan haka bana bukatar wani yaro dan bani da shirin kara aure, har dai aka fara samun sabani tsakanin umman mu da hady, umma tana tunanin ko hady ce tayi wani abu yasa bana ma son ayi man maganar karin aure yayin da hadyn take tunanin meyasa dan kawai Allah Bai bata haihuwa ba Umma zata matsa sai in kara aure ko zan samu haihuwa.
Rana bata taba wucewa ba tare da maryam a cikin zucia ta da cikin da take dauke dashi ba, kullum addu'a ta Allah Ya bayyana maryam da abinda ta haife mani duk da bani da tabbacin ta haife cikin amma abu daya dake karfafa man gwiwar haife cikin shine maryam ba zata taba zubar da ciki ba indai na san maryam to nasan ba zata aikata hakan ba saidai ko idan Allah Ya kawo tsautsayi cikin ya zube wanda kuma bana fata. A haka na shafe shekarun nan ba tare da na samu haihuwa da hady ba bare kuma maganar kara aure, umma har tayi ta gaji ta dena, itama hadyn da ada ta dagawa kanta hankali akan bata haihu ba yanzu ta dena ta fahimci Allah Ne bai bata ba gashi kuma an girma. Ahmad ya karashe zancan sa da cewa nidai kam yanzu sai dai in dawwama ina wa Allah Godia ta daban sakamakon samun maryam da nayi da kuma gudan jini na dan haka maryam yaushe za'a maida auren mu, ya karashe mata tambayar yana langabe kai kamar matashin saurayi.
Mamy tayi daria ganin yanda ya langabe kai tace to ni yanzu Ahmad ai na fara tsoron ka tun yau ba'a dena murnar dawowa ta ba an murde mani hannu inaga nan gaba? Ai kila ko gani kayi na gaisa da wani namijin sai inda karfin ka ya kare dan haka... shshshsh Ahmad yace gami da ci gaba da cewa 'Ki kwantar da hankalin ki domin babu abinda zai kuma raba mu sai mutuwa In Sha Allahu so save your words' sana kuma ko ada ban hana ki gaisawa da maza ba kawai dai idan namijin ya hada da zancan yana son ki ne ke bana iya jurewa. Mamy ta kada kai gami da kokarin bude kofa, saboda tuni suka shiga gidan su hibban basu dai bar cikin mota bane, ahmad yayi saurin ficewa bayan an bude mashi kofa yana cewa maryam ki dena wahalar da kanki let me open the door for you. Bayan ya bude mata suka jera shiga cikin ainihin gidan, suna tafiya maryam na yaba tsarin gidan tana jin dadin little sister dinta ne a gidan.
Ayisha da Adnan ne suka rugo da gudu kamar wa'anda sukai shekara daya basu ga Mamyn ba suka rungume ta suna sakar mata kiss alamun sunyi kewar ta, itama mamyn ta rungume su duka tana jin dadin ganin su sun sake gidan kanwar ta, ahmad na tsaye gefe ya rungume hannuwa a kirji yana kallon su cikin wani irin madaukakin farin ciki marar misaltuwa a gare shi, yana jin a ranshi lallai yau baisan yawan sadakar da zaiyi ba, yanzu wannan zuqeqiyar yarinyar itace babyn shi? Yana da ita sama da shekara ishirin amma bai sani ba? Bai taba bata irin wannan son da maryam take basu ba na mahaifa ba? Sai kwalla suka taru a idon shi yayi hanzarin gogewa kada su gani amma a idon mamy data juyo zata mashi magana da kuma usman da hibba da suka fito tarar su.
Usman cikin barkwanci yace wato aboki na har yau kukan bai kare ba, yau kuma na ganin yaran mu ne ko na ganin maryamu hodar idaniyar ka ne? Hibba tayi daria tace my dear ba zaka dena tsokanar yayana ba ko? Mamy tayi murmushi ta saki ayisha da adnan gami da jan hannayen su har gaban ahmad sana tace ayisha da adnan yau ga baban ku Ahmad na sada ku da shi, ta kai duban ta ga adnan tace nasan bana bukatar sanar da kai ka rike ahmad tamkar shi ya haife ka right? Adnan da ayisha da tuni suka rungume shi basu ma san me mamyn ke fada ba, jin Ayisha da Adnan cikin kirjin Ahmad bai san sadda ruwan hawaye suka biyo fuskar shi ba, ashe haka iyaye keji idan suna da yara? Haka soyayyar iyaye take ga yaran su dama? Wannan abin da yake ji a zuciyar shi lallai yafi karfin so, hala wani abin ne wanda baya da misali anan dunia? Harta adnan haka ahmad yake jin soyayyar shi a zuciyar shi tamkar shi ne ya haife shi musamman da yake tuna yanda aka fada mashi rikon da mahaifin adnan din yayi ma tashi diyar.
Ayisha da Adnan suka saki Ahmad yayin da shi kuma ya damke hannuwan su cikin nashi, sai kuma ya hau cewa kuyi hakuri yarana bansan daku ba a dunia, ban baku soyayyar iyaye ba amma yanzu I promise u sai kun ture soyayyar uba da uwa dan duka zan hada in baku, ku daina wahalar mun da maryam hakanan kuma nima ku bani koda rabi rabin son da kukewa maryam ne.
Ayisha da Adnan sukayi daria, Ayisha tace Abba sunan ta Mamy ne ba Maryam ba, Ahmad ya buge bakin shi yana cewa oppss my bad, daga yanzu mamy sunan ta ba maryam ba, aka saka daria gaba daya kafin suka nufi cikin falon. Ahmad ya kafe ya tsare Ayisha da Adnan suna tare dashi a kan two seater, motsi kadan idan dayan su yayi zakaji Ahmad ya fara tambaya what do u want? Tuni su kuma suka sake dashi suma suna jin yanayin kaunar shi a zuciyar su musamman ta yanda yake ta lallaba su. Wayar shi da tun dazu ke vibrating yanzu ma ta hau bugawa, Ayisha tace Abba your phone is ringing, Ahmad yace barta kawai Ayisha domin yau gaba daya ranar ku ce.
Haka suka sha hira kafin su tattara zasu koma gidan su Mamy, kafin su wuce Ahmad yace to yau dai nima a bani yara na hakanan Hibba inje inji dumin su nima suji dumin Abban su, hibba tayi daria tace da wannan Yaya Ahmad ai gara kawai ayi a maida auren nan kowa ya huta dan mun lura ba barin mu zakai musha iska ba, Ahmad yayi hanzarin kallon mamy at the same time yana maidawa hibba ansa da cewa hibba kamar kin shiga zucia ta ne kuma tun a mota nake wa mamy magana amma tana nema ta tsaida abun, ahmad ya maida kallon shi ga Adnan yace Adnan kana son mu tafi gidan mu
Abuja a maida ka school kada karatu ya wuce ka ko? Adnan din ya daga kai yace eh Abba, Ayisha ma tace eh gaskia kada karatun Adnan ya tsaya, Usman da Hibba suka hada baki wajen cewa suma suna bayan yaran dan haka ayi sauri a maida auren su tattara su koma.
Ganin kamar duk sun hade mata baki yasa Mamy tace to wai ni nace kada a maida aure ne da kuke ta babatun magana? Ahmad yayi hanzarin cewa Masha Allah dan haka Usman gobe kuzo daurin auren mu da Mamy, bai jira cewar kowa ba yaja hannun yaran suna daria suka bar falon.
Mamy data kasa cewa komai sai binsu da ido tayi, tana tambayar kanta wannan wane irin zumudi ne haka? Yaushe ta dawo da har za'ayi aure? Ashe a fili tayi maganar sai Usman ya ansa mata da cewa akan ki bana tunanin akwai abinda Ahmad ba zai iya yi ba dan haka karkiga laifin sa, jiran daya yi ya isa hakanan, Hibba ma tace nima ina bayan yayana. Ganin duk sun goya masa baya sai kawai mamy ta musu sallama tana rungume yaran hibban daya bayan daya kafin ta wuce wajen mota. Ahmad ne ya bude mata mota yana cewa bafa zan raba mota da yara na ba dan haka saidai kiyi hakuri ki shiga mu kutsa ciki mu duka a baya, mamy cikin mamaki tace yanzu duk motocin nan hudu sai ace a mota daya zamu kutsa mu duka? Kai ku fito ga mota can ku shiga ko kuma ni in shiga can din, Ahmad ya langabe kai yace yanzu mamy ba zaki ji tausayi na kiyi abinda nake so ba? Mamy tace Ya Ilahi! Wannan bawan naka yana nema ya saka mani headache, dole sai Adnan ya shiga gaban motar su uku kuma suka shiga a baya a haka suka karasa gidan su Mamyn.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now