Auren Sirri 19

121 15 4
                                    

🔐Auren sirri🔐 1️⃣9️⃣

Sakamako ya nuna Maryam na da shigar karamin ciki na wata daya da en kwanaki, zufa tako ina barko mata takeyi, gabanta banda dukan uku uku babu abinda yake a haka tabar clinic din ta wuce kai tsaye gidan Ahmad domin ta sanar mashi saisu nemo mafita. Kasancewar kai tsaye babu inda Maryam bata shiga a dan karamin gidan na Ahmad yasa yanzu ma ta kusa kai falon gidan inda anan tayi kyakykyawan ganin wata matashiyar budurwa rungume da Ahmad tana kuka tana rokon shi su koma Abuja a musu aure tunda ya gama service kafin komawar sa USA ci gaba da karatun shi.. Maryam ta saki salati jikin ta ya hau kyarma cikin in ina take nuna Ahmad da budurwar tana cewa Ah..m.ad wa wace wa..n batama ida sa magana ba kawai ta rushe da kuka ta durkushe anan kasa, Ahmad wanda ya kwace kanshi daga jikin Hady ya iso wajen Maryam cikin azama ya mikar da ita duk ya rude yana cewa Maryam abinda kike tunani bashi bane and i can explain my self, Maryam ta fisge tana mashi wani irin kallon tsana tace explain? What can u possible explain Ahmad? Ka cuce ni ban yafe maka ba, ta juya da gudu ta fice daga gidan tana fita kuma tayi sa'ar taxi ta shige tana kuka ta wuce gida.
Ahmad bai samu nasarar rike ta ba kafin ta shige taxi din ba, saiya dawo gidan cikin mugun bacin rai ya kwashe Hady da mari ya hauta da masifa, tunda hankalin ki ya kwanta saiki fice man daga gida, aure kuma nace banayi dake waccan data fita daga gidan nan ita nake so ita ce matata daga nan dunia har lahira, kuma ke baki isa ki hadani da ita ba, fuu ya shige ya dauko key din motar sa da nufin ya je wajen Maryam. Hady ta rike mashi hannu gam tana masifa itama wallahi Ahmad kai baka isa ka hanani abinda nake so ba kuma tunda nace ina son ka to duniyar nan babu wanda ya isa ya hanani auren ka har kai kanka kuwa kayi kadan ka hanani samun ka a matsayin miji sana kuma waccan figaggiyar yarinyar daka ke wulakanta ni ashe kanta ne dama? Dalilin tane kaki komawa gida bayan ka gama service din toka sani a kunnen Mum, Ahmad ya kuma tsinke Hady da mari yace ba Mum ba ko Dad ne duk ki taru ki fada masu nace ban son ki kuma ba zan aure ki ba ita figaggiyar ita na gani ita nake so kuma ita nake aure yanzu haka, Hady na rike da kumatu ta dago da sauri tana cewa da kake ta maganar aure aure shin wai meye tsakanin ku ma? Ahmad ya banka mata harara yace tunda uwata ce ke aisai ki titsiyeni kisa in maki bayani banza mayya kawai, yaja tsaki ya ingije ta ya wuce yana cewa aiga gidan nan saiki ci gida idan ana ci.
Sai a lokacin Hady ta kai kallo ga bangon falon wanda ke dauke da hoton Ahmad da Maryam ranar data gama exams dinta, Maryam din ta dan kwanta bisa kafadar shi suna daria aka dauke su, ai tuni Hady ta haukace ta hau farfasa duk abinda taci karo dashi, saida tayi raga raga da falon kafin ta shiga bedroom anan ma hotunan Ahmad da Maryam ne akan side bed sunyi kyau kamar a sace su, wani suna daria wani suna murmushi, wani Ahmad ya kamo fuskar Maryam yana pecking forehead dinta, wani sun rike hannuwa, pictures dai gasu nan ga duka side bed din dakin an saka cikin kananan frames, nan ma Hady ta hau yarda duk abinda ta gani ta zubar da pictures din kasa tabi tana takawa da kafa, inka ganta duk ta haukace, cikin haka taci karo da Diary din Maryam wanda Ahmad ya ansa wai zaiga me take rubutawa, kasancewar sabon diary ne da Ahmad ya siya wa Maryam wata fita shopping da sukayi data nuna tana so shine ta dauko, ashe tana rubuta abubuwan da suka faru da ita ne, Hady ta nemi waje ta zauna tana bin diary din wanda kafin ta gama hawayen dake bulbula a fuskar ta sai su jika dan light handkerchief ga wani irin azabar kishin Ahmad din da takeyi sai kuma shock wai Ahmad yayi aure amma babu wanda ya sani ko iyayen shi basu sani ba, nan dai Hady ta kwanta zuciyar ta na tafasa da kyar ta lalubo wayar ta ta kira kawar ta wacce dama dalilin ta tazo kaduna, ba'a jima ba Salma tazo gidan Ahmad din, da kyar ta iya jan Hady suka bar gidan.
Suna tafiya Ahmad yana dawowa kasancewar bai samu ganin Maryam ba, kuma yana ta kiran wayar ta amma taki dauki saima ta kashe wayar gaba daya, haka ya karaci zama kofar gidan su amma baiga gittawar kowa ba, hardai ya gaji ya dawo gida inda ya tarar Hady ta birkita gidan gaba daya ya kada kai ya yi tsaki yace jaka kawai banda dabbanci babu abinda ta iya, nan ya fita ya nemo wasu samari matasa yasa su suka gyara gidan suka fitar da abin da ya lalace sana ya kawo kudi ya basu suka tafi suna murna.
Maryam tunda tabar gidan Ahmad take kuka harta isa gida, da kyar ta iya tsaida kukan ta biya mai taxi ta shiga gida, nan ma wata masifar ce ta Adamu da uwar shi Inna Indo wai sunzo tambaya yaushe za'a turo baban Adamu suzo a sanya ranar daurin aure ayi a gama hakanan tunda ta kare karatun da aka kwallafawa rai. Wannan karon Malam Isuhu yayi tsayin daka akan Maryam ba zata auri Adamu ba tunda shi din ba shiryayye bane, wani irin kuka da Inna Indo ke rusawa kai kace yanzu ne suka samu labarin mutuwar daya daga cikin iyayen su, yayin da Inna Fulera da Inna Fatsima ke kara rura wutar fadan, suna jaddada Rahane dai ta gama da Malam sai abinda take so akeyi, Maryam ta shigo a wannan halin sai duk suka bita da ido.
Adamun yayi hanzarin danko mata hannu dama yana kusa da dakin su Maryam din, saiko ya wullar da ita tsakiyar su, wannan yace wannan, wannan yace wannan ba iyayen mata ba ba kuma yaran su ba, hakan ya idasa haddasa rikicewar Maryam saita fara kwarara wani irin uban amai, tun tana yi da karfi harta koma yi a hankali kamar en cikin ta zasu fita, sai kuma duk suka koma kallon ta, kafin su ankara Maryam data fara ganin su biyu biyu sai kawai ta ida sulalewa kasa ta some anan, Malam Isuhu yayi kanta yana salati, abinda ya fiddo Inna Rahane da Muhd da Hibba kenan, sai kuma masu masifa suka koma kallon ikon Allah, Malam ne ya zabura ya fita neman mai taxi dan zuwa da Maryam asibiti, mintuna kalilan ya dawo da dan taxi suka kwashe ta sukai asibiti.
Bayan bincike likitan ya gano karamin cikin dake tare da Maryam shiya haddasa mata laulayi wanda yayi sanadin faduwar ta, Malam Isuhu gumi ya jike shi shakaf, Inna Lillahi kawai yake ambato, a haka ya isko Inna Rahane, ko ba'a fada ba ita dake babba tasan akwai abinda ya faru, duk wanda zaiga Malam a lokacin ma yasan akwai wani abun, sai kawai ta finciki hannun sa sukayi waje, cikin rawar baki take tambayar shi abinda ya faru, kamar bazai fada mata ba har kusan minti uku haka dai ya fada mata abinda likitan yace, sai Inna Rahane ta sulale kasa tasa wani marayan kuka, Malam ma binta kasan yayi dan shima kukan yake bukatar yayi amma dauriya irin ta maza yasa baiba.
Malam ne ya lura Inna Rahane bata da niyyar dainawa saiya fara lallashin ta akan tayi shiru su binciki al'amarin a hankali dan shi har yanzu yama kasa gasgata batun Maryam nada ciki. Da suka shigo dakin a lokacin sai suka rika binta da ido, kallon da suke mata ita kuma saita tsargu saita yi kasa da ido, hakan ya fusata Inna Rahane sai kawai ta rufe ta da duka tana fadin kin cuce mu Maryam, duk abinda muke kokarin muga munyi domin ki baki gani ba saida kika je kika dauko mana abin kunya, da kyar Malam ya janye ta ya fitar da ita waje sana ya dawo dakin ya cewa Muhd da Hibba su fita daga waje zaiyi magana da yayar su. A hankali kamar Malam baya so yake tambayar Maryam wanda ya mata ciki, banda kuka babu abinda Maryam din keyi, ganin tsayin lokaci sai Malam din ya tashi ya fice ya iske Inna Rahane da Muhd da Hibba zaune kowa yayi tagumi, anan ya sheda mata zaije gida ya dawo karaf Inna Rahane tace to ni zaman me zanyi wajen ta? Ta mike gami da jan hannun Hibba ta kalli Muhd tace ku wuce mu tafi gida, Hibba tana kokarin kwacewa tana fadin Inna ba zamu tafi da Yaya Maryam ba? Inna Rahane dai kamar ma ta zauce sai jan yaran takeyi, Malam na kallon ta amma ya kasa fadin komai sai nemo taxi da yayi suka shige suka wuce gida, wannan shine karshen rabon da Maryam ta saka iyayen ta ido bare en kannen ta masu tsananin son ta.

Mrs sS❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now