Auren Sirri 11

223 12 0
                                    

🔐Auren Sirri🔐1️⃣1️⃣

A daren ranar King kasa hakurin washe gari tayi sai kawai ya kira Ayisha da faduwan gaba ko zata dauki wayar ma saboda ya da suka rabu a school, bai gama wannan tunanin ba yaji muryarta cikin sanyi ta ansa, ajiyar zucia yayi kafin yaji bakin sa ya zarce da bata hakuri, ita abun ma sai ya nemi bata daria dan haka ta dan murmusa tace 'calm down King ka dena damun kanka mana komai ai rubuce yake a babin kaddarar dan adam dan haka babu damuwa sai muyi fatan Allah Yasa hakan yafi alkhairi kuma ni da na fada maka maganar na hakura dakai a lokacin ina ganin in taimaka kayiwa iyayen ka biyayya shine soyayyar da zan maka kuma har yanzu ina kan batun kayiwa iyayen ka biyayya ni na yarda idan da rabon muyi aure sai muyi, idan sun amince sai ka aure ni koda daga baya ne.
Wata irin nannauyan ajiyan zucia mai tafe da huci mai sa samun sauki a cikin zuciyar dan adam King ya saki, hakika ya tsaya furta batun jin dadin kalaman Ayisha ma bata lokaci ne amma duk da haka bai kasa a gwiwa ba ya nuna mata asalin jin dadin shi da kalaman sa masu dadi da kwantar da hankali ya kuma tabbatar mata ba za'a samu problem ba In Sha Allah dan haka zai samu iyayen nashi ya fada masu ya amince da batun Nadiyar sana kuma ya fada musu batun Ayishan, daga nan suka danyi magana kadan kafin suyi sallama da niyyar sai sun hadu school jibi wajen zana last exam dinsu. Exams din data nemi saka Ayisha dimaucewa sakamakon munanan kalaman da aka fada mata.
** **
Washe gari King ya samu Amal da batun yanda sukayi da Ayisha, tayi murmushi tace shikenan ma kaga ta hutar damu baka fada mata niyyar ka ba dan haka yanzu abinda ya rage saimu tunkari Daddy ka sanar mashi abinda kenan, daga nan suka nufi saman Daddy. Yana zaune yana aiki a computer da farin gilashin ido ya dago yana kallon su, guri suka nema suka zauna suka fara gaidashi ya ansa, alamu sun tabbata da magana a bakin su amma sunja baki sunyi shiru sai shine ya rufe computer din ya fuskance su sosai yace yadai Amal meke tafe daku? Cikin karfin gwiwa Amal tayiwa Daddy bayanin halin da ake ciki na batun Ayisha, Daddyn yayi shiru kamar ba zaice komai ba, hakan yasa gabansu fara faduwa ko bazai karbi maganar ba amma sabanin tunanin su sukaji yace 'yanzu kai King kana ganin zaka iya rike mata biyu? Da sauri King din ya gyada kai alamun eh zai iya. Daddy yace to ai shikenan babu damuwa saika bari a fara auren Nadiyar sai aje nema maka na dayar yarinyar, da wannan jin dadin suka baro saman Daddy kuma shima bai jima ba Daddyn ya fice.
Sunanan falo suna kara tattauna batun auren ashe duk a kunnuwan Mummy wata ashar data rika zunduma masu saida su Amatullahi da Amira da Nadiya data shigo bada jimawa ba suka sakko a sukwane wani na buge wani yayin da King da Amal sukai tsuru tsuru, Mummy taci gaba da fadin 'Ni yau na shiga uku na lalace da rai na nake shirin ganin bakar rana irin haka? To cikin gidan nan zanga uban da ya isa ya kawo man maganar wata Ayisha, ashe shiru shirun da kayi lafawa kayi kana kallon mu muna shirin biki to na fadi na kara fadi bani son zancan auran ka da waccan yarinyar, Nadia ita na amince maka daka aura kuma itace zaka aura da kana so da baka so dan bari ganin ina maka duk abinda kake so wallahi anan wajen kam zamu saba ni da kai mummunan sabawa kuwa, taja wani matsiyacin tsaki ta juya da niyyan barin falon taje ta kira Maman Nadia dan su san ta yanda zasu bullowa lamarin, bata kai ga fita ba taji King ya fara fadin 'Mummy ko zaki kashe ni sai na auri Ayisha babu wanda ya isa ya hanani auran Ayisha na rantse da Allah idan ban auri Ayisha ba to babu wata shegia da zan aura, kin saba bani duk abinda nakeso yanda bansan babu ba haka a yanzu ma bansan rashin Ayisha a rayuwata ba, muddin kikai yanda kikai kika hanani auran Ayisha lallai ki tabbata daga ranar kin rasa ni rashi na har abada dan banga amfanin rayuwar da zan zauna ina rayuwa da wata da bance ina so ba, wallahi kinji na rantse sai na auri Ayisha In Sha Allah! Yana rufe baki sai saukar mari ka yakeji tako ina cikin zafi Mummy ke marin shi tana fadin saidai inga gawar ka gabana da inga ka auri wata mace da kake wa irin wannan mummunan so din, dan ganin gawar ka zaifi man kwanciyar hankali da ace in sallamawa wata mace kai, wannan ma ba mai yiyuwa bane kuma naji na yarda ina baka dukkan abinda kake so da kai da en uwan ka amma ka sani na maku hakanan ne saboda son ku da nakeyi ba dan wata rana in zo muna sa'insa nida ku ba dan haka ya zama dole ka auri Nadia ita daya.
Amal tace 'Mummy please ki tsaya abi abun nan a hankali mana... gafara can munafukar banza da wofi ai duk a kunne na naji kuna maganar waccan yarinyar kuma banyi zaton a yanda nake muku duk abinda kuke so ke za'a hada baki dake ni kuki yiman abinda nake so ba, Amal tace Mummy muma zamuyi maki abinda kike so amma ya kamata ki fahimci zuciyar Dan uwana tayi nisa akan son Ayisha ba zaki iya raba su ba kuma a cikin alfarmomin da kike mana ya kamata ki saka wannan a ciki ki bar King ya auri zabin ranshi kuma ma fa yace zai auri itama Nadiyar karewa ma ita zai fara aure kafin Ayishar... dukan da Amal taji na shigar ta tako ina yasa ta rufe baki daga bayanin ta, Mummy data dawo kan Amal tana dukan ta tako ina tana cewa gara ni in karasa ki daki karasa ni dan na lura kece ke goyawa King baya yake kara tu'azzara da batun waccan yarinyar to gara in rika hucewa akan ki. Da kyar Amatullahi da Amira suka janye Mummy suna bata hakuri suka nufi daki da ita, yayin da King yazo ya daga Amal ya jata zasu wuce side dinshi saiji yayi Nadia ta kama hannun shi tana wani irin kuka na fitar hankali ta kasa magana, dakatawa yayi amma baice mata ci kanki ba dan bala'in haushin ta yake ji saboda duk dan ta kallafa rai a kanshi ne yasa tajaza masa shiga halin da yake ciki, kai shi ba karamin daurewa yake ba da baya huce haushin shi akan ta.
Cikin Kuka Nadia tace yanzu King ba zaka tausaya irin son da nake maka ba ka hakura ka aure ni muyi rayuwar mu cikin aminci ba? Mena maka da baka so na? Me na rasa? Dami ita Ayishan ta fini? Ilimi, Kudi, Kyawu, Asali ko minene? Tana direwa King ya ansa da ai Nadia idan kika hada kanki da Ayisha to kin cuce ta danta fiki komai a waje na, kuma ita din kanta nake so ba wani abu nata ba kuma na fada na kara fada lallai zan iya taimakawa in aure ki idan da maganar Auren Ayisha amma idan babu auren Ayisha lallai kema ki sani ba zaki taba samu na ba dan yanda kikeji a taki zuciyar to tawa ta lunka taki sau goma akan son da nakewa Ayisha, Ayisha itace rayuwata kuma ita ta fara gyara rayuwa ta akan gurbataccen hanyar da Mummy tabi damu, yana gama fadin hakan yaja Amal suka ci gaba da tafiya sun kusa shan kwanar da zata sada su da side din King ya tsaya ya juyo ya kalli Nadia yace 'Ayisha kyakykyawar zuciyar ta da kyawun tarbiyar ta da lifestyle dinta su suka jani ga soyayyar ta, yarinya ce 'yar asali data san Allah wanda ke baki sani ba dan a yanda mu mukai rayuwa ke taki mummuna ce akan tamu dan haka duk wani kyawu, Ilmi, Kudi, Asali da kike magana a wajena ke fanko ce dake da dabba baku da mara ba keba dabba ba Arniya ma baku da maraba ke da ita saboda banbancin Musulmi da Kafiri shine yarda da Allah da bautan Allah, shin Nadia ki fada mani zaki iya tuna ranar da kika kai goshin ki kasa da niyyar salla? Yaushe rabon ki da azumi? Baki ma manta da kalmat musulunci ba kuwa? Lallai idan na aure ki ban kyautawa yaran da nake fatan samu ba kuma suma wata rana zasu iya tuhuma ta dalilin da yasa na sama masu ke a matsayin uwar su, nayi rayuwa mara kyawu a baya amma Alhamdulillahi da shigowar Ayisha rayuwata yanzu abubuwa da yawa sun canja daga rayuwa ta kuma ina jin dadin haka dan haka there is no going back In Sha Allah, a karshe Nadia ina baki shawara daki hakura da aure na dan bana jin zai zame maki alkhairi, yana kawo nan yaja Amal sukai gaba suka bar Nadia wacce hawayen ma ya kafe sai tsananin azabar zugin da zuciyar ta keyi.
Kafura, Dabba sune suka fi mata yawo a kwakwalwar ta, kwatanta halin da Nadia ta shiga bai yiyuwa saidai mai karatu ya hasasowa kanshi irin mummunan halin da take ciki kawai, da kyar ta iya daga kafar ta zuwa mota kuma Drivern gidan ta yafito ta mika mashi key kawai ba tare data ce wani abu ba, cikin hanzari ya bude mata motan ta shiga ya rufe yajata, saida suka dauki hanya ta iya furta mashi 'drive me home'. Ok Ma'am inji drivern.
Da kuka Nadia ta shiga gidan su kuka mai tada hankalin iyaye musamman iyayen irin na Nadia, akaci sa'a Maama ta fito da niyyan zuwa gidan su King zasu kara tattaunawa akan batun auran ai sai cin karo tayi da Nadia ta shigo tana wani kuka na fitar hankali har wani sheshsheka takeyi tana jan kukan, aisai Maama tayi wurgi da handbag ta isa ga Nadia a sukwane cikin mugun sassarfa ta kama girgizata tana fadin ke Nadia lafia meya faru? Wane irin kuka ne kikeyi haka? Ko mutuwa akayi ne ban sani ba? Cikin kukan Nadia tace nida mutuwa akayi Maama da yafi man sauki akan halin da King ya saka ni a yau, wai ni ce Kafira nice Dabba inji King? Mama tayi kankan da ido tace kamar yaya kece kafura da dabba? Nadia ta danyi wa Maama bayani cikin kukan da abinda ya faru gidan su King, Mama ta dunkula ashar tace uwar shi ma tayi kadan bara tana shi karan kada miya bari inje gidan nasu in samu uwar tashi, sai fuuu ta mike tayi waje.

Mrs sS ❤️✨

 

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now