Auren Sirri 18

150 16 3
                                    

🔐Auren sirri🔐 1️⃣8️⃣

Allah Allah Maryam takeyi gari ya waye domin ta fadawa Ahmad cewa ta amince da shawarar auren sirri, dan ko bacci kasa yi tayi sosai hankalinta ya tashi sosai ta kuma tsorata, tasan Inna Indo, Inna Fulera da Inna Fatsima da yaran su basu nufin su da alkhairi sai sharri ta kuma tabbata duk yanda zasuyi sai sunyi dan suga auren ya tabbata dan haka kawai ta amince da shawarar auren sirrin nan, inyaso idan anyi aure saita fadawa Malam da Inna Rahane da kannen ta.
Washe gari tun da uwar safiya ta bar gidan zuwa school, kusan da ita aka bude makaranta saida ta jira zuwan Ahmad ta zayyana mashi ta amince da batun auren nan yanzu ya za'ayi? Ahmad ya saki ajiyar zucia yace bari in kira Usman inji ya kusa karasowa? Bayan Usman ya daga wayar cikin zolaya yake cewa wato ba ma za'a barni ko hutawa inyi ba ko? Ahmad ya saki tsaki gami da cewa da lokacin wasa da lokacin daba na wasa ba kai dole sai kayi wasa to wane hutu muna cikin neman taimakon ka? Yanzu dai kana ina? Usman yace ina hotel din dana sauka amma tunda ka matsa bari in maza in dan watsa ruwa sai inzo school din. Kafin Usman yazo lokacin exam yayi dan haka Maryam ta shige hall.
Bayan zuwan Usman ne Ahmad yake kara masa bayanin abinda ke faru wanda Maryam din ta fada mashi abinda ya faru jiya bayan ta koma gida, basu jima ba sosai Maryam ta fito kasancewar Hausa Language ne, bayan sun gaisa da Usman din take cewa ya suka yanke shawara yau ne ko gobe? Ahmad yace tunda har yanzu safiya ce mun yanke shawarar muje yau kawai, Maryam ta kada kai tace to.
Kusan awa biyu ya kawo su hunkuyi, suka tura Maryam cikin gida wajen matan tsoho Usman, wanda daman Usman sunan shi yaci. Ahmad da Usman suka mashi bayanin abinda ke tafe dasu amma sun fada mashi akan cewa Maryam bata da iyaye sun rasu tana hannun uwar rikon ta kanwar babanta ita kuma bata so Maryam din tayi aure shiyasa take korar duk wanda yazo neman auran Maryam din, da wannan tsohon ya kada kai yace ni na rasa abinda ke damun iyayen zamanin nan, idan yara sunce ga wanda suke so meyasa ba za'a bari su auri juna ba? Ita kuma uwar rikon yarinyar ai zataje ta iske Allah ita ta sani. Ya saki tsaki yace bari in aika a kira mani Liman sai yayi waliccin yarinyar. Cikin mintina kalilan an daura auren Ahmad da Maryam, a lokacin ne Maryam taji wani zawo zawo na neman kucce mata, sai kuma nadama ta fara shigarta tana tambayar kanta ta kuwa yiwa iyayen ta adalci? Sunyi tsaye akan ba zasu bari ta auri Adamu ba amma sai kawai tayi aure ba tare da sanin su ba, sai kawai ta hau kuka.
Har suka dawo kaduna Maryam kuka takeyi, ko Ahmad ya rasa yanda zai mata tayi shiru, da kyar ta tsagaita da kukan sukayi sallama da Usman yana mata fatan alkhairi gami da bata kudi masu yawa, yace yanzu zai dau hanyar Abuja saboda shima ya baro wajen nashi PPA din bai kuma sanar bazai zo ba. Maryam ta kada kai a hankali tana cewa ka barshi Usman nagode abinda kayi ma ya isa, Usman ya saki daria yace to indai kina so in barshi ki saki ranki ki dena bacin rai hakanan, wanda kikayi ma ya isa kinji er kanwata, saida Usman ya tabbata Maryam ta saki ranta kafin suka barta ta shiga gida su kuma suka ja motar zuwa masaukin Usman da niyyar ya hada kayan shi amma Ahmad ya hana yace ya bari sai gobe da asuba sai ya tafi, da kyar Usman din ya yarda, ya kuma bashi kudin da ya baiwa Maryam amma bata ansa ba yace ya aje mata.
Da dare Ahmad da Usman suna fira anan Usman din yake rokon Ahmad akan kada yayiwa Maryam butulci yarinyar tana da hankali da alama tasan me takeyi, Ahmad ya ansa da In Sha Allahu zanyi iya kokari na inga na kula da Maryam na kuma tsaya mata a koda yaushe, Usman ya bugi kafadar Ahmad yana cewa abokina fa yanzu ango ne ko? Suka kwashe da daria Ahmad yana cewa sunan ango ne dai tunda amarya tana gidan su.
Can kuwa wajen Maryam ta tarar da hankalin Inna Rahane da en kannen ta a tashe saboda har lokacin dawowarta yayi ya wuce bata dawo ba, ta dan saki murmushi tana cewa ku kwantar da hankalin ku tunda na dawo mun tsaya munyi karatu ne ban lura lokaci yayi haka sosai ba, da wannan ta kawar da damuwar su.
Washe gari basu da exam shiyasa bata fita ba kuma ita dama ba waya gare ta ba bare suyi magana da Ahmad amma duk abinda takeyi yana ranta.
Saida aka kwana biyu sana Maryam ta shirya zuwa school yin exam wacce daga ita sai guda daya kacal ta rage mata shikenan sun gama, tunda sassafe yau ma ta wuce zuwa school, abin mamaki acan ta iske Ahmad, suka saki murmushi a tare suka nemi waje suka zauna Ahmad yana tambayar ta ya take? Yayi kewar ta kamar yaje gidan su amma baya so yaja mata matsala tunda yasan abinda ake ciki akan Adamu, Maryam dai sai er dariyar jin dadi take saki ganin gata ga Ahmad kuma a matsayin ma'aura, har lokacin exam dinsu yayi ta shiga.
Bayan sun fito ne Ahmad ya nemi da tazo suje gidan da yake zaune, Maryam tace kada inje in jima fa kaga ranar na tarar dasu Inna hankali tashe, Ahmad cikin wayau ya janye Maryam zuwan gidan da yake zaune inda anan amarci ya fara, rana ce daba zasu taba mancewa  ba a rayuwar su, basu ankara ba har la'asar tayi, Maryam tayi wanka cikin tashin hankali take cewa nasan yau kuwa sai Allah Ne Zai kwace ni hannun Inna, banma san abinda zan fada masu ba, nan Ahmad ya bada shawarar suje tare ya kaita saiya ciwo magunguna a zuwan tadanyi ciwo ne ya kaita Clinic, da wannan shawarar suka iso gidan su Maryam wacce kuma ke ji kamar karsu rabu da Ahmad, ga mamakin ta su Inna babu tashin hankali kamar ranar farko saidai tambayar ta da Innar tayi ya akai ta tsaya har yamma tun safe idan ma karatun ne ta sake tsayawa aida saita dawo gida da wuri, sai kawai Maryam din ta fake da cewa bata lura lokaci yayi har haka ba, saita shige toilet ta zubar da maganin sai wanda aka bata na ciwon jikin da takeji kadai ta bari, wanda Ahmad ne yaja mata ko ince suka yi tare.
Washe gari saiga Maryam tana fadawa Inna tana so taje gidan su kawar ta sai suyi karatu acan, Innar tayi shiru tana mamakin Maryam da zuwa gidan su kawa ita iya sanin ta da Maryam bata da kawa ko daya sai Hibba da Muhd sai kuwa ita kanta Innar, ganin kamar Inna na doubting sai Maryam din tayi saurin cewa Inna bafa dole sai naje ba kawai dai ita Aisha kawar karatu na ce kuma tana da yaya dake zuwa school yana koya mana amma basai ma naje ba, sai Innar ta kada kai tace to ai da mamaki nake naji kina cewa kawa nida nasan baki da kawa, yanzu kikai bayani toba matsala kije idan Malam ya shigo zan sanar dashi inda kika tafi, har Maryam tazo fita sai Innar tace Maryam ki kula da kanki kinji? Cikin sanyin jiki Maryam din ta kada kai kafin ta fice, saima ji take kamar ta koma gida a haka dai ta iske Ahmad a gidan shi.
Tun ba'a je ko ina ba Ahmad yasa Maryam ta mance da damuwar data fito da ita daga gida, soyayya sosai sukeyi suna kulawa da junan su, interval din kwana biyar ke gare su kuma a kwanakin kullum sai sun hadu gidan Ahmad anan suke zaman su suna amarcin su.
Ranar da su Maryam suka zana last paper ai har kuka saida Ahmad yayi wai yanzu bazai rika ganin ta ba kullum? Maryam din ma kamar zatayi kuka tace zata rika yin dabara ta fito, da wannan Ahmad yaja Maryam zuwa restaurant inda sukai celebrating gama exams dinta lafia sukai pictures. Kafin su koma gida ya wuce da ita ya siya mata waya ya bata, cikin zare ido Maryam tace inyi me da ita? Tambayoyin da zansha saboda wayar nan ai Allah Ka dai ya sansu dan haka ka bar wayar Ahmad, Ahmad din ya bata rai yace gaskia Maryam ba zanji dadin ace bana ganin ki kuma bana jin muryar ki ba dan haka ki karba, Maryam ta kuma kada kai tace kawai ka saka man cikin jakar nan da kake tara mani kudin da kake bani, saita bata rai ta kuma cewa nayi nayi da kai ka dena bani kudi tunda ko sisi bana ansa kar a gane a gida kuma ma bani da abinda zanyi dasu, Ahmad yayi murmushi yace kullum dai bazan gaji da fada maki nema na ya koma dan ke ba, tun sadda aka daura mana aure hakkokin ki suka dawo kai na dan haka idan har ban baki sutura da abinci da abinsha ba to lallai zanta tara maki kudin su na tabbata wata rana zasu amfane ki dan ina jin hakan a rai na.
Maryam ta shafo sumar Ahmad tana cewa Ahmad bazan gaji da fada maka ina son ka ba ina kaunar ka har bansan adadi ba, idon ta ya ciko da kwalla tace nidai fatana ka rike amanata kada wani dalili yasa ka juya man baya, Ahmad yasa hannu yana share mata hawaye yace har abada bazan taba juya maki baya ba Maryam, ni naki ne amanar ki, mutuwa kadai zata raba mu In Sha Allahu. Da wanna Ahmad ya kai Maryam gida sukai sallama, waya kuma yasa ta ta ansa amma ansa a silent, yace mata duk sadda zasuyi magana saita je toilet tunda daki daya suke sharing ita da Inna Rahane da en kannen ta.
Wata daya bayan nan, Maryam da Ahmad sun hadu kamar so hudu a wata dayan nan, Ahmad ya gama service din shi amma ya kasa komawa Abuja, saiya sanar wa iyayen shi akwai abinda yake jira. Yayin da a gidan su Maryam aka kuma dago maganar auren ta da Adamu tunda ta gama jarabawa, wanda wannan ya kuma hargitsa gidan gaba daya, ana wannan rikicin ita kuma Maryam ta balle zuwa clinic siyan magani marar ta na ciwo, Doctor din dake wajen ya tambaye ta ya take ji ta sanar mashi gami da karawa da cewa tana tunanin period din ta ne zai zo dama hakan yake mata tana ciwo sosai amma wancan watan ma baizo mata ba kuma batayi ciwo kwata kwata ba, sai kawai yace bari ya mata wani gwaji ya gani.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now