Auren Sirri 20

150 17 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣0️⃣

Maryam tayi kuka tayi kuka kamar ta cire ranta, ta kuma san karshen zaman ta da iyayen ta yazo musamman da Inna Rahane saida ta koma wajen Maryam din tayi mata mugun gargadi cewar ta nemi wasu iyayen badai su ba, Malam yayi kokarin yabaiwa Inna Rahane hakuri amma ganin shi kanshi tana jefa mashi wani irin mugun kallo yasa ya mata shiru a ranshi yace idan aka kwana biyu yasan zata huce dan yasan yanzu hankalin ta ne ya bata in banda haka ai shima yana jin abinda taje ji wata kila ma fiye da yanda take ji, a hakanan Maryam ta lallaba ta kai kanta gidan Ahmad saboda tasan ita da gidan su kuma sai wani ikon Allah, da wani ido zata kalle su? Wani bayani zata musu su yarda tana da aure? Zasu yafe mata auren da tayi ba tare da sanin su ba? Yaya su Inna Fulera, Inna Fatsima da Inna Indo da dikkan yaran su zata kalle su kosu su kalle ta? Wane irin habaici da daria zasu mata ita da iyayen ta? Ta kuwa yiwa iyayen ta adalci ma? Tambayoyi kala daban daban a zuciyar Maryam ga kuma mugun gargadin da Inna Rahane ta mata, a haka ta shawarci zuciyar ta da taje gidan Ahmad ta dauki ajiyar kudaden da yake tara mata, lallai yau ranar amfanin su tazo, a gida ta same shi kwance da alamun tunani yake yi, kamar daga sama Ahmad yaji sallamar Maryam saiya mike a uzirce yayi saurin kamo ta ganin tana neman faduwa, banda sannu babu abinda Ahmad yake jera mata.
Maryam baki da lafia? Meke damun ki? Da kyar Maryam ta iya masa fake smile tace bana jin dadi amma naje asibiti, Ahmad ya matsa mata akan su koma asibitin amma ta kafe akan taje dan haka ba zata koma ba, ganin taki hakan yasa ya kyale ta sai kuma ya hau bata hakuri yana mata rantsuwar babu komai tsakanin shi da Hady amma ita Hadyn tana son shi kuma er uwar shi ce domin baban ta kanin Mum din su ne, kuma ta jima tana son shi saboda shi ne ma ta koma Abuja gidan su da zama, yanzu ma sunga ya gama service din shi ne amma bai koma gida ba ita kuma ta damu, sai kuma akai sa'a da birthday din kawarta Salma yazo dan haka ta samu hanyar zuwa Kaduna amma babban dalilin ta saboda ta zo waje na ne, lokacin da kika shigo na tashi kenan da niyyar korar ta sai ta rungume ni tana roko na akan mu tafi gida ayi mana aure ne, ke kuma baki tsaya na maki bayani ba kika gudu, naje gidan ku amma na kasa aikawa a kira ki saboda sanin halin da muke ciki, nayi ta kiran ki a waya baki daga ba sai ma kashe wayar da ki kai, ya karasa bayanin sa da rantsuwa da Allah akan duk abinda ya fada mata iya kar abinda ya sani kenan kuma babu karya a ciki.
Maryam ta saki ajiyar zucia kafin ta furta kayi hakuri Ahmad na yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike ba, iya kar abinda ido na ya nuna ma shi na rike amma na yarda da kai dan haka babu damuwa, kayi hakuri kuma da abinda nayi son da nake maka ne yaja wo hakan, Ahmad ya sakar mata murmushi gami da rungume ta yace babu komai Maryam. Nan dai komai ya wuce kamar wani abu bai faru ba, amma ganin jikin ta babu sauki yasa ya matsa mata akan suje asibiti, ita kuma ta kafe akan babu komai zata warke dan ta riga da taje asibitin, babu yanda zaiyi hakan yasa mata ido amma ganin dare ya fara saiya fara shakku anya Maryam lafia kuwa? Without a second thought Ahmad ya tambayi Maryam meke faruwa da bata da niyyar tafia gida gashi dare yayi? Maryam tayi kokarin kauda damuwar ta tace duk dai akan Adamu ne, amma nasan komai zai wuce dan haka zan dan kwana biyu anan kafin in koma gida wata kila zuwa lokacin abin ya lafa, Ahmad yace to Allah Ya kawo saukin lamarin.
Kwana biyu bayan nan, Ahmad ya fita da yamma ya siyo musu abinci kasancewar har yanzu Maryam bata jin dadin jikin ta sosai kuma taki fadawa Ahmad batun cikin dake jikin ta, ita kanta ba zata ce ga dalili ba, hakanan kawai take ganin kamar tayi shiru ta kyale shi har zuwa wani dan lokaci. Hady da Salma sukai sallama suka shigo falon, da mamakin su suka tarar da Maryam kwance bisa three sitter, Maryam ta dan mike gami da tattaro duka murmushin fuskar ta, ta musu sannu da zuwa gami da cewa su zauna mana, Hady ta buga tsaki tace aiko baki bamu guri ba zama zamuyi tunda gidan dan uwa na ne kuma miji na da zan aura, Maryam ta runtse ido saboda zafin kalmar Hady wai mijin ta ne da zata aura.
Maryam ta mike ta nufi kitchen ta samo musu ruwa da drinks ta kawo musu gami da cewa ga ruwa nan kafin Ahmad ya dawo tunda ba nisa yayi ba, Salma ta saki murmushi gami da cewa mun gode dan kuwa kinyi kokari tunda da alamu baki da lafia amma kin iya tashi danki karrama mu, sannu Allah Ya inganta, Maryam dai bata fahimci ina Salma ta dosa ba dan haka sai ta masa murmushi kawai, haka nan ma sai taji zaman falon ya ishe ta dan haka ta mike ta shige bedroom. Wannan damar Salma ta samu take sanarwa Hady ke wannan yarinyar ciki gare ta da alamu ma laulayi take yi, Hady ta sakarwa Salma harara gami da cewa da uban wa ya mata cikin da har kika gane ciki gare ta? Salma ta dan yatsina fuska tace a matsayi na na nurse kina ganin bazan iya fahimtar mace mai ciki ba? Kuma har kina da bakin tambaya waya mata cikin bayan da kinsan ansar? Ko kuwa saina fada maki Ahmad, Hady ta dade kunnuwa tana fadin ya isa Salma ya isa, sai kuka ya kwace mata tanayi tana fadin Allah Ya isa tana kuma alwashin saita raba Maryam da Ahmad ko ta halin yaya ne.
Da kyar Salma tasa ta tayi shiru tana fadin bari Maryam din ta jiyo ki dai, suna haka Ahmad ya shigo rike da ledo ji ganin su saiya daure fuska ya wuce kai tsaye bedroom, Salma ta danyi murmushi gami da cewa Ahmad babu ko gaisuwa anya kuwa? Ya dan tsaya gami da cewa kune ganin ku ba alheri ba shiyasa naga babu amfanin tsayawar, idan kun gama zaman make sure u close the door on ur way out, baiji ta cewar su ba ya shige wajen Maryam.
Da kyar Salma ta iya janye Hady suka bar gidan, akan hanyar su ta komawa gidan su Salman ne suka shirya makircin da zaisa su raba Maryam da Ahmad saboda sanin halin Ahmad na bala'in kishi da Hady tayi yasa suka amince akan cewa zasui using kishin shi akan Maryam su raba su, kai tsaye Salma tayi wa mai wankin gidan su magana akan abinda take so ya mata kuma bata so wani daga gidan su ya sani, sana ta kawo kudi mai yawa ta bashi tace gashi nan yaje ya jira kiran wayar ta. Hannu na kyar ma ya damke kudin ya hau godia, suka wuce suka barshi nan yana ta zuba godia. A cikin gida Salma ta bawa Hady shawarar cewa kafin su kulla abinda suka shirya dole sai sun nemi shiri da Maryam inba haka ba lallai babu ta yanda hakan su zai cimma ruwa.
Shiri bana wasa ba suka nemi su fara da Maryam kasancewar sun girme mata nesa ba kusa, ita kuma yarinta yasa bata fahimci komai ba sana zucia daya ta anshe su daman tana kewar iyayen ta da kannen ta dan haka data samu su Salma saita anshe su da hannu biyu saidai abu daya shine duk yanda suka so bugun cikin ta dan susan sirrin su Maryam taki cewa komai akan hakan, amma sun fahimci cewar Ahmad baisan da cikin dake jikin Maryam ba wannan ya kara masu himmar shirya makircin su.
Cikin sati daya suka fahimci kusan koda yaushe Ahmad yana gida sai idan ya fita siyo musu abinci saboda ya hana Maryam tayi girki duk da ta danji sauki, sai kuma idan lokacin salla ne sana ya fita masallaci, amma daga ba haka ba to babu inda Ahmad yake zuwa sai wajen wani friend dinshi guda daya kuma yana yin kwana biyu har uku baije ba, amma idan yaje yakan dauki 2hours bai dawo ba.
Ranar da abin zai faru ranar Laraba ne, Ahmad ya fadawa Maryam zaije wajen Musty ya duba shi dan baya jin dadi, Maryam ta marairaice fuska tace kodai mu tafi tare ne? Ahmad ya dan yamutsa fuska sana yace kinsan Musty da shegen surutun tsiya nan zaisa ki gaba yana kallo yana maki labari ni kuma nasan ba wani jurewa zan ba dan haka kiyi zaman ki yau ba zan jima ba tunda dubo jikin shi kawai zanyi kuma zan wuce school in anso maki result din ki tunda ya fito, da wannan sukai sallama.
Maryam ta fito falo bayan fitar Ahmad kenan saiga su Salma, kamar kullum ta tare su da fara'ar ta, Hady ke tambayarta ina Ahmad ne? Maryam tace yaje dubo friend din sa baya da lafia, Hady ta saki murmushin jin dadi kasancewar yau da alama hakan su zai cimma ruwa, saboda yau zuwan su na hudu kenan suna zuwa da maganin bacci amma basui nasarar samun Ahmad ya fita ba sai yau, kasancewar yanzu suna zuwa har kitchen da kansu yasa Hady ta mike ta nufi kitchen a cewar ta zata kawo ruwa su sha ne, a kitchen ta bude maganin baccin da suka taho dashi ta saka a cikin cup daya sana ta jero ruwa da cups din da drink ta fito falo, anan ta aje akan center table tana zuwa drinks din ta mikawa Salma daya ta mikawa Maryam daya itama ta dauki dayan tana sha.
Ba'ai minti biyar ba da Maryam tasha drink din ya fara ganin dusu dusu kafin tai wani abu wani bacci ya dauke ta saita sheme anan kamar wacce ta suma babu ko motsin kirki. Salma da Hady sukai murmushi suka mike suka dauki Maryam suka kaita bisa gado suka cire mata kayan jikin ta suka musanya da towel, sana suka dawo falo suka kira Rabe mai wankin su Salma, suka kwatanta masa gidan, babu bata lokaci cikin minti talatin ya iso, Salma da Hady suka fada masa abinda suke so yayi masu wato acting a matsayin kwarton Maryam.
Rabe ya danji tsoro, amma jin Hady tace zan baka kudin da zaisa ka dena wanki da guga ka kama sana'a sai kawai zuciyar ta bushe yaji zai iya aikatawa kawai, nan suka bar shi a falo suka fita waje suka samu waje suka boye da nufin da sunga Ahmad ya cinno hancin motar sa zasu kira Raben saiya shiga wajen Maryam ya kwanta bisa gado yana fadin abinda suka fada mashi ya fada idan yaji shigowar Ahmad din, haka kuwa akayi basu jima da boyewa ba Ahmad ya dawo sukai hanzarin kiran Rabe suka fada mashi, Raben yayi saurin cire kayan shi ya zubar dasu anan falo sai daga shi sai gajeran wando ya nufi kuryar daki yayi saurin kwanciya bayan Maryam data fara motsi kadan alamun zata iya tashi ko wani lokaci, Rabe gaban sa saida ya fadi ganin Maryam din, surar ta ta kidima shi daga ita sai towel da suka canja mata, kafin ya gama tunani yaji shigowar Ahmad.
Ahmad daya shigo falon da farin ciki saiya fara cin karo da rigat namiji da wando, ya dan yamutsa fuska kafin ya nufi bedroom anan fa yaji Rabe na fadin 'Maryam ki tashi mana kada lokaci ya kure yau bamuyi komai ba duk da kin wanke mani rai na tunda kika fada mani kina dauke da ciki na, ai babu abinda zan maki in biyaki sai addu'a tsakanin mu, Ahmad ya wani banko kofa cikin azabar fushi, fuskar shi har wani rawa rawa takeyi saboda fushi adaidai lokacin Rabe ya kai hannu yana shafa kan Maryam dake bude yana murmushi mai nuna jin dadi, yayin da Maryam ta bude ido cikin razana saboda yanda Ahmad ya banko kofa, sai Maryam ta rasa abinyi dan komai ma saiya shafe mata a kwakwalwa ga Ahmad tsaye idanun sa sun canja launi sunyi ja, ga wani katon da bata sani ba yayi tsuru tsuru alamun an kama shi yana kwartan ci.
Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now