Auren Sirri 10

212 12 2
                                    

🔐Auren Sirri🔐1️⃣0️⃣

A hankali Ayisha take bude ido tana ganin dusu dusu, Mamy da Adnan suka hada baki wajen furta Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Adnan ne ya riko hannun ta yana smiling yana mata sannu, Mamy dai tagumi ta zuba ta gaza furta komi tun bayan godia ga Allah da tayi, kamar rada Ayisha ta furtawa Adnan yaje falo zatai magana da Mamy, yace to Sister gami da mikewa ya fice ya rufo musu kofar.
Shiru shiru babu wanda yai magana sai can Ayisha ta fara da 'Mamy nasan ni mai laifi ce babba agare ki kuma kullum ina cikin fargabar randa zaki sani ba tare da ni na furta maki ba shiyasa ban taba samun cikakkan kwanciyar hankali ba dan haka Dan Girman Zatin Ubangijin Daya halicce ki Ya halicce ni Ya halicci dukkan komai kiyi afuwa gare ni ki gafarta mani kuma ki tausaya mani, sai kuka daga ita har Mamyn amma tuni zuciyar Mamy ta karaya ta kuma yafe mata tun kafin Ayisha ta furta laifin da take tuhumar kanta da yiwa Mamyn, Mamy ta matso kusa da Ayisha ta durkusa daidai yanda zata ji dadin hugging din Ayishar data dan mike daga kwanciyar, kyakykyawar runguma sukaiwa juna gami da sakin ajiyar zucia, wannan kadai ya tabbatarwa Ayisha da Mamyn ta yafe mata dan haka cikin samun karfin gwiwa Ayisha ta warwarewa Mamy duk abinda ke gudana tsakanin ta da King na soyayyar su da abinda ya fada mata na dalilin sake komawar sa neman degree a karo na biyu da auren da ake shirin mashi da Nadia, ta karishe da fadin Mamy ina son king amma ina so yanda zaki umurce ni in aikata wani abu in kuma aikata cikin maki biyayya shima haka nake fatan yaiwa iyayen shi biyayya don sun fi ni son shi, dan haka na hakura da king ina rokon Allah Ya fitar mani da shi a rai na.
Mamy taci gaba da shafa kan Ayisha kamar wata karamar yarinya koda yake haka take kallon Ayishar tun haihuwar ta ita kullum tuni ta takeyi tana 'yar baby mai kiriniya dinnan, yayin da a zuciyar ta tunanin baya take yi irin tata rayuwar da abinda soyayya taja mata amma duk da haka har yau batai nadamar soyayyar data yi ba sai nadamar abinda ta aikata dan haka ita tausayi ma yaran suka bata sosai, muryarta da alamun tausayi sosai kuma har akan fuskar ta abinda mutum zai iya karanta kenan ta fara lallashin Ayishar da ta sawa zuciyar ta hakuri akan duk abinda ya same ta shi dan adam aduk inda yake madamar musulmi ne daya yarda da La'ilaha Illallah! To a kullum jarabawowi bibiyar shi suke kuma idan ma shi wannan mutumin bai cin karo da jarabawowi ta yaci gaba da furta Istigfari! Yana mai neman Gafarar Allah, wannan shine abu na farko da zan fada maki Ayisha. Abu na biyu kuma shine ki yaiwa godia ga Allah a duk halin da kika samu kanki basai halin jin dadi kadai ba a'a koda a halin rashin dadi ne toki yawaita godewa Allah da yawan yin salati ga Fiyayyan halitta da yawan Anbaton Allah ta hanyar yawaita karatun Qur'ani da zikirin Ubangiji wanda dama nasan kina yi tunda duk abinda na sani na koya daga Iyaye na da Islamiyar da muka rika zuwa saida na koyar daku keda Adnan dan haka nasan kina da naki sanin musummam yawan bincike da kikeyi game da litattafan Addini dan haka abu daya anan dazance maki ki kara dashi shine yawaita azumin Monday and Thursday saboda falalar azumin da kuma ansar addu'ar me azumi da akeyi. Abu na uku na karshe kuma shine nasan yanda kike ji a zuciyar ki koma fiye da yanda kike ji, anan Ayisha ta dago tana kallon Mamy cikin mamakin furucin ta wai tasan abinda takeji koma fiye to ta ina? Lura da hakan da Mamy tayi ne sai ta mata smiling tace eh Ayisha da gaske nake kuma wata rana zaki gasgata batu na, taci gaba da cewa ban baki shawarar ki hakura da king ba a yanzu sai idan shine ya yarda ya barki amma na yarda na amince ki bar king yayiwa Iyayan sa biyayya ta kowacce hanya muddin bata sabon Ubangiji bace kuma inda rabo sai kiga kema ya aure ki saiya hada ku biyu ya rike a matsayin matan shi, Ayisha ta wani bata rai tana gunani, Mamy tayi gajeran daria taci gaba da cewa kishiya ba abun gudu bace duk da akwai wasu da ake gudu saboda halayen su, dan haka Ayisha kibi al'amuran a hankali kuma ki karfafawa King gwiwa yayi wa iyayan sa biyayya shine kadai sakayyar da zaki masa.
Abu na karshe Ayisha koda wasa ban amince ki kara wata tarayya ko wacce iri ce ba tare da kin gaya mani hakikanin gaskia ba, next time idan kin aikata bazan maki uzuri ba bare yafiya ina fatan kin fahimta? Ayishan tayi nodding head dinta alamun eh. Many tace good, bari in turo Adnan ya kawo maki abinci kuma lallai ki tabbata kinci. Bata jima da fita ba Adnan ya shigo da tray na abinci ya haye gadon yana mata murmushi ya debo abinci shi a dole shine zai bata tunda bata da lafia, tana daria ya maida shi (kani) yayin da shi ya koma ita (yaya) to a haka dai taci abincin kuma da dukkan alamu taji dadin abincin dan taci da yawa may be kuma saboda sassaucin data samu ne daga Mamy.
**  **
A dakin King da shi da Amal ne sun kure suna neman mafita can King kanar an tsikare shi  yace lil sis na tuna kwanaki kin fada mani kina da mafita indai zan amince da batun ki, yanzu na shirya jin koma menene dan haka fada man inji dan wallahi ni saidai su aurawa wani Nadia badai ni ba, Amal ta danyi daria kafin ta fara da cewa ' kamar yanda na fara fada maka zaka samu damar auran zabin zuciyar ka domin cika soyayyar ka amma da sharadi kuma sharadin shine dole ne zakayi hakuri ka auri Nadia.. tun kafin ta karasa King yaja tsaki mai tsayi kana cikin harara yace ita kuma Ayishan fa taya zan aure ta idan na auri Nadia da banda wajen aje ta koda a wajen zucia ta ne bare har ta samu shiga ciki? Amal tace zaka hada su biyu ka aura ne, cikin hanzari king yace ta yaya? Amal ma tace ta yanda zakayi bori a gidan nan da cewa babu wanda ya isa ya aura maka Nadia kuma in dai so suke ka aure ta to lallai saidai a hada auran da Ayisha suje su nemo maka auran Ayisha in kuwa ba haka ba to zaka gudu ne su neme ka su rasaka, nasan idan kayi haka lallai Mummy zata shiga taitayin ta zata nemi mafita kuma dama itace keda matsala ba Daddy ba dan yanzu haka inka bibiya baisan me ake yi ba. Shiru ya biyo baya da alamun King ya amince da wannan shawarar amma sai ya kalli Amal yace zan amince da wannan shawarar kadai ne idan Ayisha ta amince. Amal tace babu laifi amma a yanda na fahimci Ayisha Iyayan ta sun bata tarbiya nagartatta data fi tamu dan a gaskia nima nasan an sangarta mu ta yanda duk abinda muke so shi muke aikatawa yayin na lura wajen Ayisha ba haka bane ka duba ka gani ko tarayya zata fara da mutum saita dauke shi ta kai wajen Mamyn ta idan Mamyn ta amince shikenan idan bata amince ba shikenan ba za'ai tarayyar ba dan haka koda wasa kada ka fada mata cewa ga boren da zakai a gida dan sai hakan ya fara canja tunanin ta a kanka, kawai ka fada mata cewa kana so ka hada su biyu ka aura ita zabin ranka yayin da Nadia take zabin Iyayan ka. Bravo lil sis bravo, cikin jin dadi King ya furta hakan ga Amal sai sukai daria su duka cikin amincewa da shawarar su da wannan Amal ga wuce cikin gida ta tarar da su Amatullahi da Amira da Uwar Gayya Nadia ana ta shirya yanda biki zai kasance nan itama ta zauna cikin su kamar babu komai a ranta kuma bata nuna bata son auran Nadiya da King ba a ranta tace 'nima bari inbi yarima insha kidana ba tare da fadawa sun kore ni ba'.
Amal akwai wani abu waishi wayo da dabara haka Allah Ya halicce ta gata dai itace karamar su amma kusan dukan su da ita suke shawara idan wani abu yana damun su shiyasa ita din ta kasance favorite din kowa a gidan su, ba Daddy da Mummyn ba baga Amatullahi da Amira dake yayyin ta ba bare uban gayya wanda a wajen ta ita shine favorite din ta wato King.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now