JAWAAD

           Tun sanda yasha maganin sai ya dinga samun nutsuwa a hankali harya  farajin ɗan ƙarfi bayan tafiyarsu bilkisu, sai kuma yaƙi da zuciya, sosai maganin na masa aiki, amma yasan wataran zai daina tamkar yanda na bayama sukai yayi suka shuɗe, ko abokinsa Doctor Sooraj ɗin da ya bashi shawarar amfani da wannan maganin ya tabbatar masa na wani ɗan lokacine kawai, babbar mafita shine yay aure, inba hakaba ƙwayoyin da yakesha domin kare kansa daga faɗawa halakar da yake gudu to lallai zasu iya masa illa ma wataran, tunda har ALLAH ya bashi lafiya da muhalli, dukiyar aure mi yakema zaman jira? Idan matarsa yakeso ya dawo da ita mana yabar cutar kansa. A lokacin da Dr Sooraj kema Jay wannan maganar ƙin ce masa uffan yay, daga ƙarshema sai yay masa sallama ya baro office ɗin.

            Da daddare bayan tafiyar su Ummah gida ya samu kira daga Uncle Nasir, duk da bayajin ƙwarin jikinsa haka ya tashi ya fita bayan ya saka dogon wando a jikinsa, dan harma ya riga yay shirin barci shi. Kansa tsaye falon Uncle Nasir ya nufa, bayan yay sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, Uncle Nasir na zaune shida matarsa suna hira da kallon labarai, ya gaishesu da girmamawa. Duk fuskokinsu ɗauke da fara'a suka amsa masa, Uncle Nasir yace ya taso susha Fruit salad ɗin da yake sha, Jawaad ya amsa da, “Alhmdllh Uncle na ƙoshi”.
      “Aiko saika shashi” cewar Hajiya Sumayya matar Uncle Nasir, ta cigaba da faɗin, “kai yanzu Jawaad kenan ka girmi cin abincin kowa a gidan nan?, tunda kai aure shikenan, da ai ba haka kakeyiba, mu yanzu ka yayemu daga iyayenka kenan?, inaga ko shayin wajenan rabon daka shashi tun daren ɗaurin aurenka da Shahudah, to ni dai yanzu kamar yanda na saba a baya kullum zan zubo abinci na aiko dashi sashenka, idan kaso kaita jerenshi kamar ɗakin amarya”.
    Murmushi yayi tare da kai hannu ya shafi kansa, yace, “Nayi laifi Ammi, amma ayi haƙuri, kinsan yanayin aikinmune yasa, wani lokacin bana shigowa da wuri, kuma ina fita da wuri,  amma daga yanzun indai na dawo da wuri zanyi magana a kawo mani”. “To yanzu naji magana, bara na zuba maka fruit salad ɗin”.
     Uncle Nasir dake saurarensu yace, “
Ke nama lura sake ɗaure masa ƙugun zama babu aure kikeyi, yanzu ba zancen adinga kai masa abinci nai zamanyi ba, zancen wadda zata dinga dafa masa kamar kowane magidanci zanyi”. Tace, “Ah Alhaji indai nan ne aini ina bayanka, ga ƙannensa nan su Abdur-rahman za'ai musu haihuwa ta bibbiyu, shiko ya zauna ruwan ido kamar wanda bai ɗanɗana auren yajiba”.
         “Barsa, ai na shirya maganinsa wannan karon, idan har bai shiryaba ni a shirye nake na zaɓi ɗaya daga yaran gidanan na aura masa”. Da sauri Jay ya kalli kawun nasa harda waro idanu. “Kalleni da ƙyau fa, ALLAH inhar baka yunƙuro a cikin shekararnan ba, a yaran gidanan zan aura maka, karkuma ka ɗauka maganar wasa nake maka, gobema insha ALLAH zanje na sami Alhaji babah muyi magana (Kakansa mahaifin Mamansa), idan kuma matarka kakeso ka dawo da ita”. Shiru Jawaad yayi baice komaiba har Uncle Nasir ya gama masa faɗa sannan ya bashi haƙuri akan insha ALLAH zaiyi abinda sukeso, amma su ƙara masa lokaci.
        Uncle Nasir yace, “Ba damuwa, ALLAH ya kawo mafita, amma ranar lahadi idan ALLAH ya kaimu akwai meeting da za'ai ƙarfe huɗu, sai kai ƙoƙari ka halarta, karka bari ayi kuka da kai kamar ko yaushe dan ALLAH”.
        “Insha ALLAHU Uncle zan kiyaye”.
       Ya daɗe a sashen suna hira dan sai kusan ƙarfe ɗaya ya koma sashensa, kasancewar yasha barcin rana sai bai iya yin na darenba da wuri, lap-top ya buɗe ya shiga wasu ayyukan, sai wajen biyu da rabi ya rufe ya tashi, alwala yayo yay nafilfili tare da jero doguwar addu'a akan mahaifinsa da mahaifiyarsa, dama sauran al'umma baki ɗaya.
     
     Sakamakon rashin kwanciya da wuri ya sashi makara sallar asuba, ya tashi a gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da salla yay wanka ya gyara gadonsa sanan yay shirin fita, Gimba ya tafi gida weekend, dan haka shi da kansa yaja motarsa sai ƙaton gidan gonarsa da ya gada wajen mahaifinsa dake can asalin ƙauyen kakansa Alhaji Yusif, inda sukai rayuwa da kakarsa mama maryam, garin kuma da mahaifinsa yay rayuwar ƙuruciya harma data girma. Sosai an samu cigaba da abubuwa masu dama a cikin ƙauyen wanda duk sanadin mahaifinsane, an musu titi, an kuma kai musu wuta, ga dam ɗinsu da har yanzu suke noman rani, dan garin yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan da ake amfanuwa da nomansu da kiwo a jihar tasu dama maƙwaftanta baki ɗaya. Alkairin mahaifinsa da shi kansa wanda yakeyi yasa a kullum yake mai daraja a wajensu, idan yaje ji suke tamkar su haɗiyeshi, saika rantse wani sarakine.
      Kamar yanda ya saba gidan mai gari ya sauka, dan haka ya keyi a duk lokacin da yaje ƙauyen, hakan na ƙara masa daraja da kwarjini, kamar yanda shima yakejin daɗin abinda suke masa ɗin, dan maigari yana masa abu tamkar uba, kasancewarsa abokine ga mahaifinsa Abdul-aziz tunna ƙuruciya. Ya samu tarba kuwa ta mutuntawa, inda akaita haba-haba dashi da abincin gargajiya masu tsafta kamar yaune aka fara ganinsa matsayin baƙo. Sam Jawaad bashi da girman kan zaɓar cima ko raina cimar ƙauye, hasalima suna masa saɗi fiye dana zamani, idan har yaje ƙauyen nan komi suka bashi cin abinsa yake, saboda yanada yaƙini akan tsaftar iyalan baba maigari, tun yana ƙanƙanin yaro mahaifinsa ke zuwa dashi, hakama mama maryam na kawosa kafin ta rasu, hankalinsa kwance yaci ya ƙoshi, dan dama da yunwarsa yazo, bayan sun gaisa da baba maigari da jama'ar dake fada suka nufi gidan gona shi da Abbati ɗan baba maigarin da zasuyi sa'anni da Jawaad, dan abokinsane na amana, dukkan sirrin gidan gonarsa yana hannun Abbati, shike kula da komai, Abbati dukda yayi karatu har matakin degree na biyu yana zaune ne anan ƙauyen tare da iyayensa, iyakarsa yaje birni wajen aiki ya dawo garinsu ya kwanta, matarsa ɗaya da ƴaƴa huɗu, yayi ɗan gininsa na zamani saboda ƙauyen yanzu yanada dukkan cigaban da ake hangensa a birnin, kuma mafi yawansu sunada aƙidar son zaman gida sai dai waɗanda aiki ya tilastama komawa birnin akan dole, dan a dalilin Abdul-aziz mahaifin Jawaad ƙauyen yanada manyan ƴan boko matasa masu jini a jika dake taka rawar gani sosai a sassan ƙasar.
     Suna tafe suna hirarsu cikin nishaɗi, inda Abbati keta kiran sauran abokansu dake gida ta waya yana sanar musu Jawaad yazo. Jawaad ya fige wayar yana hararar Abbati, “Malam ya isheka haka, sai gayyatomin ƴan iskannan kake salon kuzo ku addabeni da surutu mara ma'ana”. Abbati ya kwashe da dariya, “Oh ashe kana tsoron surutun namu? Ai indai kaga munbar maka surutu kuwa sai kayi abinda mukeso, ka dubemu daga mai yara uku sai masu huɗu amma kai ka zauna ruwan ido Jay, ai kosu Jabeer da kuke tare a birni  sunada iyalansu, wai kodai da kurwanka Shahudah ta tafine bani labari kafin su Isa su zo”.
     Kafin Jay yay magana sukaji ance, “Ai gamu mun iso”. Daƙƙuwa Jay ya watsama abokan nasa huɗu da suka iso wajen yanzu-yanzu, waɗanda suma duk sunyi karatu kowa da abin yinsa, kuma suna bada gudunmawa a gidan gonarsa suma. “Duk kunci ƙaniyarku zomayen banza, uwarwa ya gayyatoku nan?”.
      Dariya suka sanya baki ɗaya, Labaran ya dunƙule hannu ya bigi damtsen hannun Jawaad yana faɗin, “Bar wani mazurai gaye, munfika ƙarfi fa inma hayaƙin kakeji, dan mu kullum matanmu ƙara mana sukeyi” duka shima Jawaad ya kai masa, Labaran yay saurin duƙewa. “Ɗan iska da ka tsaya naima fuskarka damage sai naga ƙarfin da Asiyan ke baka, mara mutunci”. Dariya suka sanya su dukansu, Aminu yace, “Mudai mun gaji da ganinka haka ALLAH kuwa”. “Gaskiyane Aminu, ya kamata ka duba Jay” cewar isa. “Hakane kam lokaci baya jira fa, kullum girma muke ƙarawa ƙuruciyarmu na guduwa” cewar Salisu dake dafe da kafaɗar Jawaad. Murmushi kawai Jawaad yayi, yasan halin abokan nasa, tunkan yay auren farkoma haka sukaita addabarsa, sai da akai bikinsa da shahudane suka sama masa lafiya, yanzunma ko waya yake dasu faɗansu kenan, shi kansa ba auren bane bayaso, gidan jiya yake tsoron komawa........ Adam ya katse masa tunani da cewar, “Idan kuma a birnin babu wadda tai maka ka duba a garin nan mana, auren nan shine cikar martabar mutum”. Abbati yace, “Maganarku nakan hanya ƴan uwa, ko ɓato maka rai akai daga waje kana shigowa gida kaga iyalanka sai kaji ka huce, musamman idan kayi dace da macen datasan yanda zata tattali dukkanin farin cikinka, koda gajiyarka ka kwaso kanada inda za'a nuna tausayinka a sauke maka ita da kulawa”. Jawaad ya shafa kansa yana sauke numfashi da girgiza kai, “Kudai baku da magana saita aure dai jarababbu, ko hutawa bakwayi, karku damu zanyi, kumin addu'a kudai. a tare suka shiga masa addu'ar kuwa kafin su fara bashi hannu suna gaisuwa.
       Jawaad nason abokansa na ƙauyensu, dan suna bashi nishaɗi da faɗa masa gaskiya komai ɗacinta, shiyyasa ko kansa ɗaukar zafi yay a wajen aiki tuni yake ƙoƙarin ware weekend ɗin da zai shigo, dan yasan zai samu nutsuwa sosai..............✍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang