2

15K 1.1K 184
                                    


Alhmdllh inama kowa fatan alkairi, nakumaji daɗin wannan tarba, naso ace zan iya jurewa na biku ɗai-ɗai na amsama kowa Comments ɗinsa, sai dai nace kuyi haƙuri, kamar yanda matsalan ido ta dakatar dani da typing dolene yanzuma na ringa lallaɓawa saboda kunada ɗunbin yawa, akwai group insha ALLAHU da aka buɗe a shafin manhajar Telegram, masu amfani da wannan shafi su maza su garzaya idan suna buƙata, domin canne zai zama dandalin tattaunawa akan littfin ƙwai cikin ƙaya da sada zuminci, duk mai karatu yana buƙatar dandali na tattaunawa akan littafi, dan da yawanmu hakan na bamu nishaɗi da sake fahimtar da mu abinda bamu fahimtaba, kuma yana ƙarama writer ƙarfin gwiwar typing koda batai niyyar hakanba, ku maza kar a baku labari. Zakuna samuna koda yaushe a can domin ku tabbatar ina tare daku, masoyan bily kuma na isar da saƙonku gareta akan ta daina tsoron jay😂, masoyan Shahudah tana miƙo muku gaisuwa itama🤓.

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Wannan shine link ɗin group namu mai suna MASARAUTAR BILYN ABDULL A manhajar Telegram😘😘.

2

..............Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al'amari dake yawan faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai bani.
        Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.

★★★★★

     Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa fahimtar komaiba.
      Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta'aziyyah tare da jero addu'ar neman gafara ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.
          Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo musu abincin da zasu ci.
    Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.

★..::..★

        Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare, tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata, kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki naci abinci.

        Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha'i da muka fito domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.
     Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan na gaishesu jikin mota na koma na jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.
         Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen, zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL'AMARIN namu.
      Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan, hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi kuwa.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now