19

11K 1.2K 480
                                    

Page 19

................Idanunsa sunyi masifar kaɗawa sunyi jajur, batare da yace dani komaiba yaymin nuni da ƙofa alamar in fita, kasa koda motsi nayi, sai hawaye dake cigaba da ambaliya a kumatuna tamkar an buɗe fanfo.
          Cikin matuƙar kaushin murya da tsawa na tsinkayi furucinsa cikin kunnuwana, “Miemaa! niɗin sa'anki ne ko?!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai jikina na rawa saboda harga ALLAH na matuƙar tsorata da yanayinsa. Ya sake faɗin, “Tashi kifita a office ɗinan kafin naimiki duk abinda yazomin kai, Yanzunan har idonki yakai tsaurin kallona ki faɗamin abinda ya dace dani?!, ki fitar min anan kona sauya miki kamanni!!”. Kuka na sake fashewa dashi ina saurin jan jikina nai baya gudun karya makeni, dan harga ALLAH tausayin Dad na tsaga dukkan jijiyoyin jikina harda aunty Shahudah, na tabbatar samun boss ga aunty Shahudah shine farin cikin gidanmu, Hawayen dake ziraromin na share tare da faɗin “Kayi haƙuri dan ALLAH, bazan sakeba”. Cikin faɗan dana rasa abinda ya fusatashi irin haka yace..... “Baki jiniba ko?!” yay maganar a hasale yana tasowa kaina, Baya na shiga jan gwiwoyina batare dana tashiba, matsanancin fushin dana gani akan fuskarsa ya bani tsoro matuƙa, bantaɓa tunanin yanada zafin zuciya irin hakaba, ya nunani da ɗanyatsa yana faɗin, “Badai kece kika buƙata da kanki ba, to duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki ba daniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza”. Ya ƙare maganar yana ranƙwafowa kaina ya fisge rigarsa dake hannuna ya fice daga office ɗin”.
          Ɗif naji komai na ya ɗauke wuta yabar aiki, sam narasa awane mizani zan ɗora ruɗaɗɗun kalamansa marasa tushe balle makama, man kaina gaba ɗaya ya tsiyaye, babu wata jijiya dake ɗaukar saƙon ƙwaƙwalwa zuwa zuciya dake aiki a jikina har tsahon wasu mintuna da naji saukar abu mai ɗumi a jikina. Zumbur na miƙe domin samun dawowar hankalina daya gushe na wucin gadi. Ban sami damar gama tattaro abinda ya shuɗeba idona ya sauka akan Oga Jabeer dake bakin ƙofa a tsaye yana kallona. murmushi yaymin kafin ya ƙarasa shigowa office ɗin, “Tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki kinji” Ya faɗa yanamin nuni da hannu. Ban musa masaba na miƙe, dan koba komai ina buƙatar duba halin da nake a ciki.
             Bani da isashen lokacin fashin baƙi akan ruɗaɗɗun kalamansa, dan kaina tsaye ina dangantasune kawai da rufewar ido ga mamallakin furtasu, to danmima zuciyata kesan rikitani da hasashen abinda bazai taɓa zama hakaba, na ƙurama kaina ido a madubin dake cikin toilet ɗin ina mai tariyo kalaman dallah-dallah yanda zasu bani fassarar da nake buƙata, “{Duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki badaniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza}”. ‘Kenan yana nufin inhar aunty Shahudah ta sake koma masa da halinta na baya akwai hannuna wajen cutar dashi? Kuma nizai kuhunta ba itaba? To miyasa? Miyasa zan zama laifi akan ƙoƙarin ganin na inganta auren sunna, na haɗa zukata biyu masu ƙaunar junansu, na tabbata shima yana sonta kawai halayyarta yake ƙyamata, to miyasa ni laifin zai tattara a kaina kuma?’ “Saboda kalamanki ne suka tursasashi yarda ta koma” wata zuciya ta ayyanamin daga can ƙasan rai, ‘To miyasa zai amince da abinda bai zama wajibiba? Ni shawara na bashi da nuna masa ƙwaɗayin samun lada ai ba tilasba, sannan na ceto zuciyar Dad daga ɓacin ran tashin hankalin gudan jininsa, kenan hakan yana nufin kuskure nayi?, ni wacece da har zai amshi roƙona ya wajabtama kansa?, nasake tambayar kaina hawaye na silalomin. Nima kaina sai yanzu naga ƙarfin halina da wautata akan taryarsa, banyi tsammanin zan iya hakanba koda a cikin mafarkine kuwa, zan cigaba da roƙon ALLAH ya hana faruwar matsalar da yake hangowar, insha ALLAHU lafiya zasu zauna abinsu. Haƙura nai da tunanin na kimtsa jikina da tissue ɗin dana gani a toilet ɗin dan inada tabbacin zai riƙeni har zuwa a tashi insha ALLAHU, na sake ɗauraye fuskata na fito. Zaune na iske oga Jabeer, yana ganina yay ƙaramar dariya da faɗin, “Anya maman nan tamu ba raguwa baceba?” murmushin da ban niyyaba ya suɓucemin, na girgiza masa kai ina faɗin “a'a sir”. Dariyar ya sakeyi da cewar, “To ALLAH yasa, yanzu daga nan sai ina kuma?”. Nace, “Zan koma Office ne, akwai aikin da boss ma ya sani tun ranar waccan monday ɗin ban kammalaba”. Ya miƙe yana faɗin, “To masha ALLAH, nima bara na koma office, amma daga yau idan kikaga Jay a irin wannan matsanancin fushin ki daina masa naci akan koma wane irin maganace, dan idan yay fushi irin haka akwai matsala, ALLAH ne ya taimakeki ya zaɓi ya fita yabar miki office ɗin, amma dabai fitanba ke kuma kika cigaba da taurinkan kin fita komai zai iya biyo baya, ki kiyaye kinji, boss ya wuce duk yanda kike zatonsa, mutumne murɗaɗɗe mai wahalar sha'ani matuƙa, idan yaso kaji dadinsa baka taɓa fahimtar tsaurinsa, idan baiso hakanba wahala zakasha ta gaske”.
       Nace,  “Insha Allah zan kiyaye nagode sosai”.
      “Hakan shine dai-dai, ALLAH ya kiyaye gaba”.
     Tare muka fita, shi ya nufi office nikuma na sauka ƙasa, harna fara tafiya sai naji ina buƙatar ganin yah Qaseem, dan tunda mukazo yau ban gansaba kuma bai nemeniba, ko a waya.
       Nayi knocking kusan sau uku babu amsa, hakan yasani tura ƙofar office ɗin a hankali na shiga, zaune na sameshi a kujerarsa, ya kwantar da bayansa jikinta idanunsa a lumshe, na sake maimaita sallamar tawa idona kafe a kansa. A hankali ya buɗe idonu yana kallona, sai kuma ya tsashi zaune sosai yana murmushi damin alamar nazo da hannu. Takawa nai a hankali zuwa garesa, na zauna a ɗaya daga kujerar gaban tebirinsa idona har yanzu a kansa. Wani murmushin ya sakemin, kafin ya buɗe baki a hankali cikin sanyin murya yace, “Har yanzu jikin dai bilkisu?”. “A'a Yah Qaseem naji sauƙi, mike damunka? Tunda muka baro gida baka da walwala, gashi har yanzu ina ganinta a saman fuskarka kuma, mike faruwane?”.
       “Humm” ya faɗa yana cije baki, kafin yace, “Babu komai, kawai dai banajin ƙarfin jikinane”. Numfashi na sauke a hankali fuskata na nuna tausayinsa, nace, “To ko zamu tafi gida kaga likita”. Nanma kansa ya girgiza mani, cikin kauda maganar yace, “Kinci abinci ko?”. Kaina kawai na iya ɗaga masa, dan jinai dukna damu da halin da yake a ciki, shiru mukai na wasu mintuna kafin na miƙe nace, “bara na wuce dama leƙoka nayi dan naji shiru”.
      Baice komaiba saida na doshi hanyar fita daga office ɗin, “Ki ƙoƙarin gama abinda kikeyi, da anyi la'asar zamu wuce dan yanzu Mom ta kirani jikin Shahudah ya sake rikicewa”. Sosai naji gabana ya faɗi, na kaɗa masa kai kawai ina haɗiye ƙwallar data cika mani ido, “ALLAH ya bata lafiya” “Amin”. ya amsa mini akan laɓɓa.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now