63

14.8K 1.3K 458
                                    

Page 63

....................Su Jawaad basu san wainar da ake toyawaba a gari, sai iface-iface suka dingaji da tashin hayaniya, sai kuma hayaƙi daketa turnuƙe sararin samaniya a hankali. Sai sukaga kuma mutane nata fita daga asibitin.
    Gaban Jay ya faɗi, ya zaro waya daga aljihu yay kiran Jabeer dan yaji ko lafiya?. “Boss wlhy akwai matsala, an fito da mutanen nan daga prison za'a kaisu kotu jama'ar gari sun tare motar sun banka mata fetur sun saka wuta. Wlhy duk yanda jami'an tsaro sukaso tsaidawa al'amarin ya gagara, harma an raunata mana ɗan sanda guda daketa ƙoƙarin basu kariya da roƙon mutane su kwantar da hankalinsu kotu za'a kaisu, kuma a yau za'a yanke musu hukunci. Amma sam basu sauraresaba, saima suka nema haɗawa dashi shima, dan acewarua shima nasune”. Innalillahi Jawaad keta ambata zufa na keto masa a duka sassan jikinsa. Dole yabar asibitin ya nufi inda al'amarin ke faruwa..

        Wuta taci su Alhaji kokino sosai kafin ƴan kwana-kwana suzo da masu bada taimakon gaggawa na jami'an tsaro, da ƙyar aka iya samun hanyama motar ta ƙarasa, police kuma suka fara jefa barkonon tsohuwa, da wannan damar aka samu mutane suka fara darewa har aka ƙarasa gasu Dad aka basu taimakon, sai dai kuma ina komai ya gama ƙurewa, dan wutar ta cisu sosai, sunta ihu da neman taimako basu samuba. Waɗanda basu mutunba ma da wahala ace zasu rayu, dan su Dad ko iya gane fuskokinsuma ba'ayi sam. A haka dai aka kwasosu zuwa General hospital inda su Bilkisu suke.
           Faruwar hakan yasa aka baza jami'an tsaron sintiri a kowane titi, tare da kafa dokar hana shiga da fita gaba ɗaya, kasuwanni da kowacce ma'aikata an rufesu ruf an kora mutane gidajensu. Garin yayi tsit, sai gidajen redio dana tv kawai ke aiki, anan mutane kejin halin da ake ciki.
         Kafin a ƙarasa dasu Dad asibiti wasunsu suka sake mutuwa, ciki harda Uncle Nasir kuwa. Suma dai an shiga da sune kawai, amma likitoci sunma rasa ta ina ya kamata su fara basu taimakon daya dace, gaba ɗaya jikinsu ya sale tas, yay jazur tamkar naman dake kusa da wuta ana masa gashi😭.
      Ba ƙaramin tashin hankali su Umm-Anum suka sake shigaba da ganin su Dad, duk da zalincin da sukaima rayuwarsu har hawaye sukai musu. Bama suba duk mai hankali yaga wannan bahagon al'amari dolene ya shiga ruɗani mai tsanani, ya kumaji tsoron wannan mummunar rayuwa da waɗanan mutane suka ƙirƙirar ma kawunansu. Gadai duniyar an tara, kuɗi, mulki, zuri'a, da komai amma an ƙare da tafiya a barsu cikin tozarci da wulaƙanci. Basu karesu daga faruwar kowanne irin bala'iba ko masifa ba, abinda suka tara da wanda suka shuka bai hanasu mutuwaba, bai hana ƙarshensu muniba, wannan shinefa ake kira da BA FARKON BA ƘARSHEN, yakai ɗan uwa bari murna akan aikata mummunan aiki kuma babu abinda ya sameka, bari tinƙaho da taƙama akan kai haƙƙin wani bai sakaka komai sai ƙiba da kwanciyar hankali, bari farin ciki kaine sama dakowa saboda kasancewarka azzalumi, bari taƙama da tinƙahon ka tara kai babu yanda aka iya da kai. Rage buri da hangen haramun domin kawai burge duniya ko morarta dayin bishasha a cikinta. Daure ka nema halak komai wahalarta da ƙaracinta, nisanta kanka daga haramun komai sauƙinta da zaƙinta. Ji tsoron UBANGIJI koda ace baka ganinsa to shifa yana kallonka. Kiyaye ruɗin duniya dana abokan banza ka kama ALLAH da abokan ƙwarai masu nuna maka muhimmancin tsoronsa. Ya ALLAH ka gafarta mana, kasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe. ya rabbi ka ɗauki rayukanmu muna masu cike da ɗunbin tsoronka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)🙏🏻😭.

__________________________________

           Al'amura sun sake ƙwaɓewa, a gaba ɗaya kwanakin satin da suka biyo baya, babu wani farin ciki daga jama'ama balle su Jawaad da iyalan waɗanan mutane. An samo gawar Aunty Mah-Mah (Rahmah) a gidan Dad cikin wani akwatin tsafinsu, ashe lokacin da suka halakata wata gawar daban suka kawo a zuwan itace, shiyyasa Dad ya hana kowa yimata wanka shine yay mata a lokacin. To ashema ba gawarta baceba, gawarta na nan cikin ɗakin sirrinsa da ko Mom ta rantse bai taɓa barinta ta shigaba, ita kuma duk tunaninta bai taɓa kaiwa ga hakanba.
     Abin sha'awa da tsarkake sunan UBANGIJI gawar Rahma fes aka sameta dukda sheɗancin da Dad ya ɗauki tsahon shekaru yanayi da ita. Fuskarta fayau tamkar a yaune ALLAH ya ɗauki ranta. Bilkisu ta rungume gawar tana kuka abin tausayi. Da ƙyar Jawaad ya ɗagata akan gawar shima yana nasa hawayen da baisan suna zirarowaba. Alhaji babba kam yayi dauriya matuƙa, sai dai haɗiyar zuciya kawai yakeyi da kukan zuci. Umm-Anum tai mata wanka aka suturtata. Ɗunbin al'umma daga ɓangarori da dama suka sake sallatar gawar Rahama a karo na biyu, ta kuma samu rakkiyar ɗunbin jama'a zuwa makwancinta na gaskiya.
       An samo zunzurutun kuɗaɗe da kayan tsafi kala-kala da wasu abubuwan a gidan Dad, hakama Uncle Nasir da sauran abokan sheɗancinsu irinsu Kokino. Kamfanoninsu ma an samo abubuwa masu yawan gaske masu matuƙar tada hankali, ciki harda kayan shaye-shaye kala-kala da tabar wuwu buhu-buhu da adadinsa ya tasarma dubu goma. Sai wasu gurɓatattun abubuwan da bama zasu lissafuba gamai sauraro.
     Ƙasa tayi tsitt, manyan dake huɗar kasuwanci dasu data abokantaka sun fito sunata ALLAH wadai da nisanta kansu da ɓoyayyun ayyukan su Dad ɗin, komai dai ya fito fili, anyi walƙiya ijiya taga kowa da komai. Inda aka bar iyalansu da waɗanda aka zalunta irinsu Jay da jiyyar zukata.
     Idan kaga Bilkisu a irin wannan lokacin dole ka tausaya mata, ga laulayin ciki ga tashin hankali da damuwa, sauƙintama ƴan uwanta da mijinta kowa tattalinta yake da burin ganin farin cikinta. Takanyi kukan jin daɗi da ganin ƴan uwanta zagaye da ita, waɗanda ada ta rasa samu.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now