8

11K 1.2K 280
                                    

Page 8

.............Jawaad dake kallonsu daga ciki yay murmushi kawai yana girgiza kai, dan ya fahimci wani abu daga Rose ɗin. hannu ya miƙa ya buɗe murfin ɗayan gefensa, Hafiz dake ta wajen tsaye yace, “Kinga mai sunan Momcy zo tanan”.
      Amsa masa nai da “to” na nufi can duk da a raina banso hakanba dai, sai dai haka kawai naji inason bama shegiyar rose ɗinnan haushi yanzun, dan na kula sam bata ƙaunata dai, su mutanen duniya dasun ganka shiru-shiru saisu dinga ɗaukarka sakarai ko bakasan abinda kakeba, indai nice kuwa tasa kanta a ramin damisa wlhy. Ina shiga Hafiz ya rufe murfin, gimba yay ma mota key, bansan yanda aka ƙare da rose ba mukabar gidan bayan oga Jabeer ya shiga gaba bisa umarnin Boss da yay masa magana.
   
           Har muka isa station oga Jabeer da gimba na hira, amma ni dashi kamar mun haɗiyi kwaɗo. Yanda na takurama babu abinda nake buƙata kamar mu iso na sauka nidai. koda gimba ya tsaida motar ban fitaba saida duk suka fita, baiko kalli kowaba a cikinmu yay gaba abinsa zuwa hanyar office ɗinsa, Jabeer ne kawai ya kalleni fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “To mai sunan mom sannu da ƙoƙari, ki ƙara ƙaimi da jarumta dan aiki da boss sai jarumi na gaske”.
       Duk da ban fahimci zancensaba nai murmushi ina ɗaga masa kai, sannan nace, “ngd” a ƙasan raina kuwa ina tunanin wai sunan wa? gareni suketa wani boyen suna.
    Murmushi yay shima, ya nunamin cikin motar yana faɗin, “Karki damu babu godiya a tsakaninmu, ki tattara masa tarkacensa kibisa office dasu, ai kinsan office ɗin ko?”.
          Tamkar na fasa ihu haka naji, amma sai na daure nace, “Ban taɓa shigaba dai, amma na sani”. Yace, “To Alhmdllh saiki kaimasa ni na wuce office ”. Kaina na jinjina masa batare da nace komaiba, shima yay murmushi kawai ya wuce abinsa.
    Duƙawa nai na tattaro wayoyinsa da tab da wasu takardu daya bari sai bindiga da keys da bansan kona miyeba, sai ƙamshi suke tamkar suma turaren ake fesa musu, ledar takeaway ɗinmu gimba ya bani, ban musaba na amsa, dan duk zatona duk shi zan kaimawa, sallama nai masa na nufi hanyar da zata kaini office ɗin da kaya riƙi-riƙi saikace wata ƴar gudun hijira, danma na barma gimba ledata akan idan na fito zan karɓa dukda yacemin gida zaije. Sai da na hau lifter domin office ɗinsa na hawa na uku ne, sai saƙawa da kwancewa nake ina zancen zuci, na iso shataletalen da ya raba hanyoyi uku na offices ɗinsu, ɗaya nasan hanyar dazata sadaka da offices ɗin su B.G ne, wanda suke a hawa na ƙarshe, sai kuma ɗayar hanyar bansan offices ɗin suwayeba a wajen, sai ɗayar hanyar da naga ya fito ɗazun, nan na nufa kai tsaye, dogon corridor ne da ƙofofi jere kusan goma, hakan yasa na fara bi ina karanta rubutun saman gudun kuskure, sai da naje na bakwai sannan naga an rubuta Captain Jawaad A yusif, inada tabbacin nanne, dan tunda aka gayamin cikakken sunansa bantaɓa mantawaba koda a second ɗaya ne kuwa. Sai da na daidaita kaina da sake ƙarfafa zuciyata da ke neman faso ƙirjina ta fito sannan nai knocking har sau uku, amma banji an amsa maniba, nai jim kusan na minti ɗaya kafin na ƙara yin knocking ɗin kamar mai tsoron a jita, nanma shiru, nakai hannu zan sake aka amsa mani. Ajiyar zuciya na sauke a hankali kafin na tura ƙofar da sallama na shiga, office ne da ya amsa sunansa office, dan kuwa yayi ƙyau, babu wasu tarkace komai kuma tsaf, ga mayen turarensa ya kama office ɗin haɗi da freshener mai daɗin ƙamshi, sai suka bada ƙamshi na musamman, kallo ɗaya naima inda yake zaune a kujerarsa ta office na duƙar da kaina, shima kuma bai kalleniba, baikuma cemin komaiba, yanata rubuce-rubucensa hankali kwance tamkarma baisan wani ya shigoba. Jinai tsayuwar ta isheni, dan haka na gyara kaɗan ina yamutse fuska, batare dana ɗago na kallesa ba nace, “Sir gashi inji oga Jabeer”.
      Jay da tun ɗazu ya daina rubutun ya kwantar da bayansa jikin kujerar kawai yana kallonta da jinjina shegen miskilancinta ya lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci ɗaya, sai faman goga ƙasan biron hannunsa yake a jikin laɓɓansa, ko motsi baiyiba ballanta ya amsa mata. Tsabar miskilancin yarinyarne kawai ke bashi mamaki, ya ɗan taɓe baki tare da maida kallonsa ga Computer ɗin dake kan desk ɗinsa, bironsa ya ajiye yana lafe jikin kujerar ya fara sarrafa keyboard ɗin Computer ɗin.
          Ƙaran danna keyboard da najine ya sakani ɗago idanuna nai masa kallon second 2 na janye, karan farko a rayuwata dana sake jinjina wulaƙancin mutuminnan, ‘kenan bazai tanka mani ba komi yake nufi?’ na ambata a zuciyata ina maijin takaicinsa. Satar kallonsa na sake yi sai muka haɗa idanu, da sauri na janye nawa ina tura baki gaba batare dana san nayima hakanba.
     Sautin fitar ƙaramin tsakinsa ya sakani saurin sake kallonsa, yako dallamin harara alamun har yanzu idonsa a kaina suke, “Kin zama bodyguard ɗinane shin?” yay maganar a hankali kamar baison yi.
       Kaina na girgiza masa, duk da bani da tabbacin kallon nawa yake har yanzu, takawa nai zuwa gaban tebir ɗin na ajiye kayan harda ledar abincin, ban kallesaba bai kuma tankaminba na juya zan fita.
      “Zonan”
Na tsinkayi umarninsa. Juyowa nai kaina a ƙasa batare dana kallesa ba, “Zauna” ya sake faɗa a daƙile. ‘Kai nikam na shiga uku da wannan mutumin’ na ambata a zuciyata ina mai jina a matuƙar takure, zuciyata sai faman harbawa take da sauri-sauri. Shiru office ɗin ya sake ɗauka na kusan minti ɗaya, sai ƙarar keyboard da yake dannawa kawai kake ji. Knocking ƙofa akai ya bada izinin shigowa, matashin sauriyi ma'aikacinmune ɗauke da takardu a hannu, kallo ɗaya nai masa na ɗauke idona, duk da shi na lura sai kallon mamakin ganina a nan ɗin ya keyi, har takai boss ya daka masa tsawa.
      “Kallon mutane aka turoka yine!?”.
     Cikin sauri da ladab yace, “Sorry sir”.
      Banji ya tanka masaba, danni kaina a duƙe banma ɗagoba, sai sautin siririn tsakinsa naji kawai, shidai saurayin sai faman nanata kalmar haƙuri ya keyi kusan sau huɗu kafin ya fara masa bayani akan takardun hannunsa, banji ya tankaba, hakan yasani satar kallonsu, gani nai ya miƙa hannu ya amsa takardun yana dubawa, kafin ya ɗago ya kallesa da sake miƙa masa ta kardun yana faɗin, ”Ka kaisu office ɗin Lieut..; Richard, kace ya duba, zuwa anjima sai yazo dasu ina nemansa”. “Okey sir” ya faɗa cike da girmamawa kafin ya amsa ya fita ko sau ɗaya bai sake gigin kallon sashen da nakeba.
        Ɓoyayyen numfashi na sauke bayan ficewarsa, saima naji yaɗan bani tausayi........

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now