21

11K 1.1K 436
                                    

Page 21

...............Kallonsa nai ya zubamin harara, babu shiri na ɗauke idanuna na zauna kamar yanda ya buƙata a lallausar kujerar tasa dariya nazomin a cikin rai, danni mamakin yanda ya iya harara wa mutane nake, sai kace wani mace. Da ƙyar na iya riƙe dariyar daketa son fallasa na saka flash ɗin a jiki, duk abinda nake yana tsayene a kaina harna kunna video ɗin. Har ya kai karshe ya sake komawa baya baice komaiba, ganin mun maimaitashi sau uku yaƙi magana saina juyo dan inga koma dai nikaɗai nake kallon. Mamaki ya kamani ganinsa tsaye a bayana hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa, idanunsa akan Computer alamar duk yana kallona. “Idan kin gama kallon nawa saiki nuna inda baki ganeba”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kamar wani mai tsoron a jisa.
      Fuska na kumbura tare da ɗauke kaina, a raina nace, ‘Kai wama ya kaika iya kallon mutane’. hannuna na ɗaura saman mouse ɗin nai zumin dai-dai wajen mai faci ina faɗin, “Akan mai facin nan ne dama, kamar akwai alamar tambaya dangane da shi, dan......” kasa ƙarasa maganar nai saboda kusancin da muka samu, a dalilin ranƙwafowar da yay har munajin saukar numfashin junanmu, ya ɗaura hannun hanggunsa saman table ɗin, na damar kuwa saman nawa dake kan mouse. Da sauri na rumtse idanuna, tare dayin azamar janye hannuna dake ƙasan nasa, saboda wani mugun harbawa da zuciyata tai. Baice komaiba, shikam ko a jikinsa, saima ƙoƙarin maida video slowly da yay. Nayi matuƙar takura da tsorata da wannan kusancin namu da yay matuƙar yawa, har takai jikina ya fara rawa, idanuna suka ciko da ƙwalla, sam bana fahimtar bayanin da yakemin ma, dan sama-sama nake jin sautin muryarsa.
     Jawaad da duk abinda yake akan sani yayisa ya juyo yana kallonta, ta rumtse idanu zufa dukta tsatstsafo mata a goshi tamkar babu ac a office ɗin. “Hummm” ya faɗa acan ƙasan maƙoshi ya janye jikinsa. A mamakinsa sai yaji ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, hawaye sun silalo saman kumatunta, saurin ɗauke kansa yay tamkar bai ganiba.
         Har bigewa nake da shi wajen rawar jikin miƙewa daga kujerar jin ya matsa, na goge hawayen dake bin kumatuna batare da na bari ya ganiba, gefen tebirin na koma na tsaya kaina a ƙasa nace, “Sir, bara kawai naje can dashi saina ƙarasa tattara bayanan”. Jawaad da har yanzu yake binta da kallo yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana ƙoƙarin danne dariyar dake son kufce masa, murya a daƙile yace, “Barshi zan ƙarasa, ɗauka waɗanan files ɗin ki kaima Hafiz, zuwa anjima ki dawo zamu fita”. Bawani fahimtarsa nakeba, kai kawai na ɗaga masa na ɗiba files ɗin na fice cikin sassarfa. A raina banda takaici babu abinda nakeji, miyasa halin mazan wannan zamanin kusan duk ɗayane? Burinsu kawai su taɓa macen da ba muharramarsu ba a matsayin wayewa, ashe shima mutumin nan haka yake ban saniba?, “Aikam na daina sakar masa fuska wlhy” na faɗa a fili cike da takaici.

★★★★

       Ƙarfe biyu muka fita cin abinci ni da Ummie, sai da muka gama nai ƙoƙarin biya sai nagama kuɗin dake jikkar tawa bazasu isaba, kusan koda yaushe Ummie ke biya mana inhar bada Yah Qaseem mukazo ba, sai naga da kunya hakan tacigaba da faruwa ai, ATM ɗina na shiga lalube dan na basu su cire, amma sai shima ɗin dai ban gansaba, gabanane ya shiga faɗuwa, dan bama shi kaɗaiba duk cards ɗina basa ciki kenan tunda a tare nake ajiyesu waje guda, kuma inada tabbacin itace jikkar danasan na fita da ita daga gida last. “Wai mikiketa lalube hakane kamar wata makauniya?” Ummie dake shan ruwa ta faɗa bayan ta ajiye kofin. Guntun tsaki naja ina mai bata amsa da, “Ai namafi makauniya yau Ummie, wlhy banga duk Cards ɗinaba, kuma inada tabbacin anan ciki suke”. Tasowa tai tana tayani, sai dai kumafa da gaske babu ɗin, hankalina yayi matuƙar tashi, “Ummie na shiga uku, a ina na jefar nikam?”. “Bily bazan saniba, amma nasan baki da mantuwa, yaushene rabonki dasu?”. “Ummie A ranar lahadi fa da hannuna na sakasu cikin nan dazan fita”. Tace, “Ai da sauƙima, ki tuna ranar ina da ina kikaje tunda kin tabbatar a ciki suke?”. Zama nai idona cike da kwalla ina tunano dukkan abinda ya wakana a wannan yinin, da sauri na kalli Ummie, “Ummie idanma har yardawa nai to bazai wuce wajaje biyu ba wlhy”. Ummie tace, “Ina da ina ne?”. “Saloon da wani garden, amma bara na bincika a saloon ɗin dan inada Number ma'aikaciyarsu ɗaya”.
       Ummie ta biya kuɗin muka fito a wajen, sai da muka koma office sannan nai kiran Number danai saving da Ladies mirror, bugu biyu kuwa aka ɗaga, bayan mun gaisa nace, “Dan ALLAH kiyi haƙuri, na kiraki maybe ba'a lokacin daya daceba”. Daga can tai dariya da faɗin, “lah babu komai”. Nace, “Okey ngd, ranar danazo wajen nan naku ina tunanin na yarda wallet ɗina, sam hankalina bai kaiba sai yanzu, ina fatan anan na yardar ɗin?”. tai ɗan jimm na wasu sakanni kafin tace, “Eh tabbas anan kika yarda, amma bata wajenmu, tana masarauta wajen su aunty Amaturrahman, dama sunbar saƙo akan idan kinzo nema a baki card ɗinsu, yanzu yaya za'ai kenan?”. Wani sanyi naji ya ratsani, na sauke numfashi da cewa, “Babu damuwa, idan na tashi aiki zan biyo na amsa, nagode sosai”. ta amsa da “Babu damuwa, sai kinzo”. Bayan mun kashe wayarne na faɗama Ummie duk yanda mukai, daga ni har ita mamaki muketayi na cewar wallet ɗin na masarauta.
          Ban samu kiran boss ba kamar yanda yace zamu fita har lokacin tashi yayi, zuwa nai na sanarma yah Qaseem ya wuce gida ni zamuje nida Ummie wajen wanke kai, yanzunma da damuwa na iskesa, dan haka bai wani jamin zanceba yace mu haɗu a gida. Nidai al'amarin nasa sake ɗauremin kai yay yanzunma, har muka isa Ladies mirror banbar mamakin wannan canjin nasaba. Sosai Ummie ta rikice da haɗuwar wajen, harda ma kanta alƙawarin zuwa wannan weekend ɗin su mata aiki, bamusha wata wahalaba muka samu wadda na kira ɗin, ta bani card ɗin da suka bari. bamu daɗeba muka fito dan magriba ta gabato.
         Ummie ta ajiyeni a gida ta wuce, koda na shiga saina iske an sallamo auntu Shahudah, falon cike da dangin Momy, da sukazo dubata, nidai na gaishesu itama nai mata yaya jiki na wuce, saboda a rayuwata na tsani kallon wilaƙanci, sukuma naga alamar indai ba nasuba to kowa banzane. Wanka na farayi harda wankan tsarki saboda baƙona ya gudu,  na fito na gabatar da sallar magriba nai azkar, ina zaune a wajen har aka kira isha'i, har lokacin inajiyo hayaniyar ƴan gidansu Momy, dukda yunwar da nakeji saina zaɓi haƙura na kwanta a haka, ɗan kayan maƙulashen da yah Qaseem ke yawan siyamin nakan ajiye a ɗaki su nai zamanci, gefe guda kuma ina ƙoƙarin kiran Number jikin card ɗin da aka bani, saida ta kusa tsinkewa aka ɗaga, munyi gaisuwa da wadda ta ɗagaɗin a mutunce dukda bansan wacece ba, kafin na mata bayanin kaina. Nayi mamakin yanda tai saurin ganewa, kai tsaye tace na tura mata address ɗin inda nake kawai, zasuzo su kawomin har gida. Sosai na ƙara mamaki da jinjina ƙyaƙyƙyawar tarbiyyarsu gaskiya, sam basuda girman kai tamkar ba waɗanda suka fito daga babban gidaba. Godiya nai mata mukai sallama, ban zauna ɓata lokaciba na tura mata number dan inada buƙatar cards ɗina su dawo hannuna da gaggawa.
            Jin gidan yayi shiru yasa na miƙe, dan fitar motoci da naji ya bani tabbacin duk sun wuce, ƙaramin hijjab na saka saman wando da rigar kayan barcina kalar ruwan hoda na fito, wata irin muguwar yunwa nakeji wlhy, rabona da abinci tun wanda mukaci da Ummie da rana. Babu kowa a falon duk sun tafi, na wuce kicin hankalina kwance, plates kawai nagani zube wanda sukaci abinci, sai dai babu komai a kulolin duk an cinye, cike da haushi na fara ƙoƙarin ɗora noodles dan bazan iya haƙurin kwanciya banci komai ba, dan danan na kammala dafawa na fito, mamaki ya kamani jin ƙamshin turaren da banyi zatoba, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri, waige-waige na shigayi a falon, saiko idona ya sauka akan wanda zuciyar tawa ke rayamin,  tsaye yake dafe da ƙarfen benen dake falon waya a kan kunnensa, kamar koda yaushe ƙananun kayane a jikinsa, ido cikin ido muka kalli juna, nai azamar janye nawa ina damƙe plate ɗin indomie ɗina daketa tururi, inaji a jikina har yanzu kallona yake, hakan saiya haifarmin da tafiya a hankali kamar wata hawainiya harna shige lungun ɗakinmu ni da aunty Aamilah.
       Jawaad daya kasa ɗauke idanunsa a kanta har saida ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido da cije lip ɗinsa na ƙasa, sannan ya cigaba da wayarsa, bai wani jimaba sukai sallama ya maida wayar aljihu idanunsa akan lungun da bily ta shiga, cike da kasalar data saukar masa yanzun ya haye saman ya koma wajensu Dad da Alhaji baba da Uncle Nasir da sukazo tare suke tattaunawa.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now