13

10.8K 1K 119
                                    

Page 13

.................Shiru tai na wasu mintuna kafin tace, “Ban taɓa ganinsu da idanunaba a gado ɗaya da mace, amma tabbas Salman yakansha zuwa da ƴammata gidan idan kamar basa nan, ko kuma suna barcinsu na ƙaddara, dan akwai lokacin farkon dawowarsu da yataɓa zuwa da wata yarinyar ƙabila suka kwana a gidan, da safe ta fito zata tafi ALLAH ya haɗasu da Alhaji a bazata, koda ya tambayeta daga ina? Saita faɗa masa Salman ne ya kawota, wlhy a lokacin nazata Alhaji zaiyi kiran Salman yaymasa tatas a gaban yarinyar, ya kuma gargaɗesa sake kawo wata sai kawai naga ya sallami yarinyar ta tafi, shikuma ya shiga mota abinsa ya fita rai a ɓace, dan ko driver hanawa yay ya tuƙasa da kansa yaja mota ranar. Bilkisu bansan miyasa Alhaji keda sakaci wajen tsawatarma yaransa akan abinda ba daidaiba, ya gwammaci ya shanye ɓacin ran a ransa komin zafin da abun yay masa da kuma illarsa garesu da yazauna ya nuna musu kuskurensu, gaskiya ban taɓa ganin wanda yayma boko da rayuwar yahudu ƙazamin ruƙo irin Uncle ɗinkiba, sai dai ina tausaya masa, dan banyi tunanin waɗannan ƴaƴan nasa zasu masa addu'a ba a lokacin da ƙasa ta rufe idanunsa, sai dai dayake UBANGIJI gafurunne kuma rahimun ba'a shigar masa al'amari, ikonsane ya canjasu kosu ƙare rayuwarsu a haguggunce kamar yanda suka tashi. Qaseem kam dai bazance na taɓa ganin ya kawo mace gidan nanba, sai dai nakanji yana waya, dan kusan sau uku ko biyu inajin yana waya da ambatar sunan hotel, ba sunan hotel daya shigo ciki bane kawai yasa nai tunanin hakan, sunan mata dakan shigo a zancen nasa da salon yanda yake wayarne kawai dai ya ɗarsa mani haka. Sai kuma faɗa da naji wataran Hajiya na masa akan batun aure, take cewa ya zauna yanata shashanci a waje sai ya gama tsufa baiyi aureba, idan soyake wata ta haifa mata jika a waje sai ya bada himma. Kinga a zancenta yana nuna kenan yana yin abinda bai daceba ta kamashi ko aka kawo mata labari. Sai dai shima babu tabbas, tunda ba ido da ido nidai na gansaba. Abu na biyu kuma Qaseem baya shaye-shaye, baida wulaƙanci tamkar Hajiya, dan baya shiga huruminka sai idan kaine ka saka kanka a ciki ko wani dalili ya haɗaku, da wahala kiga yana hantarar masu aiki sai idan sun ƙuresa gaskiya, shiyyasa lokacin da kikazo gidan naga yanata biyema su Hajiya akan abinda suke miki nata mamaki, dan nasan ba halinsa bane, sai daga baya na fahimci soyayyace yake miki batare da shima ya saniba, shiyyasa baya iya yin shiru akan al'amarinki. Salman yana shaye-shaye, dan ɗakinsa ma zaki gansu zube baya shakka balle shayin kowa, sannan ɗan wulaƙancine dason yanƙwana mutum, sai dai shi kuma akwai ƙyauta, dan bashi da rowa, akwai kuma tausayi idan ƴan mutuncin na kansa bai cake ba, dan wani rashin mutuncin nasa abinda yake sha ne ke azashi bisa hanyar aikatawa. Haka rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa kuma”.
      “Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.

         Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na idar da sallar la'asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na taɓasu.
      Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle hantara.
        “Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace, “Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai.....” sai kuma nai shiru ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna. Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace,
      “Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani kominene kike da buƙata a matsayinki na wacce take sama dani kuma nake ƙanwarki, nikuma nai miki alƙawarin inhar baifi ƙarfin himmata ba zan yimiki shi”. Tai guntun murmushin da ke ƙarama ƙyaƙyƙyawar fuskarta ƙyau tana jinjina kai, Tace, “Bansan haka kike da kirkiba ai, amma duk da haka zan biyaki, domin aikin ya cancanci hakan”.
      “Humm” kawai nace mata.
Ta sake muskuta zamanta da cewar, “Waje ɗaya kuke aiki da Broth ko?”. Nasan Yah Qaseem suke cema haka, dan haka nace mata “Eh”. Tace, “Yauwa, a Station ɗinku, akwai wanda nakeson kimin aikin a kansa, sunansa Jawaad, bai zama lallai ki sanshiba, dan shi mutumne da baya shiga kowane tarkace, yanzu ɗinma sai munyi shawara da dogon nazarin da har zaki iya samun kusancin taimakon nawa a wajenshi, dan nasan bazai kulaki ba kai tsaye”. Ta ɗanso bani dariya a maganganunta, amma sai na danne banyiba, dan nima nasan gaskiya dukta faɗa akan halayyar Boss, to amma yanda take faɗan magana a habaice kuma tanason na mata aikine ya saka abin son bani dariya. Tace, “Abinda yasa na zaɓeki a aikin nan saboda, baki da surutu, sannan kin iya hausa sosai, zaki fimu sanin hanyoyin da zaki fahimtar dashi ya fahimta saboda shi mayen son yaren hausane”. Yanzunkam kasa daurewa nai sai da na murmusa, banda shirme irin nata dasu da suka ɗauki yaren wani wata tsiya, ai sai sakarai ke ƙin yarensa.
     “Tom aunty Shahudah, yanzu mikikeso nayi ni?”. Jim tayi alamar tunani akan abinda ke'a ranta, sai kuma zuwa can ta sauke numfashi, “Zan ringa baki saƙo kina kai masa kulum, wannan shine kawai aikinki, idan kuma ya tambayi wani abu game dani, sai kisan yanda zaki tsarashi da manya-manyan hausarnan naku. Amma dai Aamilah zata sake miki bayani yanda zaki fahimta, danni harma narasa yanda zaki sake ƙara fahimtata”.
       “Karki damu Aunty, ko a yanzunma na fahimceki, matsalar kawai shine yanda zan samu kusancin dashi, da har zan sako masa babbar magana data shafi rayuwarsa ne, dan kinga wannan babbar maganace data kasance sirrinsa da ya shafesa ba zancen aikiba, amma namiki alƙawarin zan gwada ta wasu hanyoyi, saiki dage da addu'a kuma”.  
      “Okey, zuwa anjima zamu fita ni da Aamilah, zamu sayo abinda zakije masa dashi ranar Monday”. Na jinjina mata kaina kawai, dan bansan miyasa take bani tausayiba yanzu, na kula tana sonshi sosai, to ai Boss ya cancanci a soshi, sannan ita kanta ina mamakin yanda ya iya sakaci da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar, ba namiji irinsaba hatta dani mace aunty Shahudah na birgeni, tana cikin mata ƙyawawa ajin farko da ba cikin baƙaƙeba kosu kansu fararen ta shiga cikinsu saisun yabata, sun dace sosai matsayin ma'aurata ita da Boss, ‘sai dai nikam ta yaya zan tunkaresa da maganar nan?’.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now