14

916 28 0
                                    

*
"Ba ita bace Aliya ce 'yar uwar ta, please dan Allah wanene kai? And meyasa kake b'oye mata kanka?"

Shiru Sahal yayi jikinsa yayi wani irin mugun sanyi shima sai yaji tamkar ta gano shi, amman yana fatan kar Allah yasa hakan kasan cewar bai fiye yi mata magana ta irin wannan yanayin ba. Amman yanzu da take yi masa wannan tambayar mai zai ce mata? Babu abinda zai iya ce mata domin bashi da amsar bare kuma kwarin gwiwar yin magana, hakan ne yasa ya dinga ce mata,

"Hello... Hello... Hello, Soulmate ko kinyi bacci najiki shiru? Hello..bana jinki ko bacci kikai? Good night love! may angel wishes watch over your sleep tonight."

Yayi maganar a zuwan baya jinta kwata-kwata sannan ya katse kiran, sakato Aliya tayi tana bin wayar da kallo, lallai wai daman haka ake soyayya?shin me yasa ita Yaya Sahal bayayi mata irin wad'annan kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya, haka Muhamman S yake yiwa Fa'iza kalaman kauna ita da bata son shima, me yasa suda suke son juna ita da Sahal amman koda wasa bai tab'a yi mata kwatankwacin furucin kauna ba, lallai akwai gyara a cikin lamarin soyayyarta da Sahal dan tafi kowa buk'atar jin kalaman kauna, wato abin sauyawa yayi ita take yiwa Yaya Sahal furucin kauna yayin da ita kuma Fa'iza Muhamman S yake mata ita kuma kullum budar bakinta bata sonshi musamman ma da yake b'oye mata kansa.

Ajiye wayar tayi taje ta d'auki pad ta nufi toilet, jikinta ta gyara sannan ta koma d'akin su ta janyo wayarta itama, tunani take ko ta turawa Yaya Sahal text tunda shi yaki ko kiranta bare suji muryar juna. Murmushi tayi tare da tunanin kila aiki ne yake yi masa yawa shi yasa baya kiranta da dare sai dai ita ta kira shi, kai koda safe koda ranar itace take nemansa amman shi sai dai idan zaizo gidan su sannan yake kiranta yaji suna gida, ta shiga gurin rubuta sako ta fara rubuta masa good night text,

_'I was waiting the night to see the moon it didn't appear, so I called the sky 2 ask where the moon is? It told me the moon is reading your sms, good night and sweet dreams my Habibi.'_

Sai da ta sake karantawa kafin ta tura masa tana murmushi kamar ita ya turowa, tashi tayi taje tasa phone d'in a charge ta koma ta kwanta gefe d'aya zuciyar ta kasa manta muryar Muhamman S da taji a waya. Shirun da taji Fa'iza bata dawo d'aki ba shine yasa ta mik'e itama ta nufi d'akin Umma dan ganin ko tana can, tana zuwa kuwa ta ganta kwance cikin su Hidayya tana shak'ar baccinta, itama ta rab'a gefenta ta kwanta, ranar dai duk a can suka kwana daman Umma tana d'akin Baba Suleiman hakan yasa bata san Aliya ma ta koma d'akin ta ba sai da asuba da ta shiga.

Da safe suna breakfast Aliya ta gaya mata cewar Muhamman S ya kira ita kuma ta d'aga so ita tana jinshi shine baya jinta dan haka har abinda ya fad'a saida Aliya ta sanarwa da Fa'iza sannan ta karkare da cewa.

"Ke yanzu Sissy daman haka Muhamman S yake kashe ki da dad'ad'an kalmomi? Gaskiya Sissy kinji dad'i wallahi ni Yaya Sahal bai tab'a ce min koda I love you ba, kullum nice nake gaya masa haka."

Numfashi Fa'iza taja tare da cewa,

"Kema Sissy kin matsawa bawan Allahn nan, tuntuni na gaya miki akan ki rabu dashi ki kama wani ga samari nan Allah ya baki kamar zasu kasheki amman kin wani nace masa ba dole ya dinga yi miki rashin mutunci ba, ni wallahi haushi kike bani ma."

Aliya ta d'auki Jakarta tare da sanya takalmi tana cewa,

"Sissy ke baki san love bane shi yasa kike ganin kamar ina shirme, amman bari kema ki fad'a tarkon soyayya wallahi sai na yi miki dariya."

Fa'iza tayi murmushi cikin ranta tana cewa, 'Aliya kenan ni tun kafin nasan meye so nake soyayya ballantana kuma yanzu da nake jin tafi ta da zafi duk da na rabu da ganin wanda nake so d'in.' Amman a fili itama jakar ta d'auka ta zura takalmi da hijjab tana cewa,

"Sannu wadda tasan so, nima ina yin nawa ai kawai kece baki sani ba."

Dariya Aliya tayi saboda bata yadda da maganar ba, sallama suka yiwa gwaggo Talatuwa sannan suka yiwa Umma suka fita daman Baba Suleiman ne zai rage musu hanya dan haka shi a cikin mota suka gaida shi ya basu transport money, tun a cikin motar yake taja musu kunne akan su kula da tarbiyar da suka basu karsu biyewa kawaye musamman maza, sosai sukaji yana taja musu kunne akan duk abinda suka san yana faruwa a cikin jami'a har suka rabu akan idanunsa suka shiga napep shi kuma ya wuce inda zashi. Fa'iza na son yi mata zancen Raheenah amman tana tsoran kar Aliyan taje ta tare ta da maganar hakan yasa ta had'iye son gaya matan da kyar domin abin yana damunta tana son fitar dashi daga zuciyarta. Tun akan titin tarauni kowacce ta hau Adaidaita sahun ta, Saboda Aliya zasu tsaya a kano poly suyi assignment tukun, Akan hanyar Fa'iza ta zuwa Old site ne taji mota ta tsaya a gefenta, kamar karta kalla sai kuma taga tabbas gurinta aka zo hakan yasa ta tsaya.

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now