3

1.3K 45 0
                                    

*............_KAI MIN HALACCI!_*
      💕

_*NA_*

_*©️NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO)_*

®️_*HASKE WRITERS ASSO💡_*

       *_SHAFI NA UKU_*

Ganin yadda Shamsu ya zuba mata na mujiya yasa Aliya k'arasawa wajan da yake zaune, yana ganin tahowar ta yayi saurin kawar da kai yana kallon wani wajan daban. Dariya yaji tana yi masa a wajan kansa amman bai tanka mata ba itama juyawa tayi ta shige gidan Talatuwa, cikin d'aga murya take yi musu sallama har sai da ya jiyo shi da yake zaune kofar gida, bawai yau bane ganin sa na farko akanta ba, amman yau shine farkon ganinsa da ita har yaji zuciyarsa ta motsa wanda bai san dalilin hakan ba kodan yasan gidan da tazo ne?, ga wani mugun kwarjini da yaji tayi masa a yau dan ta 'kara girma akan lokacin da ya santa, ya sosa tsakiyar rantal din kansa tare da d'aga kafad'a alamar rashin damuwa yaci gaba da sana'arsa.

Cikin gidan kuwa tana shiga Talatuwa ta dafe kirji tana zaro ido, a duniya taki jinin Aliya tazo mata gida saboda shegen yawonta, wani lokacin idan tabar gidan sai kayi tunanin sace ta aka yi domin sai dare take dawowa, daka ganta da sassafe kuma ta fita bayan babu wani ciwon hauka ko shafar aljanu a jikinta, kawai tsabar fitina ce da rashin son zama guri guda. Cikin takaici domin sam Talatuwa ba taji dad'in ganinta ba duk surutunta sai Aliya ta 'kure ta, bata san lokacin da tace da ita.

"Aliya zuwa kika yi?" Aliya tana shirin d'aukar goron gwaggo dake kan ice tace.

"Zuwa nayi gwaggo Talatu, ko baki yi farin cikin gani na ba kakata ta kaina?"

Murmushin yake Talatuwa tayi tana kallan Aliya, ko tace ba tayi farin ciki ba tasan ba komawa zata yi ba dan haka ba taga amfanin cewa eh ba, aikinta taci gaba da yi kafin tace.

"Ina su Adama?" Aliya na zama a kan tabarma tace.

"Suna can a 'kauye, ai wallahi inna Adama ta tsaneni gwaggo, kinga yadda ta koroni kuwa wai harda cewa na tafi can inda aka haifi uwata dangin jaraba, wallahi gwaggo so nayi nak'i tahowa tunda ai can d'in ma akwai jini na a gidan, da suka kama suka wani koreni."

Gwaggo Talatuwa ta yatsina fuska tasan kila wani abun ne ya faru shi yasa suka koreta, amman haka kurum Adama ba zata ce Aliya ta taho nan ba har da uban kaya, yadda Adama keji da Aliya saboda abin arzikin da ake kai musu sanadin ta, kasan cewar kyakyawa ce samarin birni idan suka ganta sai sun yaba da halittar fuskarta saboda akwai hanci ga gashin gira da na ido sai dai akwai 'kauyanci da rashin kunya domin bata ganin girman duk wanda zai yi mata magana ta nasiha ko kayi mata hannunka mai sanda.

"Toh Allah ya kyauta."

"Amin gwaggo ina Fa'iza take ne?'" Gwaggo Talatuwa tace.

"Tana makaranta kinsan yanzu karatun nasu yayi zafi tace min jarabawa zasu yi ta fita daga primary, kullum cikin karatu take yarinyar nan ko hutawa bata yi ita a dole sai ta zama likita wai."

Dai-dai sannan Fa'iza ta shigo gidan da murnar ta, duk juyawa suka yi suna kallanta taje ta rungume Aliya cikin murnar ganinta dan Shamsu ya shaida mata tazo, raken da ke hannun Fa'iza Aliya ta 'kwace tana cewa.

"Wannan kuma fa Fa'iza, na gutsira?" Fa'iza na k'ok'arin zama tace,

"Takice daman aka ce na kawo miki."

"Inji waye?"

"Inji Shamsu mai raken dake nan k'ofar gidan, na d'auka siya ki kai kika ce ya aiko miki da ita idan ya yanka?"

Girgiza kai Aliya tayi alamun ba siya tayi ba ta fara gatsawa tare da da cewa Fa'iza.

"Jeki d'akko wuka na gutsirar miki."

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Onde histórias criam vida. Descubra agora