7

1K 45 0
                                    

*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

——
*I/9/S*

*G/G/S/S/S.... SUMAILA*

Tun lokacin da aka kai su kasancewar su kyawawan yara, yasa manyan makarantar wato 'yan aji shida suka fara rubibinsu da son yin school daughter's dasu, ss1b shine ajin da aka kai Fa'iza, ita kuma Aliya aka kaita ss1c, sunci sa'a aka kaisu hostel d'aya, inda aka kaisu corner d'in captain d'in hostel d'in. Kasancewar Aliya tafi Fa'iza rawar kai hakan ya sanya kowa yake janyota jikinsa, tun a ranar suka tabbatar da cewa lallai sunzo makarantar kwana domin suna zaune suka ga an fara gudu kowa yana 'daukar kwanonsa, Aliya ce ta kasa yin shiru sai da ta tambayi ta kusa da ita wadda taji ana kira da sister Bakori tace,

"Sister Bakori ina za'aje ake gudu?"

Rumaisa'u shine asalin sunanta, kasan cewar 'yar Bakori ce shine sunan nata ya 'boye kawai ake kiranta da hakan, ta kalli Aliya tana murmushi tace,

"Dining hall zasuje su karbi abincin rana, kuma ku shirya sai captain d'inku ta tafi daku ta zuba muku."

Tashi suka yi ko wacce ta bud'e akwatin ta suka d'auki robobin su merry verry (irin ta almajirai),sunga abin mamaki ganin yadda kowa ya jeru gashi gurin yayi tsit bakajin komai su maganganun prefects suna ta shewa, jansu aka dinga yi, robobin su kuwa sai da aka cika musu su da taliya. Haka sukaci gaba da rayuwa suna jin dad'i domin Mommy's d'insu na can sun tsaya musu, head girl itace Mommyn Fa'iza, sannan labour prefect ta Aliya, an gatanta su na tsawon lokaci kafin su fara d'an-d'anar wahalar makaranta, dan sai da ya zamana wata ran basa samun ruwan wanka dan an dena basu kamar yadda ake musu a baya.

Duk abinda Aliya take yi hakan baya hanata maida hankali wajan yin karatu, tana daya daga cikin zafafan ajinsu, malamai da dama suna ji da irin fikirarta kamar yadda Fa'iza ma take a ajin su, sosai suke karatu kuma duk da haka baya hana Aliya yin wasu abubuwan. Ana gobe visiting suka samu damar yin wankin uniform dinsu, suna bushewa suka ninke ko wanne yasa nashi a 'karkashin katifarsa saboda su samu suyi karin goga yadda za'a gansu fes.
                       •••
   *A* can gida kuwa dama tunda suka baro gidan gwaggo sai Baba Suleiman yaje ya d'auke mahaifiyarsa daga gidan ta, ya maida ita gidan shi, da kyar gwaggo Talatuwa ta yadda saboda a cewar ta kartaje su dinga samun matsala da matarsa, amman yace mata babu komai, babu yadda zata yi haka ta bishi suka tafi, d'aki d'aya aka bata daga can baya harda band'aki a cikinsa yadda ba sai ta fito sun had'a toilet da surukarta ba.

"Gwaggo zakije visiting?"

Maman su Fa'iza ta tambaya bayan ta d'aga labulen d'akin gwaggon, Gwaggo Talatuwa dake gyara 'dan tofin cikin zaninta tace,

"A wane garin yake shi zibitin d'in?"

Gwaggo ta tambaya tana kallanta cike da son jin karin bayani. Sai da Mama tayi murmushi kafin tace,

"Gwaggo ba gari bane, ina nufin zakije ziyarar su Aliya makaranta."

D'an Jimm! Tayi kafin tace,

"Allah sarki 'yan jikokina, zanje mana na ga halin da suke ciki."

"Toh shikenan gwaggo, gobe ne dama za'a yi shi yasa nace bari nazo na tambayeki ko zaki je?"

Fitowa tayi ta wuce tana ci gaba da harhad'a kayan da za'a tafi musu dashi goben, yayin da itama gwaggo ta fara yin nata, inda ta bayar aka siyo mata manja da man gyad'a ko wanne ta zuba mishi a jarkar lemo, ta siyo aya da sauran abubuwan da duk tasan jikokin nata suna so.

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now