4

1.2K 47 1
                                    

*............_KAI MIN HALACCI!_*
      💕

_*NA_*

_*©️NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO)_*

®️_*HASKE WRITERS ASSO💡_*

       *_SHAFI NA HUDU(4)_*
             _*KAI MIN HALACCI!_*
                               💕

nanahafsat.wordpress.com

"Amman dai gaskiya kai d'an k'auye ne wallahi, ya zaka nacewa yarinya sai kace idanunka sun rufe?okay na gane saboda kyanta shine duk kabi ka damu har kake jure duk wannan iskancin da take yi maka ko?"

"Ba zaka gane ba khaleel, duk wani abun da zan gaya muku ba zaku tab'a ganewa ba indai akan yadda nake jin Aliya a raina ne."

"Kaji wawa, dalla can matsa kai nan gaba bamu san me mace zata maida kai ba."

Kabeer yayi maganar yana mik'ewa tsaye, sallama yayi musu ya tafi sabida ya tabbatar idan ya zauna a wajan toh zasu iya samun sab'ani da abokinsa, yarinyar ta had'u, sai dai bata da kunya shi kuma zai iya zaneta tunda ba soyayya tsakaninsu, wanda yake son ta kuma zasu iya samun sab'ani da shi duk kuma a kanta bayan sun jima cikin yin abota tsakanin su.

"Gaskiya Shamsu ka canza takun ka akan yarinyar nan, karka ja ta raina ka duk da kariga ka janyo tunda ka furta mata kalmar so."

Cewar khaleel yana k'ok'arin ajiye kofin shayin da ya gama sha, shima Shamsu tashi yayi, sakamakon wani mutum da yazo siyan sabulun wanki yaje ya bashi daga nan be sake barin sunyi maganar Aliya da khaleel ba, Saboda baya son duk wani abu da zai sa a zagar masa ita. Ita kuwa Aliya haka tayi ta fitowa neman Kabeer wajan Shamsu baya nan, daga 'karshe ce mata yayi tafiyar sa zuwa makaranta saboda yasan duk wannan neman da take yi masa wulak'anci zata mai kuma yasan Kabeer ba kyaleta zai yi ba musamman da yasan baya kaunar yarinyar. Cikin hukuncin Allah Abban su Shamsu yasamarwa Aliya makarantar secondary js one tare da temakon gwaggo Talatuwa, Saboda bata san wannan zaman da Aliya keyi na janyo mata surutun da yafi karfin ta.

Shi kuwa Shamsu kasuwarsa ce ta shahara wajan yin ciniki ga arha ga sauki domin wani shago ya bud'e anan unguwar tasu daga d'aya b'angaran, dan gidan suma yana kallan shagon nashi k'ato dashi na provisions, babu abinda babu a cikin shagon hakama yana da yara masu kular masa da customers d'in shi, sai dai kawai shi ya zauna a gurin ko kuma yaje ya siyo wasu abubuwan, cikin k'ank'anin lokaci ya bunk'asa gashi duka befi shekaru Ashirin da biyu ba, ya kuma bud'e shagon saida wayoyi da yin charge ga kiwon kaji da tantabaru da Umma take kular masa dashi, sosai Allah ya sanya masa albarka a cikin kasuwancin amman duk da haka Aliya bata son shi sai dai taci abin hannunsa, yayin da shi kuma befasa kyautata mata ba kamar yadda ya saba.

Cikin takun ta na cewa itama fa yanzu 'yan mata ce kuma budurwa, tazo wucewa ta gaban shagon sa, yana zaune akan kujera a k'ofar shagon nasa. Yayin da daga cikin shagon kuma wak'ar *alagidigo* ce take tashi ta cikin speakers hannunsa rike da game yana ta faman yi.

Muryarta kawai ya jiyo kamar yadda ta saba duk lokacin da ta hangoshi a guri ko cikin mutane abokansa ne sai tayi masa waka, tun lokacin da tsautsayi yasa shi furta mata kalmar SO.

Satar kallanta yayi yaga yauma ta cokaro d'aurin d'ankwalin nan nata wato ture kaga tsiya, mayafin nan a kafad'arta ta tsaya dai-dai shagon, kusa da wata mai suyar awara ta rike kugu tana karkad'a jiki bakin nan yasha kanta kile, cunoshi take tana waka.

_''Allah ya tsine wa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yazo.., jiya ma yazo..yauma kuma zaizo...!''_

Kamar yayi shiru ya kyaleta kamar kullum idan tayi, amman yau zuciyarsa tana son ramawa dan bai ga dalilin da zai sa k'aramar yarinya dan yace  yana sonta ta dinga gasa masa magana a fakaice ba, dan haka shima yana danna game d'in ba tare da ya kalleta ba yace.

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now