5

1K 26 0
                                    

*Littafin nan na kudi ne, me so DAN GIRMAN ALLAH ya nemi wannan number 08030811300 YA BIYA YA KARANTA*

*💕*
*F/S*

Murmushi A..... tayi, dan tasan da wasa Fa'iza take yi mata ba zata fad'a ba, kawai dai tasan ba tasan mu'amular su, gashi daman tana jin haushin abinda ta yiwa Shamsu. suna shiga gida Baba Suleiman ya kalle ta, suka had'a ido ganin yanayin sa yasa ta saurin yin k'asa da idanun ta, jira kawai take taji ya fara yi mata fad'a, amma taji shiru, sai muryar Fa'iza da ta katse mata tunani inda take cewa,

"Baba gata nan wallahi tare na gansu ita da wannan saurayin Sahal na gidan, sun kusan mannewa da juna."

Zaro ido Aliya tayi, Cikin firgici dan bata tab'a tunanin Fa'iza zata tona mata asiri ba, kuma wannan shine karo na farko da ta fara duk da cewar ta b'oye cewar a jikinsa ta ganta tace sun kusa ne kawai, wani banzan kallo Baba Suleiman yayi mata tare da had'e rai yace,

"Wato Aliya har yanzu kina nan da rashin mutuncinki da rashin tarbiya ko? Har yanzu baki dena mu'amula da abokanta ka da maza ba ko? Sai anyi miki fad'a ki fara kuka kina cewa an tsaneki, saboda munga iyayenki sun mutu ko? to wallahi bari kiji na gaya miki bana san iskancin banza dana wofi ni sai naci ubanki nan take, duk wani abun da za'ayi miki fad'a kinsan shi, ni nama fara tunanin kai ki makarantar kwana (boarding school), kinga bakya garin ma bare ki dinga janyo mana magana."

Kamar ya sani kuwa sai kawai ta fara zubar da hawaye, gashi taki ta bashi hakuri hakan ne ya sake tunzura shi yace mata,

"Tunda baki da kunya zanje duk yadda zanyi na samo miki boarding ki tafi, kuma ke kad'ai zaki tafi ba tare da Fa'iza ba, sabida ita tana zama gurin gwaggo tana yi mata wasu aiyukan."

Tana jin haka kuwa sai ta saki kukan ya fito waje, tana matsar hawaye gwaggo na zaune tana cewa,

"Wallahi kuwa gara a kaita can d'in, idan ta dawo hutu muka ga babu wani canji sai ka kaita gidan kangararru can su horata tunda mu ta raina mu, bata ganin girman mu da mutuncin mu.."

Wani matsanancin kuka ne ya sake zuwar mata, tana jin wani irin takaici a ranta, ta kasa gano ainahin abinda yasa basa so tana mu'amula da mutane musamman masu kud'i.

"Wallahi Baba sharrin Fa'iza ne kawai munafuka, lokacin fa da taje na fito ma zan dawo gida shine fa muka had'u da Sahal d'in a bakin gate, to ina cikin gaidashi yana amsawa sai gata ta shigo tace kana kira na, dan Allah Baba karka kai ni boarding, wallahi bana santa ana kwasar aljanu da gudun gardi cikin dare wayyo Allah na.."

Cikin rashin damuwa da yadda yaga ta shiga cikin tashin hankali na rashin san zuwa makarantar kwana yasa shi kuma had'e rai yana nuna ta da yatsansa,

"Kuma daga yau duk ranar da naji ance bakya zuwa makarantar islamiya data dare wallahi-wallahi kinji nayi rantsuwa, sai ran ki yayi mummanan b'aci, babu ke babu zuwa gidan kowa indai ba gwaggo ce ta aike ki ba, wannan shine karo na karshe da zanyi miki gargad'i, idan kika sake aikata wani abun zaki ga abinda zanyi miki, tashi kije kuyi shirin makaranta kuzo ku wuce."

Tana kuka ta mik'e, d'aki suka shiga ita da Fa'iza suna zuwa ta cakumi wuyan Fa'iza suka fara fad'a, 'karar da su gwaggo suka jiyo ne yasa Baba Suleiman lek'awa, a kan gadon gwaggo mai rumfa ya hangosu sai dukan junansu suke yi, ya shiga da sauri yana salati, cikin zafin rai gabaki d'aya ya janyo su ya wawwam ka musu mari, wanda yasa duk kan su fashewa da kuka mai sauti,

"Wato ni zaku mayar d'an iska ko? Wai menene ma ya fara kawo rigimar daga shigowar ku ciki?"

Shiru suka yi wanda ya sake bawa Baba Suleiman haushi, yaja tsaki tare da zama a bakin gadon ya kalle su, yana cewa,

"Ku saurareni da kyau kuji, sam bana jin dad'in yadda kuke wannan banzan zaman naku, babu wacce tafi wata a guri na domin duk 'ya'yana ne ku, sannan babu abinda ya raba tsakaninku, idan wata tana jin cewar anfi son ta a cikin ku to ta dena, sannan idan wata tana ganin an tsaneta itama ta dena, dan tushe d'aya ne yayi ku, idan baku san asalin ku ba toh ku tsaya kuji da kyau dan kar wata tayi zaton ko 'yar rik'o ce ita."

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Onde histórias criam vida. Descubra agora