2

1.6K 60 6
                                    

*~............_KAI MIN HALACCI!_*
      💕

_*NA_*

_*©️NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO)_*

®️_*HASKE WRITERS ASSO💡_*

       *_SHAFI NA BIYU(2)_*
*_~*

Bayan wasu kwanaki sai ga Shamsu ya shigo gidan da baro mai dauke da damin rake, Umma na daki taji gararam cikin sauri ta fito dan ganin abinda yake faruwa, tsaye tayi tare da kama baki tana kallan Shamsu dake k'ok'arin sauke damin rake, tayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa.

"Kai dakata malam, wannan kuma ta waye kaje ka rakito mana uban 'yan kwashe-kwashe?"

Shamsu ya tuntsure da dariya ba tare da ya fasa sauke raken ba, sai da ya jinginar dasu sannan ya matsar da baron gefe yana karkad'e jikinsa yace.

"Umma wannan fa ba kwashe-kwashe bane, kayan sana'ata ne tunda nace ki dinga yi min fanke da kunun zaki ina siyarwa kinki, shi yasa naje na siyo abinda zan fara siyarwa anan kofar gidan."

Baki da hanci Umma ta bud'e kafin ta nufi d'akin mai gidan, Shamsu na ganin haka ya juya da sauri ya tura baron ya fita zaije ya mayarwa da masu ita, yasan 'karar sa zata kai gurin mahaifinsu. Kamar ya sani kuwa, Umma ta samu abban su Shamsu yana shirin zuwa masallaci kasan cewar juma'a ce, fuska cike da damuwa tace masa.

"Kaga wannan yaron nema yake yaja mana abin magana."

Abba dake karya hularsa ya kalli matar tasa yana son jin 'karin bayani, kafin ya tambaya tace.

"Shamsu mana, ko kasan wai rake yaje ya siyo, wai siyarwa zai dinga yi kuma a nan kofar gidan salan yaja mana zagi wajan mutane."

Ga mamakinta sai taga yayi murmushi yana jujuya kai kafin yace mata.

"Alhamdulillah dadi na da yaron nan akwai neman nakai, yanzu ke menene abin damuwa dan zai fara sana'a? Ai wannan k'ok'arin hanashin da kike yi shine zai sanya ya janyo mana magana domin zai iya d'aukar abin wani ko kuma abokai su rinjayesa ya shiga cikin wata mumunar rayuwar, amman yanzu fa? halal d'insa fa yake nema kuma ma yace miki anan kofar gidan zai yi, kinga riba biyu kika samu, na farko kinsan d'an ki yana da sana'a, sannan idan kina nemansa dakin lek'a kofar gida zaki tarar dashi toh mai yafi ranki Umman su?"

Washe baki tayi dan sosai taji dad'in yadda maigidan nata ya wayar mata da kai, cikin jin kunya dan tasan zai bata rashin tunani irin nasu na mata a wani lokacin idan sunyi abu tace.

"Kwarai kuwa Abban Shamsu domin da yaje ya kwaso min magana, gara a zauna a kofar gidan yayi sana'arsa ko wacce iri ce, Allah ya dafa masa daman yaron nan akwai shi da son kasuwanci."

"Yauwa toh kinga ni kema, yanzu dai babu abinda yake buk'ata a gurinki sai addu'a nima zan taya ki Allah yasa albarka a cikin duk wani abu da yaran nan zasu fara."

Cewar Abban su Shamsu, Umman su ta rausayar da kai tare da cewa.

"Amin ya Allah."

"Toh ni zan tafi masallaci, sai Allah yayi mana dawowa."

Sai da ta gyara masa mab'allin rigarsa, sannan ta mik'a masa sallayar da zai tafi da ita tana cewa.

"A dawo lafiya a samu cikin addu'a." Sai da ya fito sannan yace da ita.

"Zanyi miki kuwa harda ta samun 'yan biyu k'annan Shamsu."

Cikin sauri tace. "Ba amin ba wallahi, haba Abban su ya za kai wannan fatan da girmana, haihuwa sai dai in kaine kayi amarya sai taxo tayi 'kannan amman banda ni.''

Dariya yayi yana fita, shi tunda yake a rayuwarsa bai tab'a ganin matar da take neman ayi mata kishiya ba sai matarsa, wani lokacin idan tana yi masa magiyar ya 'karo aure sai yayi ta tunanin ko son shi ne ba tayi take ta matsa masa akan yayi aure. Ita kuma tana ganin kamar yana san 'ya'ya da yawa ita kuma gashi tun guda biyu da Allah ya bata, bata kuma yin koda b'atan wata ba, hakan yasa take son ya kara aure saboda farin cikin sa. (Tab kunji true love).

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now