10

823 30 0
                                    

*_

Dariya Faysal yayi yana bubbuga kafa a kasa tsabar mugunta, Salman ya kallesa cikin b'acin rai yace,

"Ba wannan ne zai baka haushi ba, kasan yarinyar nan har yanzu taki bari naje gidan su, kullum sai tace min ba yanzu ba wai Maman su ta hanata kula samari na bari duk lokacin da aka ce ta fara zata min magana."

Ya k'arasa maganar yana jan d'an guntun tsaki tare da cusa wayar tasa a aljihu ransa duk a b'ace. Faysal ne ya bugi gefen kafad'ar Salman tare da cewa,

"Toh kai abinda na kasa ganewa shine, shin kana sonta ne kokuwa dai kara yawa kake yi da ita?"

"Wallahi nima ban sani ba Faysal, ban san tak'amaimai wane iri nake ji akan Khadija ba, ina sonta ban sani ba, bana sonta shima ban sani ba kawai dai naji ina son kulata wani lokacin, gashi idan muna waya ko idan mun had'u a hanya wallahi bana jin wani abu akanta."

"Kai dalla can baka sonta haka kawai zaka ce bawai ka tsaya rainawa mutane hankali ba, idan banda rainin hankali ai abu uku ne zaka zabi d'aya, kodai kana so ko baka so ko kuma kawance kake da ita, meye na tsayawa yi min kwana-kwana."

Shafa kai Salman yayi tare da huro iska daga cikin bakinsa, kasa cewa komai yayi domin babu abinda zai fad'a dan haka ya mik'e yana gyara wuyan rigarsa tare da kallan Faysal yace.

"Abokina zan wuce, idan na samu amsar tambayoyinka zanzo na sanar dakai, amman yanzu bani da ta cewa, sai anjima mu hadu a gidan kallo ya za'a buga mai zafi."

Faysal ya tab'e baki tare da mikewa shima ya shige cikin gida.

A can b'angaren su Umman Shamsu kuwa sun tattauna maganganu ita da aminiyarta wato mahaifiyar Khadija akan yadda suke son komai ya tafi ba tare da ko wanne b'angare yaga anyi masa rashin adalci ba. Umma ce zaune akan sallaya ta idar da sallar magriba taji kira, tana dubawa taga sunan auta, cikin murmushi ta d'aga tare da karawa a kunne tayi masa sallama cikin farin ciki,

'"Assalamu alaikum Ummah nah."

"Wa'alaikas salam d'an auta yaron kirki, ya kake?'"

Shamsuddeen dake zaune kan teburin cikin abinci a wani katafaren restaurant gabansa drink ne kawai yana sha, bayansa ya jingina a jikin kujerar yana sauraran Ummansa wadda yake jin tamkar yayi tsintsuwa yaje ya ganta, ya shafa kwantaccen bakin gashin dake kwance a hab'arsa tare da cewa,

"Umma lafiya ta kalau, sai fama da rashinku a kusa dani, ina Abba ne? sai kiransa nake amman ana cewa a kashe take."

"Aikuwa nima kaga sai kiransa nake bana samu da yake nazo nan gidan Maman Khadija."

Cikin murmushi mai d'an sauti Shamsu yace mata,

'"Ahh yau ankai ziyara kenan? Umma a mika min gaisuwa wajan Maman."

Dai-dai sannan Maman Khadija ta shigo dakin hannunta dauke da tray na abincin da ta kawowa aminiyar tata.

"Gata ma kawai ku gaisa."

Cewar Umma tana mika mata wayar. A kunne ta kara cikin kulawa itama ta fara yi masa magana, cikin girmamawa ya gaida ita ta dinga sanya masa albarka sannan ta mik'awa Umman sa, hirar sukaci gaba da yi lokacin ne Khadija ta shigo hannunta d'auke da jug na ruwan sanyi ta kawowa Umma ta ajiye mata a kusa da tray din abincin, tana k'ok'arin fita Umma ta dakatar da ita ta hanyar cewa.

"Khadija zoku gaisa da Shamsuddeen."

Khadija ta juyo tare da zuwa kusa da ita, ranta duk babu dad'i sai dai babu wanda zai fahimta sakamakon murmushin yak'en dake saman fuskarta.

"Shamsu ga Khadija ku gaisa."

Cikin rashin damuwa Shamsu yace.

"Okay Umma bata"

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon