1

5.9K 136 8
                                    

_بسم الله الرحمن الرحيم_

_In the name of Allah, the Gracious, the Merciful...!💕_

"Tsakanin d'an Adam..d'an Adam.. tsakanin d'an Adam da kud'i..! Kai..! Wayyo Allah na! Ooh! ya Subhan'Allahi Allah ka rabamu da babu ko ta mecece ma, na rantse da Allah idan aka ce yau baka dashi toh sunanka sorry Umma.."

Wani matashin saurayi dake sunkuye wajan rijiya yana wankin uniform d'insa shine yake wak'ar, yana kuma had'awa da addu'a duk da cewar yayi tane cikin takaici da jimami.

"Amin ya rabbil alamin Shamsu, ai talaka yana d'an-d'anawa a cikin k'asar nan, shi yasa muke son kayi karatu sosai, wata rana ka zama wani babban a k'asar nan."

Matar dake zaune kan tabarma can nesa dashi take bashi amsa, tare da nuna masa burin su akan sa, nasan cigabansa nan gaba.

"Kai! Umma ni fa gaskiya wallahi na gama karatu daga secondary d'in nan, haba! hauka ake yi, ni yaushe zan zauna nayi ta cin boko kamar wani marar aikin yi? Ina.. billahil'azim babu inda zan d'ara daga wannan karatun kinji na rantse."

Murmushi tayi tana girgiza masa kai,

"Shamsu kai yaro ne, ba zaka tab'a gane abinda muke son ka gane ba a yanzu, shin idan baka yi karatun ba ta yaya zaka cika burin ka a rayuwa nan gaba?"

Ya kad'e rigar uniform din, fara 'kal da ita ya shanya a igiya kafin yace,

"Umma ba fa sai kayi mugun karatu kake zama wani a cikin k'asar nan ba, ki duba ki gani d'an majalisar jaharmu mai wakiltar mu iyakarsa sakandire, amma aka d'auki mulki aka bashi, shima sanatan mu iyakarsa NCE. Amman ki duba su Alhaji Aminu, su engineer Tijjani duk degree na biyu gare su, amman suna k'asa, saboda wad'ancan suna da kud'i shi yasa duk takarar duniyar nan sune suke cinye wa, dan haka na sawa raina wallahi daga wannan karatun ba zan d'ora wani ba Allah ya amfana wanda nayi."

Tasan duk yadda zata nuna masa ba zai gane ba, Saboda abinda yake cikin zuciyarsa hakan yasa tayi masa fatan alkairi cikin ranta, can kuma ta d'ago tana kallan sa yana shanya wandon a jikin igiya tace dashi.

"Amman dai Shamsu ba harkar siyasa zaka fad'a ba ko? Ni wallahi bana son ta, Azo ayi ta zaginmu ana ambato ahalin mu wad'anda kai kanka baka sansu ba."

Dariya yayi wanda kyakkywan dimples d'in sa suka lotsa, wushiyar sa ta bayyana, yana kallan Umman tasu yace.

"Kai Umma ke duk wata harkar samu sai kice bakya santa ki yi ta kushewa idan ki kaga anfi samu a ciki, toh bari dai mu gama makarantar sai muga abinda ya kamace mu muyi wanda zai yi dai-dai da ra'ayin ki."

"Ah'ah ni 'karya kake yi min Shamsu, yaushe na kushe abinda yake kawo samu ne? kawai dai ina nuna maka muhimman abubuwa ne da zaka yi ka cimma burin rayuwar ka, kaga da zaka samu ko NCE ko kuma 'yar diploma, kayi ka rike kwalin zai yi maka amfani nan gaba."

Tsalle yayi ya dire kan k'afafunsa, kamar wani d'an k'aramin yaro, jin Umma tana kuma cusa masa son ci gaba da karatun da baya so, yana tafiya wajan bokitin da ya zuba ruwan d'auraya yace mata.

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now