NANNY..

1.8K 163 0
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕

_Don't Forget to Follow us on Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA SHA TARA*

Ƙarfe 2:40pm. Ta isa Ɗanbatta, Tahir da Hakimi da sauran mutane suna zaune a ƙofar gidan suna karɓar gaisuwa gurin jama'a masu zuwa musu ta'aziyya, haka ta ratsa tana sunne kai ta shige cikin gidan, tana shiga direct ɗakin Goggo Abu ta dosa.

Tana shiga da Umma suka fara haɗa ido, rass taji gabanta ya faɗi tana turo baki ta ƙarasa ciki ta zauna a kusa da Goggo Abu ta duƙar da kai taƙi kallon kowa dake ɗakin, Mufeeda kuwa tana ganin Farida ta shigo tayi maza ta miƙe ta fita falon Goggo ta zauna, don bata son abinda zai haɗasu da Farida guri ɗaya, gani take zata iya rufeta da duka don haka take jin tsoronta.

Miƙewa Goggo Abu tayi itama ta fito falo gurin Mufeeda ta zauna akabar Umma da Farida kaɗai a cikin uwar ɗakin, ɗagowa Farida tayi tana kallon Umma tace "Umm..." Da sauri Umma ta dakatar da ita tana watsa mata harara take faɗin "Uban me ya kai ki gidan Bilkisu Farida...? Wato dai ke har yanzu bazaki natsu kiyi hankali da duniya kisan me take ciki ba ko Farida.? Yanzu da kika je gidan Bilkisun uban me kikaje tayi miki? Me ma yasa kika saka ƙafa wai kika bar gidan mijinki da 'ya'yanki bayan duk irin faɗan da nayi miki ranar kafin mu tafi? Wato baki ji ba shine kika shure kika tafi gidan ƙawa har na tsawon kwanaki huɗu kina can a zaune saboda gaki ballagaza ko...? To uban me kika je yi gidan aurenta tayi miki..? Tana zaune da mijinta lafiya ke da baki san mutunci da darajar naki mijin ba shine kika kwashi jiki kika tafi gidanta tayi miki maganin taki matsalar ko?" Ta faɗa a hasale tana ji aranta kamar ta tashi ta rufeta da uban duka saboda takaicinta, ita ko Farida wani bala'in haushin Bilkisu ta ƙara ji a zuciyarta, take wasu hawaye suka fara zubowa daga cikin idanunta Umma na kallonta tace "Ai kuka kam yanzu kika farashi Farida..tunda dai kince ke ba mai hankali da tunani bace balle kisan ya kamata, na ɗauka zaki yi nadama ne saboda abinda sakacinki da toshewar tunaninki ya janyo muku ke da mijinki, ashe ba haka bane, ke inda tunaninki yake daban, abinda kika ɗaukarwa zuciyarki tun farko shi zaki ci gaba da yi. To kiyi Farida, bance ki  fasa ba kici gaba..." Haka Umma tai tawa Farida faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Farida kuwa in banda kuka ba abinda take yi har da shassheƙa, sai yanzu ne ita da kanta take ganin aibun abunda tayi a rayuwarta, bata kyautawa kanta da 'ya'yanta ba, uwa uba kuma mijinta, bata tashi sanin babban kuskuren data tafkawa rayuwarta ba, sai data je gidan Bilkisu taga yanda take yiwa mijinta take kaffa kaffa dashi, bata haɗa komai da mijinta ba. Ita yanzu wace riba zata ce taci na irin halayen dasu Bilkisu suka dinga zigata suna ɗorata akai kuma tana bi...?

Umma ce ta katse mata tunanin da take da faɗin "Yanzu a irin waɗannan abubuwan da kike yi wace riba kika samu? Me kuma zaki ɗorar? Miji ya gaji da halinki, har ya daina damuwa da duk wasu lamura da suka shafeki, kin kaisa bango halayenki sun gama isarsa, kin tafi kin bar gidan mijinki da 'ya'yanki kin tafi gidan ƙawa kin zauna har tsawon kwanaki, kin gama fallasa kanki da zuri'arki a gaban ƙawayenki, sirrin gidanki da komu bai kamata mujishi ba kin gama tallatashi a titi ga wasu can kinyi terere da mijinki, don nasan sai kin gaya musu duk abinda yake faruwa, tunda tunaninki ya gama toshewa..." Ta faɗa tana murmushin takaici, wani kukan baƙin ciki Farida ta fashe dashi tana girgiza kanta, kafin ta ɗago hawaye na tsirarowa daga cikin idanunta tace "Umma don girman Allah..." Sake dakatar da ita Umma tayi da faɗin "Komai kika yi fa kanki kika yiwa, nidai zanci gaba da tayaki addu'a Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya. Don haka maza ki tashi kije ki yiwa Mufeeda gaisuwa..." Ta faɗa tare da miƙewa, itama Faridan tashi tayi tana share hawayen fuskarta tabi bayan Umma suka fito falo, inda Goggo Abu da Mufeeda suke sai Nailah da Iya da Maman Lantana, Umma zama tayi a kusa da Mufeeda tana kallon Farida da tayi tsaye tana kallon Mufeeda a sace tana turo baki alamar bazata iya ba an takura mata, wani kallo Umma ta watsa mata ba shiri ta dubi Mufeedan data sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da bakin hijabinta, sai data zabga mata uwar harara kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Ya ƙarin haƙuri...Allah ya jiƙanta ya gafarta mata.." Ta faɗa a tare tana zama a kujerar dake falon.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now