NANNY..!

2.5K 187 22
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕

_Dont Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA SHA UKU*

Gyaɗa kansa yayi hawaye masu zafi da raɗaɗi na zuba daga cikin idanunsa ya duƙar da kai ƙasa yace "Tabbas nine nayi mata ciki...cikin jikin Mufeeda nawa ne bana wani ba..." Yana faɗa ya sake rushewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya da ban tausayi. Itama Mufeeda ƙara sautin kukanta tayi da ƙarfi zuciyarta cike da tausayin Daddy ta tsura masa ido tana ji a ranta dama wannan ranar bata zo musu ba.

Gaba ɗaya falon salati suka ɗauka kowa faɗi yake "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...." Yayinda ita ko Farida ta ƙara gigicewa ta ruɗe da jin kalaman da Tahir yake faɗa, lokaci ɗaya komai ya tsaya mata cak, sai aikin nunashi take da yatsa tana girgiza kai ta kasa magana, kafin ta koma da baya ta faɗa saman kujera daɓas ta zauna a ruɗe tana faɗin "A'a Abban Basma don Allah kar kace haka...wannan nasan ba gaskiya kake faɗa ba...nasan ba halinka bane a ko'ina kuma zan iya yin shaidarka akan haka...kuma nasan kowa ma zai yi shaidarka indai akan haka ne, nasan ko akan wata bazaka taɓa iya aikata haka ba, balle akan Mufeeda 'yar damuka raina muka ɗauketa tamkar 'yar da muka haifa da cikinmu...plz Abban Basma karka sakamu cikin wani yanayi plz kace ƙarya ne abinda ka faɗa ba gaskiya bane...don Allah kace ƙarya ne Abban Basma.." Ta faɗa tana ji a zuciyarta dama a tasheta ace mafarki take ba gaskiya bane abinda kunnuwanta suke jiye mata ba.

Yana kallonta da idanuwansa da suka rine sukayi jajir suna tsiyayar ruwan hawaye yace "Tabbas Farida abinda na faɗa gaskiya ne, kunnuwanki sun jiye miki dai-dai...cikin dake jikin Mufeeda nawa ne...nine na yiwa Mufeeda ciki..cikina ne...amma a bisa ƙaddara data faɗa min ba'a son raina ba..." Salati duka falon suka ƙara ɗauka, kafin Inna Fulera ta fashe da kuka mai sauti ta miƙe ta cakumi Mufeeda ta fizgota ta rufeta da duka baji ba gani tana yi tana kuka take faɗin "Kin cuceni kin cuci kanki Mufeeda, kin wulaƙanta rayuwarki kin tozarta kanki...Allah ya isa tsakanina dake..ki rasa sakayyar da zakiyi min sai ta abun kunya...kina marainiya kin zubarwa kanki kima da mutunci...Allah ya gani iya tarbiyya na baki ita dai-dai gwargwado ban san kuma meya shiga kanki ba har kika iya watsar da mutuncinki a titi ba..." Ta faɗa tana ƙara shurinta da ƙafa tana kuka, Mufeeda ma kukan take tana jujjuya kanta amma ta kasa tashi ta ƙwaci kanta, da sauri Tahir ya matso ganin Inna Fulera ta ɗaga ƙafa zata taka cikin Mufeeda tana faɗin gwara na kasheki da inci gaba da ganinki ina jin baƙin cikinki a raina, da hanzari ya riƙeta yana girgiza kai a hankali yace "Laifina ne Inna, ita da niyyar taimakona tazo, dukkanmu bada niyya mukayi ba...ƙaddara ce ta afka mana..." A fusace Farida ta miƙe tana faɗin "Babu ruwan ƙaddara Malam, dama can kana da niyyar aikatawa shine zaka fake da ƙaddara..." Ta faɗa tana fashewa da kukan takaici da baƙin ciki tana faɗin "Amma Tahir ka cuce ni ka cuci zuri'arka ka wulaƙantamu, yanzu da wani irin idanu kakeso a kalli 'ya'yanka? Ka ɓata mana sunan zuri'a, ka haikewa 'yar da take ɗaukarka a matsayin uba...tirr da kai da irin halinka, wallahi bazan iya ci gaba da zama da kai ba, ni ba fasiƙa bace don haka bazan zauna da fasiƙi ba...sai dai ka zauna da ita da shegen cikinku..." Ta faɗa tana ƙara fashewa da kukan baƙin ciki da takaici tana kallon Mufeeda dake kukan itama tana ji kamar ta tashi ta shaƙeta har sai taga bata numfashi.

Wani murmushin dayafi kuka ciwo Tahir yayi yana kallon Goggo yace "Komai da ya faru bada son raina bane kawai na ɗauki hakan ne a matsayin ƙaddarata kuma na karɓeta hannu biyu, Allah ya bani ikon cin jarabawata... Nan take ya shiga bada labarin duk abubuwan da suka faru, kafin yana kuka ya ɗago yana faɗin "Duk da wannan abun daya faru dani ba kowa bane sanadin shigata wannan halin sai Farida dake Goggo, domin ke kika hanani na sanarwa Baba Hakimi wannan matsalar dake faruwa dani kuma kika hanani maganar ƙara aure, alhalin baki taɓa tambayata dalilin da yasa na nace inaso na ƙara auren ba, sai dai a kullum idan naje miki da maganar irin abubuwan da Farida take yi min sai kice inyi haƙuri zaki mata magana, zata gyara, baki taɓa nuna damuwarki akan halin da nake ciki ko ki tambayeni abinda yake faruwa ba, sai dai dana fara sai ki katseni kice bakyason ayi abunda zumunci zai lalace...Goggo ni ɗanki ne amma baki taɓa damuwa da matsalata ba, domin baki taɓa bani damar nuna miki damuwata ba, sai dai ma kiyi ƙoƙarin hanani faɗawa mahaifina halin da nake ciki, to yau ga abinda kika jawo min nan..." Ya faɗa tare da juyawa yana kallon Farida data daskare a zaune ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi hawaye sai zubowa suke a idanunta, Girgiza kansa kawai yayi yana faɗin "Kuka ai yanzu kika fara yinshi Farida, domin tun asali abunda na dinga gujewa faruwarsa kenan a tsakanina dake...Nayi haƙuri har na kai maƙura amma Farida baki canza halinki ba, nayi ƙoƙarin gyaraki amma baki gyaru ba...kin ɗauke ni tamkar ba mijinki ba, baki maidani a bakin komai ba, baki san ki sauke hakkina dake kanki ba, baki san ki kula da 'ya'yan da Allah ya baki ba...sai dai kullum kina yawon bin gidan bikin ƙawaye, baki san ki tambayeni fita ba, sai dai duk lokacin da kikaso kiyi fitarki kuma ki dawo duk lokacin da kika so ba abunda ya dameki, na nuna miki nima fa mai lafiya ne ba dutse bane kuma dole ne in nemi hakkina a gurinki, amma yawon zuwa gurin biki ya hana ki zauna ki kula dani da 'ya'yanki...kullum baki nan baki nan, kuma kinsan ban ajiye wacce zata kula dani bayan ke ba, tunda ke kaɗai gareni baki damu da wane irin hali zan shiga ba, kedai kawai abunda ya shafeki kuma ya dameki shi kikeyi, 'ya'yan da kika haifa kin barwa masu raino baki damu da tarbiyyarsu ba, baki damu da halin da zasu shiga ba, kedai kawai ki tafi biki..sai kibar gidanki da mijinki da 'ya'yanki babu abunda ya dameki, babu ruwanki da duk irin halin da zamu shiga, Saboda Haka Dukkan abunda ya Faru Tsakanina da Mufeeda Keda Goggo kuna da Alhaki akai..."

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now