NANNY.."

2.7K 273 5
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

'''Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto'''

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA BIYU*

  Tun Bayan daya Dawo Daga masallaci Shida Bassam Lokacin 7 Saura Na Safe,Kai Tsaye dakinsa ya Koma ya iske Naila Tatashi Tana Ta Kuka,Daukanta yayi yana lallashinta Tiolet ya Shiga da Ita ya Tube mata kaya ya Zage yayi mata Wanka Domin Taji Dadin Jikinta Ammh Duk Da Haka Naila yar Wata Goma Sha Daya bata bar Kuka ba Daga Gani Yunwa Takeji Shiyasa yana gama mata Wankan Ya Nadota Cikin Towel ya Sauko Kasa Zuwa Dakin Mufeeda yana Kwalamata Kira.

Iya dake Kichen Ta fito Jin yana Kiran Mufeeda Agaggauce In kaji Ance Iya Zaka zata Tsohuwa Ne Ko Daya Matashiyar Dattijuwa ce Mai Kimanin Shekara Hamsin da Wani Abu Kawai Su Bassma ne Ke Kiranta Iya Tun Sanda Mami ta Aiko ma Farida Da Ita Daga Kano Shine Kowa yakama.

Ganin Tahir da kanshi yasa Ta Washe Baki Tana Fadin"Alhaji kai ne..? Kardai yar Rigimar Tatashi Da Kukanta yau,Barka da Safiya..? Yana Mirmishi ya Rankwafa yana Fadin"Ina Kwana Iya.."Ta Amsa Cike da jin Dadin Yadda Tahir ke Girmamata Da Darajata,Take Fadin"Hala Rigima Naila Keyi Bata ga Uwarta ba.."Yana Sosa kai yace"Eh Wlh Iya Inaga Yunwa Takeji na Mata Wanka Ammh yanzu bata bar Kuka ba Shine nazo Zan bama Mufee Ita Ta bata Madara ko Tayi Shuru.."Iya Ta Mika Hannu Ta Karbeta Tana Fadin"Eh kuma da Yunwar Inaga bari na Dama mata Inaga Mufeeda Barci ne ya Kwasheta Don Nima yau najita Shuru..."Mika mata Ita yayi kafin yace"To Iya..."Daga Haka ta Juya Ta Nufi Dakin Mufeeda Inda Kayan Madaran Nailan Suke da Komai Nata,Shi Kuma ya Juya Ya Haura sama.

Wanka ya Shiga Yafi Minti Talatin Kafin ya Fito Domin Tahir Akwai Dadewa Wajen Wanka,Yana Fitowa Ko Mai bai Tsayawa Shafawa ba Don Tahir Kwata Kwata baya Kaunar Shafama Jikinsa Wani Abu,Wardrope dinsa ya Bude yaDauko Daya Daga Cikin Fararaen Gezner nan Shi Dinkim Tarzace,Wanda ya Amsheshi Sosai Aikin Jikin Shaddar baki ne,  Hular Kansa Zannar Bukar mai Zanen Baki ce,Haka Rufaffen Takalmin Kafarsa na Ma baki ne,sai Kyakyawan Agogon Fatar Dake Hannunsa na Kamfanin Rado,shi kanshi Tahir daya kai Dubanshi kanshi Acikin Madubi sai da ya Murmusa Aransa yasan Cewa Tabbas Shi mai Kyau ne Kuma ko Acikim Maza sai An Tona Uwa uba Kuma Baba Hakimi zaiji Dadin ganinsa yau Cikin Shigar Manyan kaya.

   Yana gyara Zaman Hulan kansa Wayarsa na Hannunsa yake Saukowa Daga Saman step Kamshin Turarensa na Man na Tashi Tun Kafin ya Kariso,Basma da Bassma da Mufeeda Wacce Ke goye Da Naila Bayan Ta bata Madaranta ta Sanyamata Wata Bulawus mai Kyau Tayi Shuru ta goyata Ram Abayanta Haka itama Tana Sanye da Riga Da Sikat na Atamfa Cikin Wanda Daddy,ya Dinkamusu Ita da Basma,sai Iya  dake Gefe Suna Zaune Bisa Wani Katon kayattacen Teburin cin Abinci mai Kama dana Alkarya guda,Dama Haka Akidar Gidan Tahir Yake ba'a nuna Bambamci da Bare Dana Gida Duk Daya Ake Kowa Dake gidan bayan Megadi da Direba Ne kadai basu Haduwa Suci Abinci Tare Farida Kuma Bata Damu ba,don bata Cikama Zama agidan ba balle Ra"ayin Tahir ya Dameta,Tun Iya da Mufeeda basu Saba ba Har Sunzo Sun Saba Domin Dukkanasu Sun Haura Shekara Biyu Agidan..

Tundaga Nesa Yaran Suka Zubamai ido Suna Kallonsa Harda Mufeeda Wacce Duk Sanda Taga Tahir sai Taji Ta Raina Duka mazan,Duniya domin yagama Cika Kowani Mizami da Zati,ga kyau ga Asali ga Nasaba da Kyan Hali Har misaltawa Takeyi Acikin Ranta Allah ya bata Miji irin Daddy Wanda ya Iya Daukan Wanka Da Gayu,Tunaninta ya KatseNe sanda Taji Su Bassam na Gaisheshi Amsawa yayi yana Shafa Kan Basma Yana Fadin"bbyna Kin Tashi Lafiya..?

Tana Hadiye Chips din Data Tura Abakinta Tace"Lafiya lau Daddy.,Allah Daddy Today u look so Fine kamar Dan Saurayi ko Bassam..?."Tafada Tana Dariya Gyada kai yayi yana Fadin"Eh mana Daddy.."Dariya yayi Fararen Hakoranshi Suka bayyana Yana Kallon ya"yan Nashi Cike da Jin Dadi ya Dago Kenan Karaf idonshi ya Fada Ana Mufeeda Data Shagala da Kallonsa Rage Fara"arsa yayi yana Fadin"Mufee,uwar Naila Har Tayi barci ne..?

NANNY(Mai Reno.)Место, где живут истории. Откройте их для себя