NANNY..!

2K 209 14
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Follow us on wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

    *BABI NA GOMA SHA BIYAR*

.....""Har kan Gadonta ya Zaunar da ita,Dagowa Tayi Tana kallonsa Da Jajayen Idanuwanta Tana Zubar da kwallah Cikin Siririyar Muryanta ta Furta"Kayi hakuri Daddy..."Tsam ya Tsaya yana kallonta gefe Daya na Zuciyarsa Tsausayinta na Ratsashi,Basma Dake gefe Tsaye ya kallah kafin yace"Ku kula da Ita sai na Dawo..'

Yafada Haka kafin ya kai ya Fice Daga Dakin da Sassarfa,basma Dake Tsaye ta Kariso Kusa da Ita Tana lallashinta Tahir yana Fita yaci karo da Iya Tsayawa yayi yana Fadin"Iya don Allah ki kula da Mufeeda..."Iya Ta gyada kai Tana Fadin"Insha Allahu Alhaji.."

   Sama ya haye Cikin Dakinsa ya Shiga Daga ganin yadda yake Komai Cikin Hanzari zaka Fahinci yana Cikin bacin Rai,Cikin Sauri ya Dauki Duka Fayels din ya Fito Garzali Dake Waje yana Jiransa ya Shiga Mota Suka koma Campany Wanda Tunda ya Dawo Ishaq ya lura kamar Ranshi abace yake ba Haka ya Fita ba bai mai mgana ba Sai da Suka Dawo Masallaci Sun Shigo Office Din Tahir din

Kan Wata Kujera Dake Cikin Office din Ishaq ya zauna yana Fadin"Kai inaga fa zan Koma gida cikina yana ta Kiran Ciroma.."Tahir Dake zaune kan Kujeran gaban Tuburansa Ya Dago yana Fadin"Allah Sarki kuda Kukayi Dace kenan Mu ko Mun koma muda banza Duk Daya While sai ka Dawo ni kila sai la"asar in zan Koma gida na Biya na Siya Fura ."

Ishaq ya gyara zama yana Fadin"Tahir meya Faru ne..? Dazu Bayan kaje gida Dauko Wadanan Fayels din ka Dawo Ranka bace.."Ajiyar Zuciyar Tahir ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Nida Farida ce Wato Ishaq Farida Muguwar Yar Rainin Hankali ce Ayadda nakeji yanzu kamar na kamata nayi ta Duka Gabadaya na Doramata kaso mai girma na Abunda ya Faru Domin Data Kiyaye Hakokina na aure da Duka Haka bata Faru ba.."Yafada yana Saka Duka Hannuwansa Ciki  Aljihun Wandonsa.

Ishaq yace"Me kuma ta Sakeyi..? Tahir ya waigo yana Fadin"Zuwa nayi na tarar da Ita zata kori Mufeeda Daga gidan.."Ido Ishaq ya zaro yana Fadin"Kabari don Allah...? Tahir ya kariso Kusa da Ishaq ya zauna yana Fadin"Wlh Allah ina gayamaka tana Kuka Wai Tana Fadin Ta Cuceta Ishaq can u juz imaging Wai Farida na Kuka saboda ni Tahir na Ma Mufeeda ciki.."Ishaq ya saki Dariya ahankali yace"Dama tana Sonka Tsabar Iskanci ne ke Cinta nayi Takaichin Abunda ya Faru Tahir Duk da bawa bai isa ya Gujema kaddaransa ammh Ta wani Fanni naji Dadi ko banza Lokaci yayi da Farida zata girbi Abunda ta Shuka.."

Tahir ya kuramai ido yana kallonsa kafin yace"Kamar yafa..? Bangane ba..? Tashi Ishaq yayi kafin ya Sakala Duka Hannuwansa Akirjinsa kafin ya Fuskanci Tahir yana Fadin"Eh mana Ai ada Tana ganin baka da Wani amfani Awajenta,Tana ganin ka Daga Ita sai kai yanzu kuwa Dole zata Shiga damuwa Domin Tana Sonka auren Soyayyah Kukayi bana Kiyayyah ba So Dole Farida tayi kuka Kishinka Take Tahir.."Shuru Tahir yayi kafin ya Jinjina kai yace"Hakane..,? Toh ai Ta makara Sai dai komai yagama lalacewa.."Ishaq yace"Shine ake Jiyemata Tun Farko Kada tayi Nadamar Dole Wacce bata da Wani Amfani.."

Mikewa Tahir yayi kafin yace"Wannan ya Rage nata Ishaq Abunda na sani Shine Matukar Farida tace zata matsama Mufeeda Wlh Itama zata Shiga mtsala na Fadamata in batason ganin Mufeedan agidan zata iya komawa gidansu ban Hanata ba ."Ishaq yace"Ina bayanka Wlh gwara ka Nuna mata Kuskuranta Tun yanzu.."

Tahir yace"Uhm,Kabari kawai Ishaq Zata ga ainihin kalata Wlh.."Ishaq yace"Asaussauta mata Alhaji Abarta taji Da Daya..Yafada yana yar Dariya Shima Tahir Dariyan yayi kafin yace"Yau da Safe Goggo Ta Kirani Tana Kuka Tana Fadamin Tunda Suka Dawo Baba Hakimi baya kulata nadai lallasheta nace Tabari Ranar sati zan Shigo D'anbatan,Duk da ina jin kunya Ishaq sai nake ganin kamar kowa yasan Abunda na aikata.."

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now