NANNY..!

2.3K 223 26
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

        *BABI NA TAKWAS*

*BAYAN SATI BIYU*

Zuwa wannan lokacin komai ya gama daidaita a tsakanin Tahir da Fareeda basu da matsalar komai yanzu, Fareeda ta natsu ta bar duk abun da take yi ta daina fita ko'ina kullum tana gida tana baiwa mijinta da 'ya'yanta kulawar data dace, wanda sauyin wannan hali nata ya yiwa kowa daɗi a cikinsu gidan ya zama cikakken gidan ma'aurata masu tsananin so da ƙaunar juna haɗe da tarairaya. Kullum cikin farin ciki da ɗoki 'ya'yanta suke, yanzu babu abunda ke damunsu saboda suna samun kulawar mahaifiyarsu kuma tana jansu a jikinta bata kyararsu komai suke so tana yi musu, Mufeeda da Iya suma abun yayi matuƙar yi musu daɗi gidan ya zama happy family babu damuwa ko matsalar komai a gabansu sai farin ciki.

Suna zaune dukansu a falo gidan suna kallo a makeken talabijin ɗin dake manne a bangon falon Naila na kan cinyar Mufeeda tana bata madararta yayinda Basma da Bassam ke gefe zaune a kan kafet suna yin Homework ɗinsu kasancewar gobe Monday akwai makaranta Iya ta fito daga ɗakinta da sauri tana share hawayen dake zubo mata ta nufo Tahir ɗa Fareeda dake zaune a saman kujera suna magana ƙasa ƙasa wanda su kaɗai suka san abinda suke faɗawa junansu dan babu mai jinsu ta ɗan rusuna a gaban Tahir tana goge ƙwallah tace "Sannunku da hutawa Alhaji." A hankali Tahir ya ɗago da kansa yana kallonta kafin ya gyara zama sosai yace "Yauwa Iya sannu da fitowa... amma lafiya kuwa na ganki haka?"

Tana ƙara duƙar da kai tace "Yanzu ne aka yo min waya daga can gida Allah ya yiwa Yayana Malam Danladi rasuwa..." Ta ƙarashe maganar ƙwallah na ziraro mata ta kwanto haɓar zaninta ta share wasu na ƙara zubo mata, salati Tahir da Fareeda suka yi yayinda Fareeda ta miƙe ta kamo Iya ta miƙar da ita tsaye tana kallonta tace "Sannu Iya, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Allah yasa ya huta." Da Ameen ita da Tahir suka amsa kafin ya tashi tsaye shima yayi mata gaisuwa cike da alhini kana ya fice waje ya kira Garzali yace ya shirya ya fito da mota zai kai Iya Kano ba ɓata lokaci ya dawo ciki yace da Iya taje ta shirya su wuce Garzali ya kaita, sannan ya haura sama zuwa ɗakinsa ya ɗebo kuɗi masu yawa yazo ya bata ta duƙa tasa hannu biyu ta amsa tana masa godiya ta koma ɗakinta ta ɗauko 'yar jakar gana most go ɗinta ta fito Mufeeda dasu Basma da Bassam harma da Fareeda suka rakata har bakin mota ta shiga Garzali yaja suka fice daga gidan, su kuma suka koma cikin gida cike da kewarta da tayata alhinin rasa ɗan'uwanta da tayi.

Washegari da sassafe wayar Umman Fareeda ta tashesu daga barcinsu mai daɗi da sukeyi rungume da juna, da magagi ta lalubo wayar ta ɗauka ta kara a kunnenta nan take faɗa mata Abbanta ba lafiya ciwon sugansa ya tashi an kwantar dashi a asibiti. A gigice ta tashi ta sauka daga gadon tana tashin Tahir shima ya tashi ta faɗa masa abunda Ummanta tace cikin tashin hankali tashi zaune ya ziro ƙafafuwansa ƙasa ya sauka daga gadon ya riƙe hannunta suka shiga toilet agurguje sukayo wanka suka fito suka shirya Fareeda ta ɗebi kayanta kala biyu ta zuba a ƙaramar jakarta suka fice zuwa falo.

Ɗakin Mufeeda ta nufa ta samu har tayi wanka ta yiwa Naila itama tana shiryata ta shiga ta ɗauki Naila tace Mufeeda ta ɗauko hijabinta ta fito, da mamaki Mufeeda ta ɗauki hijabinta ta saka ta biyo bayanta suna fitowa falo taga Basma da Bassam a shirye cikin kayan gida saɓanin na makaranta da tayi tsammanin zata gansu dashi, duƙawa tayi zata gaida Tahir dake tsaye yana kallonta, ɗaga mata hannu yayi yana faɗin "Lafiya Alhamdulillahi Mufeeda... Ku muje lokaci na ƙurewa." Ya ƙarasa faɗa yana karɓar Naila dake hannun Fareeda ya saɓata a kafaɗarsa ya fice suna biye dashi a baya. Garzali na ganinsu ya taso da sauri ya nufosu ya buɗe masa mota ya shiga gaba ya zauna sannan ya buɗewa Fareeda ta shiga baya Mufeeda ta shiga kusa da ita ta zauna sannan Basma da Bassam suma suka shiga ya rufe ya zagaya da sauri ya shiga ya tada motar maigadi ya buɗe musu gate suka fice sai daya hau titi sannan Tahir ya faɗa masa inda suka nufa, nan ya taka mota suka ɗauki hanyar Kano.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now