NANNY...!

2.1K 195 13
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_Don't Forget to Vote us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA BAKWAI*

....Duk da yaran Sun Tashi Zuciyarsu ba Dadi bai Hanasu Shirin Tafiya mkaaranta ba,Suna bisa Dinning Suna Breafsat,Kowa ka gani Fuska ba Walwala Don Daga Tahir din Har Faridan ba Wanda Sukaji Motsinsa Har Gwarashi yazo da Asuba ya Tashi Bassam sun Tafi masallaci.

Batare da Sun saka iyayen nasu a ido ba garzali ya Kwashesu Zuwa Mkranta Naila Kuma dama Wajen Tahir Ta Kwana,Sun Fita ba Dadewa Farida ta fito Daga Cikin Bedroom Dinta Dauke da karamar Trolly dinta Fuskarta ta Kumbura Idanuwanta Sun Chanza kala Saboda Kuka Tana Sanye da Riga da Sikat na Wata Atamfa Holland,Daurin Dankwalin dai gashi ga kamarshi,sai karamin Gyale Vail Data Yafo Bisa kafadarta,karamar Jakarta na Hannunta Hade da Wayarta sai Key din motarta Dake Hannunta.

    Ahaka ta Sauko Har Zuwa Main Falo din Tana Tafiya tana Share Hanci da Iya taci karo Wacce Tafito Daga Kichen,cikin mamaki Take kallonta kafin Tace"Hajiya lafiya Kuwa..? Wata Uwar Harara Ta maka mata kafin Ta Saki Tsaki takama Hanyar Fita Daga Falon,iya bata Dandara ba Tace"Haba Hajiya gaskiya Wannnan ba girmanki bane,Ina Zaki Tafi ki bar mijinki da ya"yanki Kefa ba yarinya bace Yaji bai kamace ki ba,kin kai Munzalin Da Zaki ma Wata Fada bama Kanki ba..."Tafada Cikin Nuna Alamun Abun bai mata Dadi ba.

Juyowa Farida Tayi Afusace kafin Tace"Wlh iya sai na Tafi nagaji da Irin Tozartanin Da Tahir yake yi nagaji..!kina gani Jiya gabanku gaban ya"yana Ya Tsinkeni da maruka har biyu Saboda ga baiwarsa ko,Allah sai na Tafi Sai ya Zauna Shi kadai.."Tafada Tana Sharbe Kwallah kamar Wata yarinya.

Iya tayi kasake kafin Tace"Hakuri Ake Hajiya,Kowa fa kikagani yana Zama lafiya agidan Mijinshi karki Tambayeshi Hakuri,Kema Kiyi Hakuri Don Allah In kika Tafi Gida Kicema su Umma Mene Don Allah.."?Tana Sharan Ido Tace"Ai ba Kano Zani ba Danbatta zani Wajen Goggo Abu taga Shaidan Yatsun Tahir Akan Fuskata..."Tafada Tana juyawa da Sauri Ta Fice Daga Falon Tana kara Rike zaman karamin Akwatin Dake Hannunta Iya Dake Tsaye ta Yunkura Zata Bita sai Taji Muryan Tahir Daga Sama yana Fadin"kyaleta iya..."yafada Cikin Halin ko Inkula

Iya ta Waigo Jiki asanyaye kafin Ta Rusuna Tana gaisheshi,Shiko yana Daga saman Benen ya amsa mata Fuskarsa na Nuna Alamun baida Damuwa yana Sanye da Amarican Suit,Ash colour,Yar jakar Briefcase dinsa ne Ahannunshi da alamun Fita Zaiyi Tana Kokarin Barin Falon ya Karisa Saukowa yana Fadin"Naila tana Room Dina iya Ta Koma barci plz ki Haura ki Daukota Ta Zauna Kusa dake.."Ya Fada yanq Nufar hanyar da Zai Sadashi da Haraban Gidan Lokaci Daya yana kallon Agogon Fatan Dake Hannunshi.

Iya tabi bayanshi da kallon Tsausayi kafin Tace"Insha Allahu Adawo lafiya Alhaji.."Bai Jita ba Don ya Riga yaFita Daidai Lokacin Kuma Garzali ya Sawo kan Motar Cikin gidan ya Dawo Daga kai Su Basma mkranta batare da bata Lokaci ba ya Shiga ya Juya Dashi Zuwa Office don Ya Makara gashi Kuma Meeting garesu Suna Tafe yana kallon Agogon Dake Tsitsiyan Hanmunshi kafin Wayarsa kirar iphone 11 promo,tadauki Tsuwa Sunan Ishaq ya Fito baro baro Afuskar Wayar Dauka yayi Da Hanzari suka gaisa kafin Su Cigaba da mgana Cikin Kulawa da Tsantsan Ilimi.

********

*D'ANBATTA*

Goggo Abu Sai Dai Taga Farida Kwatsam Tazo Tana Mata Kuka Wiwi kamar Wacce Aka yanka Ko Akace Uwarta ta Mutu Lokacin Data Iso Ashe na gidan,nan Goggo Abu Ta Rude Ta Shiga Tambayanta Abun ya Faru,Farida na Kuka tana Zayyanama Goggo Wai Tahir ya mareta Har guda hudu Dukkanta ma yaso yi sai da iya mai aikinsu Ta Shiga Tsakani Farida na Kuka Tanama Goggo Abu Rantsen Rantsen Cewa Tahir yace ma bata da Wani Amfani Acikin Rayuwarshi.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now