NANNY...!

2.3K 186 10
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA HUDU*

  *MALLAM BELLO GURGUN D"ANBATTA* sunan Mahaifin Mufeeda Wanda Shima ya kasance Haifaffan garin na Danbatta ne gaba Da Baya Hakama matarsa Inna Fulera Itama Haihuwan nan Kuma Tashin nan.

Sai dai kuma Tun Asali Dukkansu biyun Sun Fito Daga Tsatson Talakawa ne,futuk marasa karfi Kuma Dama Auren Zumunci ne Tsakanin Bello da Fulera,Bayan Haka Kuma Dangin Nasu basu da yawa Saura Sun Mutu Saura kuma Sun lula garuruwa Neman kudi.

Bello gurgun Danbatta ya samo Asali ne da Tun yana yaro Ciwon Daji yakamashi Ahannu Wanda yayi Sanadiyar Cire mai Hannu guda Daya Shikenan In za"a Kirasa Sai Adingamai in kiya da Bello gurgun Danbatta,Daga Mallam bello Har Inna Fulera Duka Sun Rasa Iyayensu So Suna Zaune Awani Kuntattacen gidan kasa Cikin Wahalar Rayuwa Dukkansu babu Wanda Yayi ilimin boko sai na Allo Shima din Sama sama Don Lokacin bawai Sanin Darajan Abun Sukayi ba,balle Su Damu Dashi Baida Wata Sana"a Sai Sana"ar Noma kayan lambu kamarsi Tumatur dasu Cabeji da Su Albasa,yana Shiga cikin gari yana Siyarwa Da Hannu nasa Guda Har Su Samu Su Rufama kansu Asiri

Sun Shekara kusan goma da Aure Kafin Allah yabasu Mufeeda wanda bayan Ita Ta Haifi yan biyu Duka maza basu zo Da Rai ba Daga Lokacin Kuma Haihu ta Tsayama Inna Fulera sai Suka Cigaba da Rainon Mufeeda Wacce Suka Dauki Son Duniya Suka Doramata Saboda Ita kadai Garesu Itace yarsu kuma Ahalinsu,Kuma abokiyar Hirarsu Shiyasa Itama Mufeeda Tataso Cikn So da Kaunar Duka Iyayen Nata Guda Biyu,duk da Tazo ta iskesu Cikin Wahalan Rayuwa ammh Suna iya bakin Kokarinsu Akanta don Ita Kanta Inna Fulera bata Zauna ba Tana Saida Dafaffen Kabejin Acikin gida Ana Zuwa Siya ba laifi Tunda Tana da   Tsabta...

Haka suka Cigaba da Gangara Rayuwarsu Da Dadi ko Ba Dadi Har Lokacin Da Mufeeda keda Shekara goma Sha Uku Aduniya Ta Girma Duk Wasu Alamun budurci basu bayyanar mata Sakamakon Siririyace Ita bata da Jiki Sosai,kwatsam Suka Tashi da Wani Rashi,Rashi mai girma Wanda Har yau Suka kasa mantawa Dashi Na Rasuwar Bello Gurgu Sanadiyar Fadawa Rafi Ruwa ya Cinyesa Inna Fulera da Mufeeda Sunyi Kuka kamar Ransu Zai Fita,duk da Alokacin Mufeedan Nada karancin Shekaru ammh Wannan Rashin Da Sukayi ya Tsaya mata Sosai Acikin Ranta

Ko Takaba Inna Fulera bata Fita ba Suka Fara Shiga Wahalan Rayuwa Na babu sai Su Kwana basu Ci Abun na Damunta Duba da karancin Shekarun Ita Mufeedan Shiya sanya Tana gama Tagama lbrin Neman Ma"aikata Daga gidan Hakimi ya Sameta Inda Tahir yabada Cigiyar Neman Wadanda Zasu Dingama ma Iyayensa Hidima yana Biyansu duk Wata Inna Fulera batayi kasa Agwiwa ba Ta Isa Gidan Hakimi gaban Goggo Abu Sai dai koda Taje An Riga Angama Daukan Adadin Ma"aikatan,nan Inna Fulera Ta Fadi gaban Goggo Abu Tana Kuka Tana Rokonta Data Rufamata Asiri Ta Taimaki Rayuwarta Data Marainiyar Allah Mufeeda Toh Alokacin Sai Tsausayin Karancin Shekarun Mufeeda ya Darsu Acikin Rayuwar Goggo Abu Har yayi Sanadiyar Data Dauki Inna Fulera Amatsayin Hidimarta Ammh In Tagama Da Shashenta takan Shiga Madafi Ta Taimaka duk Wata 15k Tahir ke biyansu Dukkansu Wanda Cikin lokaci Kadan Ya Taimaki Rayuwar Mutane Dadama Ciki Harda Inna Fulera,wanda Cikin Haka ne Ta Sanya Mufeeda A makrantar primary Danbatta Tana Zuwa Indan Tataso sai ta Biyo Gidan Hakimi Wajen Innarta Taci Abinci Ta Koshi Ba Shashen Datake Zuwa Sai Shashen Goggo Abu Ta Zauna Tayi Shuru Dayake bata da yawan mgana Wani Lokacin In Goggo Abu Ta Ganta sai Tahir ya Fado mata Acikin Ranta Tana Tunanin Shigen Miskilancinsa Ammh In Ta Kalli yanayin Mufeeda sai Taga ta Shanyeshi Haka Kurum Takejin Tsausayin Yarinyar Shiyasa Take Janta Ajiki Sosai.

Mufeeda Bata da Wata kawa agarin Sai lantana Wacce makotansu ne Itama mamarta Tana Aiki Agidan Hakimi Ita kadai Ce Kawarta Kuma Gashi Mkrantarsu Daya Kuma Ajinsu Daya,shiyasa sai Tasu Tazo Daya Kuma In Sun Tashi Daga Mkranta Tare Suke Wutowa gidan Hakimi Wajen iyayensu,Mufeeda bata da Saurayi kamar na Sauran yanmatan kauye ko nace baata bi Ta kansu Kwata kwata Saboda Ita bata Son Auren Wurin Da"ake musu Mutum Daya ne Take Kulawa Shima sai ya Dameta Iliya mai Rake,Tun Tana karamarta yake Bibiyarta Abokin Saurayin Da Lantana Zata Aura ne Murtala Shiyasa Wani Lokacin in Su biyo hanyar Mkrantar Allo In Murtala yaja Lantana gefe Itama sai iliya yajata Duk dai bata Sakarmai Fuska Bai damu ba Inda Saboda yaci Ace ya Saba da yanayin Rayuwar Mufeeda.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now