NANNY...!

2K 206 5
                                    

*NANNY...!*
     (Mai Reno..)

*Alƙaluman:✍🏻*

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR (Janafty*💕

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI*💔
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM*💘

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

        *BABI NA BIYAR*

Ƙarfe 3:30pm. Suka shigo garin Kaduna direct suka nufi Unguwar Rimi GRA suna zuwa maigadi ya buɗe tangamemen gate ɗin gidan direba ya sulala motar ciki ya yi parking ya fito da sauri ya buɗewa Farida ta ziro ƙafafuwanta waje sannan ta fito riƙe da wayarta da ƙaramar jaka a hannunta ta buɗe jakar ta ɗebo kuɗi ta miƙa masa "Gashi kaje tasha ka shiga motar haya ka koma gida. Allah ya tsare." Cike da ladabi ya karɓa yana mata godiya, hannu kawai ta ɗaga masa ta juya ta ɗauki ɗan ƙaramin akwatinta ta shige cikin gidan, direban ya juya shima ya fice daga gidan.

Falon tsit yake babu kowa a ciki da alamu yara basu riga sun dawo daga makaranta ba, a gajiye take dan haka bata bi takan komai ba ta nufi ɗakinta, tana gab da shiga ɗakinta ta tsinkayo muryar Iya cike da murna tana faɗin "Sannu da zuwa Hajiya, ashe kece? Ina kichin zan haɗawa Naila madararta na jiyo motsin shigowa..sannu da dawowa." Iya ta faɗa fuskarta cike da fara'a tana tahowa inda Farida take tsaye da Naila riƙe a hannunta tana murmushi.
Murmushin itama Faridan tayi ta aje ɗan akwatin hannunta ta miƙa hannu ta karɓi Naila ta ɗagata sama ta sumbaci goshinta ta shafa kanta sannan ta miƙawa Iya ita ta ɗauki akwatinta tace "Sannunku da gida Iya." Ta faɗa kawai tare da shigewa ɗakinta, turus iya ta tsaya tana bin bayanta da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta juya ta koma kichin dan cigaba da abinda take yi, dan in dai halin Farida ne na nuna halin ko in kula da 'ya'yanta da duk wani abun daya shafi gidan aurenta yaci ace zuwa yanzu duk sun saba dashi, bai kamata a kullum ya zama wani sabon abu ko baƙon abu a gurinsu ba.
Kwana da kwanaki bata gida bata tare da 'ya'yanta da mijinta ga yarinya ƙarama mai shan nono wacce ko yayeta bata yi ba amma ta dawo ko ta tsaya ta tambayi yanda suke balle ta ji ina suke da bata samesu a gida ba, gashi ko ƙaramar 'yarta mai shan nonon ma bata wani damu da ita ba ko ta nuna kulawarta a kanta ba, shiyasa itama 'yar ko murna da ganin uwar tata bata yi ba sai kallonta kawai da take kamar wata baƙuwa.

Tana shiga bedroom ɗinta ta zube wayarta da jakarta ta tuɓe kayan jikinta ta jawo tawul ta ɗaura ta faɗa toilet, bata wani daɗe sosai ba ta watsa ruwa ta fito ta faɗa gado tai kwanciyarta abinta saboda wani irin bacci take ji duk ta gaji jikinta sai ciwo yake mata.

Ƙarfe 4pm. Bassam da Basma suka dawo daga makaranta, suna shigowa suka tarda Iya na bawa Naila madara a falo a gajiye duk suka zube saman kujera suna maida numfashi, Iya ta ɗago tana kallonsu da murmushi akan fuskarta tace "Sannunku da dawowa ya makarantan?" Basma na turo baki tace "Ba daɗi Iya, yau munsha wuya ga rana ga zafi." Dariya Iya tayi tana kallonta tace "To Mummy dai ta dawo..." Da murna duk suka miƙe suka kwasa da gudu suka nufi ɗakinta tana kwance suka shigo cike da farin cikin ganin mahaifiyarsu suka faɗa kanta da gudu suna murna suke faɗin "Oyoyo Mummy..!"
haɗe rai tayi ta yatsine fuskarta ta tashi zaune haɗe da janyesu a jikinta ta ɗaure fuska tace "Please kuje waje ina so zan huta ne, idan na tashi zan nemeku.." ta faɗa tare da janye hannunta ana Basma tana nuna musu ƙofar fita, a sanyaye yaran ke kallonta kafin su juya a hankali suka fice daga ɗakin suna waigenta, ƙaramin tsaki taja ba tare da tunanin komai ba ta gyara kwanciyarta abinta ta lumshe idonta tana jira bacci ya ɗauketa.

Yanda Iya taga sun fito daga ɗakin jikinsu a sanyaye yasa ta miƙe da Naila dake bacci a hannunta ta nufesu ta kamo hannun Basma tana ɗan murmushi tace "Kuje ku cire kayan makarantan kuyi wanka sai ku fito ku ci abinci, kafin nan Mufeeda ta dawo itama sai ku shirya ku wuce islamiyya.." gyaɗa mata kai suka yi kafin kowa ya nufi ɗakinsa, itama ta juya ta nufi ɗakin Mufeeda ta kwantar da Naila ta fito.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now