NANNY...!

2K 232 17
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA*

Ranar barci ko barawo bai Sace Tahir ba,kuka kuwa yayishi kamar Ranshi Zai Fita Daga karshe ya Hakura ya Fauwalama Allah komai ya kuma Daukeshi A Matsayin Kaddaranshi,Ammh yasan Duk Abunda ya Faru Dashi Farida ce Sila kana goggo Abu Da'ace Sunyi Duba da Lalurarsa da Irin Hallittarsa,Da Duk Haka Bata Faru ba Ammh yana Ta Neman gafaran Allah,sai dai Kunya da Nauyi Sun Cikamai Kirji Sun Hanashi Sukuni

Shi yazo yatashi Bassam Suka Tafi masallaci Sallar Asuba basu Dawo ba sai Wajen Bakwai Saura Koda suka Shigo iya ta gyara Ko"ina Tana Kichen Tana Musu Abun Karyawa Bedroom dinsa ya Zauna Kawai ya Zabga Tagumin Makomar Rayuwarsa yadda ya Cucu Rayuwar Yarinya kamar Mufeeda.

Su iya ko tana gama Abun karyawa Ta Dorama Mufeeda Abunda Zatasu Tafin mata Dashi Asibiti Tunda Tahir yace in Sun karya Garzali zai Tafi Dasu,Shiko yana Cikin Daki yama kasa Fitowa Bawai bayajin Yunwa bane A"a yanaji Domin Rabonshi da Abinci Tun Jiya da Dara,Ammh Cikinsa ne A Chuse bayajin Akwai Abunda Zai samu Wajen Zama ga bakinsa ba Text Kwata kwata Daci daci ma yakeji Shikanshi Damuwa ta Saukarmai Da Zazzabi mai Zafi kan gado ya Kwanta ya Lulluba da bargo Haka basma da bassam Suka zo Suka iskeshi ya Dunkule yana Hawaye,yanajin Muryansu Suna Kiranshi yayi Saurin Share Kwallah ya Fito da kanshi yana Kokarin Daidaita kansa

   Basma ce Ta karisa Tana Zama Gefen gadon Lokaci Daya Take fadin"Daddy jikin ne...? Tafada Cike da Tsausaya Kai ya girgiza musu kafin yace"No ba sosai bane Basma,nasha mgani da nayi barci zan Warware,kun Shirya ne...?"Bassam ne ya Dagamai kai yana Zama Shima gefen basma Fuskarshi ta bayyana Damuwar Dayake Ciki,Cikin Raunin Murya ya Furta..."Daddy What Wrong Wit u ne,bama jin Dadin Ganinka Ahaka in Mommy bata sonka Why not ka samomana Wata Second mom ko Basma..."? Yafada yana kallonta,Saurin Kuka ne da Ita sai ga Hawaye Shar da gyada kai tana Fadin"Eh mana Daddy,mommy tana Barinka kana Wahala bamai kula dakai ka karo Aure plz kasamu Wacce Zata Dinga Zama dakai kullum muma Mu samu Mommy Wacce Zataso mu sosai Fiye da mommy.."Tafada Kuka na Kwaceta mata ta Kifa kanta Jikin Tahir tanayi,Hannu ya saka yana Shafa kanta Dake Cikin Hijabin yanajin Kaunar ya"yansa Har Cikin Ranshi Duk da kananan Shekarunsu Sun Fahimci Damuwar naashi Acikin Ranshi Fadi yake dama dama ace bai Aikata da Abunda ya Aikata ba,Ammh yanzu da Wani ido Zai kalli ya'yansa yace Shine ya Ketama Mufeeda Mutumci.

  Cikin Sigan Lallashi yake Fadin"Shiii..Is ok karku damu Kunji na samu Sauki Sosai Ku Tashi Ku Tafi garzali zai kaiku Room9 Take kunji.."Gayda kai Basma Tayi kafin Ta mike Tana Share Kwallah Hannunta bassam ya Riko Kafin su Duka Dukkansu Su Sakarma Tahir kiss Goshi Lumshe ido yayi Idanuwansa Sun Cika da Kwallah Cikin Raunin Murya yace"Take care..."Suka Fice Suna Dagamai Hannu Suna Fita Wani Kuka yazo mai ya Shige Cikin Bargo yanayi kamar ya Shide Saboda Takaichi So yake ya Bude Ido yaga Duk Abunda ya Faru mafarki ne Ammh Ina bakin Alkami ya Riga Daya bushe,Abunda yasa Ma ya bari su iya suka Tafi Asibitin bashi da mafita ne don ya cigaba da Hanasu Zuwa Zasu Zargi Wani Abu,shiyasa yakira Dr Hadiza da Safen nan,dayake sun karbi Nimbar Juna,ya Roketa Akan Don Allah mahaifiyar Mufeeda Zatazo Dubata koda Wasa Kada Ta mata Narrated din Abunda ya Faru da Mufeeda baya son Hankalinta yatashi Sai daga baya zai sanar da ita,jin Haka yasa Dr Hadiza ta Amince da Rokonsa suka Rabu Akan sai Anjuma zai Shigo Asibitin.

Su Basma Sun Iske Jikin Mufeeda da Sauki Tana ta Baeci ga Nurses nata kula da Ita sai Wajen 1 ta Farka taji Dadin ganinsu iya dasu basma Tadinga Mirmishi,Ta daina Kukan yanzu,Tunda Tafara jin Sauko Gasata Suke bana Wasa ba ga mgaunguna gashi tana samun Hutu Dr Hadiza Da Tazo da Safe Haka ta Dinga Tambyar Mufeeda ko Zata Tuna Fuskar Wanda yayi mata Wannan Aiki Ko Zata Taimakesu Su Nemarmata Hakki,Acikin Ranta Kuka Take Har Asarari,Saboda Bazata iya Bude baki ta Furta Wanda ya Inganta Rayuwarta ne ya Aikata mata haka Bazata iya karya Alkawarin datayima Daddy ba Koza"a Kasheta Akaro na Farko Zata sakamai da Abunda yayi mata Arayuwa,Tana kuka take Cemata bata sani ba Dole ta kyaleta.
.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now