45

1.1K 62 3
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*SIS FAUZY YAR AMANA Y'AR AMANAN KAINUWA*
    *wannan page din naki ne kiyi yanda kika so dashi*

PAGE 45


*LAST PAGE*


Khairat gida ta koma rai a bace, tana shiga taga Mahmud da rahma a falo, wanda yasa dole ta saki fuska, dan karsu fahimci halinda take ciki, rahma taga shigowanta tace a'ah yana ganki yanzu Nasan lokacin tashi baiyi ba, khairat tace rahma na ajiye aiki, rahma tace mene? Khairat tace eh na gaji gwara in huta, rahma zata kuma magana khairat tayi sauri ta rigata tare da gaida Mahmud tace saukan yaushe? Yace dazu nazo dan inga gimbiyar, dariya khairat tayi tace oh I can't wait to see your weeding, alh Mahmud murmushi yayi cikin jin dad'i domin shidai bashi da burin daya wuce ya auri rahma, Khairat shiga ciki tayi inda ta fad'ama y'an uwanta tabar aiki tare da fad'a musu dalili koda rahma tazo itama Sun fad'a mata ransu ya baci Sosai sukace gwara ma data bari.



Iyalan marigayi alh Ibrahim ne zaune suna cin abincin dare akan dinning, suka ji karan nocking, khairat ce ta tashi danta bude kofar Tana bud'ewa ta zare ido domin ganin oganta Muktar, cikin mamaki ko magana ta kasa, rahma jinta shuru yasa taje itama, tace sannu shigo, shigowa yayi tare da kallon khairat yace Wajanki nazo, sannan ya karasa cikin falon, inda yagaida su Ummi, suka amsa cikin fara'a dan basu San ko Waye ba, yace nine ogan khairat, nazo in bata hakuri akan abunda ya faru, khairat kallon mamaki take mai, yace dan Allah Ina neman izinin magana da ita, ummi tace babu damuwa tashi khairat tayi yabi bayanta har zuwa falon ba'ki, zama yayi akan kujera sannan ya kalli khairat yace nazo in baki hakuri akan abunda ya faru, dazu sanda nazo Ina miki fad'a mum dina tazo office din duk taji abunda Nayi miki ranta ya baci Sosai dan Allah kiyi hakuri, tace babu komai sir, murmushi yayi tare da fad'in Banyi signing a takardan barinki aiki ba dan haka saiki dawo aikin ki, tace kayi hakuri sir bazan dawo aiki ba domin na riga Na yanke hukunci, yace baki hakura ba kenan? Tace koh d'aya na hakura, murmushi yayi tare da fad'in Indai kin hakura Toh ki koma aiki, tace sir am so sorry bazan iya komawa aiki ba, dan shuru yayi sannan yace koda na aureki? Da sauri ta kalleshi ya d'aga mata kai alaman eh dagaske nake, tace sir.....  Yace Nasan Kin taba ganina da hauwa dan shuru yayi can yace ko wace mace dole tayi zargin wani abu, hauwa ita naso na aura amma tunda tamin wannan abun na fasa danna gane bata da kamun kai, khairat gaba d'aya ta yarda da abunda ya fad'a mata tun daka ranan suka fara soyayya har manya suka shiga wanda za'a had'a bikinsu su uku, Zainab rahma, khairat, sai hidiman biki akeyi. Faruk ne zaune yana cin abinci cikin wani gidan cin abinci sai yaga Muktar shida wata suna magana yana ta bayansu ne shi yana ganinsu amma su basa ganinsa, yaji yana fad'in ma yarinyar kiyi hakuri hauwa zan auri yarinyar nan ne saboda wani dalili, hauwa tace miye dalilin,? Labarin abunda khairat tayi mai yayi yaci gaba da fad'in saina wulakanta ta na mayar da ita abun tausayi, Idan na rama abunda tamin saina saketa in shawo kan mum muyi aure, faruk cikin Tashin hankali ya fita daka wajan rasa abunyi yayi can ya dawo ya daukesu hoto shida yarinyar sannan ya fita, Muktar yazo wajan khairat suna zaune a falo harda su Ummi domin a kullum yazo sai ya shigo ya gaidasu Kafin su tashi suje falon ba'ki, faruk ne ya shigo ya kalli muktar yace asirinki yau zai taunu, munafuki Allah bazai baka Nasaran auran yayata ba, zarah ta tashi ta wanka Mai Mari tace karka manta kaiba kowa bane a gidan nan, harka sami bakin fad'ama Wanda zai zama siriki a nan gidan magana, yace zarah abunda zan fad'a yanzu saiya baku mamaki Labarin abunda ya faru ya basu tare da nuna musu hoto, zarah ta kalli muktar tace wannan fah, muktar yace itace da zan aura rabona da ganinta wajan wata biyu kenan, khairat amsan hotan tayi sannan ta kalli faruk tace Kai Waye? Mai yasa kke son batamin aure? Na ro'keka ka fita daka harkan mu, bazamu kara yarda dakai ba dan kaci amanan mu, faruk cikin kuka yace khairat Dan Allah ki yarda da abunda zan fad'a miki Wlh wannan mutumin cutanki zaiyi marinshi zarah ta karayi tare da fad'in bar nan, Amina ce taja hannun faruk sukai sama, zarah bama muktar hakuri sukayi, yace babu komai,  koda faruk da Amina suka haura Amina tace faruk na yarda da abunda ka fad'a Nasan gaskiya ka fad'a amma ina ro'kan ka karka kara magana akan komai zai faru, tunda basu yarda dakai ba,yace Nayi miki alkawari mum.



You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 30, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now