12

719 65 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*SA'ADATU ALKALI TSAFE MY LOVELY DAUGHTER😍 WANNAN PAGE DIN NAKI NE KIYI YANDA KIKA SO DASHI*

PAGE 12





Bude takardan tayi taga rubuta kaman haka.....  *_my love nayi rubuta Kala biyu na farko Idan kin amince dani shi zan baki wanda gashi yanzu kina karantawa, ina sonki dagaske bada wasa ba ban taba jin son wata mace ba kaman ki, Nima Ina fatan zaki soni kaman haka, koda ban sami haka ba a dan nema min waje cikin zuciyarki koda kad'an ne, I really love you Ki kulan min da kanki_*
ido ta lumshe tana wani jin dadi lallai ta sami irin namijin da take buri a rayuwa, jin karan ana buga mata kofa yasa ta tashi da sauri ta boye letter din sannan ta bude kofar su khairat ne suka shigo, khairat ta Fara ciro kayan dake cikin ledan, su chocolate ne dasu biscuits masu tsada sai turaruka masu dadin kamshi, zarah ce ta dauki chocolate daya ta bude takai wajan bakin aysha da sauri ta kawar dakai tare da rufe fuska tana dariya, ummi ce ta shigo ta samesu suna ta dariya tace miye kuka wani sata a gaba?
Dariya suka kuma yi zarah tace ummi ki fadama Abba tace bata sonshi, da sauri aysha tace ni nace miki haka? Jin ummi tayi dariya yasa ta tuna tana d'akin da sauri ta tashi ta fita suko in banda dariya babu abunda suke, ummi fita tayi ta sami Alh Ibrahim a falo dasu mama, Bayan ta zauna yace ya kinyi mata magana?  Ummi tace eh ta amince, Abba yace Toh Alhmdlh Allah ya tabbatar mana da alkhairi suka amsa da Ameen, Amina ce ta fito domin tunda akayi magana akan saleh bata fito ba sai yanzu, kallo daya zaka mata ka gane tana cikin damuwa, Alh Ibrahim yace amina baki da lafiya ne? Tace lafiya na 'Kalau, zama tayi tana d'an shan kamshi hindu tace Amina kin fadama saleh sa'kon kuwa?  Wani irin kallo ta wurgama hindu sannan tace eh.



Zainab da aysha ne cikin shiri zasu raka khairat ganin Dr domin glass dinta Ya fadi ya d'an tsage gashi guda d'aya gareta, Bayan sun gama shiri suka fita kama khairat din sukayi har mota, driver yaja suka nufi hspt din, Bayan driver ya faka motar suka kamo khairat din suka fito domin in bata sa glass din ba dishi dishi take gani, suna cikin tafiya wayan zainab yayi kara dauka tayi tare da fadin aysha kuje zan amsa waya, dauka tayi tare da fadin zarah ya akayi? Zarah tace Kun Kai taga Dr din?  Zainab tace eh yanzu suka shiga ita da aysha, zarah tace OK sai kun dawo, kashe wayan zainab tayi d'ago kan da zatayi suka had'a ido da yazeed gabanta taji yana dukan uku uku, matsowa yayi kusa da ita tare da fadin mun sake haduwa ko baki fad'a ba nasan kina so na, kasa magana tayi sai kallonshi da takeyi ta gefen ido, yazeed yakai namijin da duk wata mace zata soshi ...... Katseta yayi da fadin kin gudu daka kano kin dawo nan gashi mun hadu, zainab plz ki bani lokacinki, cikin rawar murya tace taya akayi kasan sunana?  Yace Aiba Abun mamaki bane dan Nasan sunanki kin, zainab tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, dan Allah ki bani dama,.......  Jin maganan su aysha sukayi suna fadin sannu, yazeed yace sis yakike har kun dawo ashe? Aysha tace eh Wlh, yace gani ga mutuniyar inata ro'kan a bani dama inzo Gida, khairat da aka bata sabon glass tasa da kuma wani extra, ta Fara mishi kwatance yace a'ah gidan Alh Ibrahim?  Khairat tace eh yace muna kusa ma ashe, kallon zainab yayi yace sai kin ganni, yayi masu khairat sallama ya wuce, sun fito zasu tafi zainab ta hango mutumin daya ma yasmin magana rannan da sauri ta bishi tana son ta isa gareshi, waigowa yayi yaga zainab wanda ya ganeta sarai ganin shi take nufowa yasa yayi saurin tsaida mashin yahau, mota ta koma da sauri tare da cema su khairat su shiga da sauri, Bayan sun shiga tace driver yabi mai machine din can, aysha tace zainab Waye ne shi?  Zainab tace shine wanda yama yasmin magana rannan, zainab tace driver kayi sauri mana, mutumin ganin suna bin shi yace ma mai machine subi ta wani lungu Wanda mota bata shiga hakan ko sukayi suka bace musu, tsaki zainab taja haka dole suka koma Gida, koda suka koma sun fadama zarah abunda Ya faru tace subi a hankali koma miye zasu gano bada dadewa ba.




Magabatan yazeed sun zo neman auren zainab Alh Ibrahim yayi na'am, koda yasa ummi ta tambayeta ta amince Dan haka aka saka rana ita da aysha za'a had'a bikin amma Alh Ibrahim saida yayi maganan a gidansa su yazeed zasu zauna, yace babu damuwa duk da bawai yana so bane Amma son da yake ma zainab zai iya yarda da komai dan ya mallaketa, zainab ce kwance tana tunani tunda suka had'u da yazeed a hspt bata sake ganinsa ba, harya turo gidansu kuma ta amince gashi ko kiranta a waya bai taba yiba, tana cikin tunanin zarah ta shigo tace zainab tashi ki shirya zaki raka ni, amma fah kici gayu sannan kiyi sauri dan Allah, tace zarah ban son fita Wlh wani iri nake ji, zarah tace plz my little sister ba dadewa za muyi ba, zainab tace toh, zarah tace yauwa my little kiyi sauri, Bayan fitan zarah zainab ta tashi tayi dan normal makeup sannan ta fito, a falo taga zarah tace yauwa danje falon ba'ki ki kaimin drinks din nan Nayi baki, amsa tayi ta fita tana shiga sukai ido biyu ido ta zare alamun mamaki shiko murmushi yayi tare da fadin Barka da shigowa my hrt, cikin jin kunya ta ajiye tray din tare da zama a gefe tace sannu da zuwa amma baka kyauta min ba, yace mai Nayi? Tace bana son surprise visit, dariya yayi tare da fadin dan Zanzo wajan wife dina saina fad'a mata?  Itama d'an murmushin tayi tare da zuba mai drinks din tace bismillah, kallonta yayi tare da fadin nifa nayi alkawarin matata zata dinga bani abinci, cikin jin kunya tace ai matarka kace Dan haka saika bari a d'aura koh? Murmushi yayi tare da fadin my luv baki da dama sunyi fira Sosai wanda duk yawancin firan akan yanda bikin nasu zai kasance ne, koda zai tafi ledan waya Ya bata tace waya kuma Bayan Wanda ka bani, yace wancan dana baki na nagani Ina so ne wannan kuma Na amsan soyayyata da akayi ne dariya tayi tare dayi mishi godiya tace na aure kuma fah tana fadin haka ta shige Gida da gudu, dariya yayi tare da fadin komai kikai yana miki kyau zainab motarshi ya shiga yaja yabar gidan, zainab koda ta shiga d'akin zarah tayi dan tasan suna ciki, aiko tana shiga ta gansu khairat ta amshi wayan tace wow iPhone, aysha ce ta shigo da sauri tace zarah naji binta da yasmin suna magana Wai duk da sun bar maraba faruk ya canza musu Gida amma wani d'an iska nason tauna musu asiri, zaman gidan karuwai ai baiyi ba ko wani shege ya gaya maka magana amma nan gidan komai yi mana ake kai zaman gidan masu kudi akwai dadi, aysha tace Ina jin iya nan nabar wajan, zainab tace kenan yasmin karuwa ce Anya binta mamanta ce kuwa? Tace zarah nayi alkawari Kafin auren mu nida aysha saina gano ko miye kenan faruk yasan komai, zarah tace bake  d'aya ba har damu koma miye daka gobe zamu fara......






     *vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now