43

572 44 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 43




Murmushi ya sakar mata, sannan yace plz ina son magana dake, fita yayi ta bishi har motanshi, Bayan ta zauna tana dan rawan sanyi domin har yanzu ruwa akeyi, ganin tana ruwan sanyi yasa ya dauko dadduma a Bayan motar ya rufeta dashi, magana ya fara kaman haka rahma tun sanda na had'u dake nake jin wani abu a tare dake Wanda sai daka baya na gane sonki ne ya kamani, ba rayuwanki na baya nake soba wannan kuma bai dameni ba a yanda kike yanzu na ganki kuma nake sonki bai dameni ba dan baki karatun boko ba, ni rahma nake so ba komai ba, murmushi ta saki Wanda bata san tayi ba, ido ya kura mata Wanda itama ta d'ago dakai jin yayi shuru suka had'a ido, sunyi wajan minti d'aya suna kallon juna sannan yace rahma iyayena burinsu kullum inyi aure, amma ban sami wacce nake soba sai yanzu, yace mahaifiyata ta rasu wajan shekara uku da suka wuce, tunda ta rasu mahaifina bai kara aure ba har yanzu tun Bayan rasuwan mahaifina nike kula da kasuwancin shi domin nine kadai d'a  d'aya tilo daya mallaka, kullum burinshi inyi aure yau Idan na bashi Labarin na samu Mata Nasan sai yafi kowa murna, murmushi tayi yace Toh na samu karbuwa? Fuska ta rufe tana dariya, yace fad'amin mana plz plz, kin magana tayi ganin shima yayi shuru yasa ta cire hannunta a fuska tare da kallonshi caraf suka had'a ido, saurin kawar da fuskanta tayi dariya yayi Sosai tare da fad'in kina da kyau rahma, a hankali ta furta dare yayi gashi zakai tafiya Mai nisa kuma ana ruwa, ya kamata ka wuce, murmushi yayi yace a nan zan kwana, ido ta bude alaman tsoro tace kabar wasa dan Allah ka wuce, murmushi yayi tare da fad'in ok sai yaushe kuma?  Tace gobe zamu koma kaduna sai dai muyi waya kawai, yace karfe nawa zaku tafi? Tace kaman 10 yace OK Allah ya kaimu za muyi waya, tace OK fita yayi ya rakata har ciki sannan ya koma ya shiga motarshi yaja dan tafiya Kano.



Kaman yanda yace wajan tara sun gama shiri, suna cikin fito da kaya saiga Alh mahmud da security dinshi, gaida Haulat yayi ta amsa cikin fara'a sannan suka gaisa dasu zarah, ido suka had'a da rahma ya kashe mata ido d'aya, murmushi tayi tare da kawar dakai, kallon Haulat yayi tare da fad'in aunty za'a gina ajizuwa inaso harda secondary Ayi tun daka primary har secondary school, sannan za'a saka malamai, Haulat hawaye ta Fara tare da saka mishi albarka, Suma su zarah godiya sukai tamai tare da taya Haulat murna, mota d'aya ya ware yace su zarah a ciki zasu koma, yasa driver ya kaisu cikin jeep Mai baya biyu kaman cikin seeyana haka jeep din yake ga AC, Bayan an gama saka musu kaya a mota suka shiga ciki amma banda Rahma dake tsaye kusa dashi kallonta yayi yace Zanzo cikin week din nan Dan Ayi maganan auren mu, dan bazan iya Bari ya dad'e ba Kar wani ya kwace min ke, murmushi tayi tare da fad'in ni taka ce, tana fad'in haka ta shige mota da sauri, shikam nanata Kalman data fad'a yaita yi yana murmushi haka suka wuce.




Su ummi na falo suna fira Wanda jiran yaran nasu kawai suke, sai gasu kaman daka sama, da sauri suka nufi iyayen nasu suna murna, gaida iyayensu sukayi cikin farin ciki, nan suka zauna a falo Anata fira, zarah tace ummi Ina farida? Ummi tace tana d'aki kaman bacci takeyi, haka suka ci gaba da fita har suka nufi dinning kowa yaci abinci, nan khairat ta Fara basu Labarin soyayya alh Mahmud da rahma, hindu dake zaune ta kalli khairat tace Kai wannan Labarin ni har naji wani iri yanzu kanwarki sai ace ta rigaki aure gaskiya ya kamata Kema ki kawo naki mijin, khairat barin wajan tayi da sauri tana kuka, hindu jin kowa yayi shuru tace maina fad'a mara kyau a nan? Gaskiya Aina fad'a, duka yaran barin wajan sukayi aka bar Amina da hindu sai ummi, d'akin khairat suka shiga wacce take kuka, wajanta suka nufa Zainab tace haba khairat miye abun kuka? Kiyi hakuri karki d'auki maganan Anty hindu da zafi, Khairat cikin kuka tace zainab abunda Anty hindu tace gaskiya ne, nima Ina son inyi aure bani na hana miji zuwa min ba, zarah tace toh Kema Kinji abunda kika fad'a koh, dan haka ki d'auka komai lokaci ne, haka sukai ta rarrashinta har farida itama tazo ta samesu a haka.



Kullum rahma da Mahmud suna nan manne da waya koda yaushe, yauma dai suna falo Su duka ana fira kiranshi ya shigo cikin wayanta amma taki d'auka haka yaita kira taki d'auka, Amina dake zaune kusa da zarah ta kalli zarah tace dan Allah kusa a sako faruk tunda bashi yayi kisan ba, Kafin zarah tayi magana mama cikin fushi tace Amina karki kara fad'in irin wannan maganan, zata kara magana mama ta dakatar da ita, rahma cikin jin takaicin abunda mahaifiyarta ta fad'a yasa ta tashi tabar falon, d'akinta ta shiga bata dad'e da shiga ba saiga khairat ta shigo ta mi'ka mata waya tare da fad'in Mahmud yana ta kira kinki d'auka gashi ya kira a tawa wayar, amsa rahma tayi tare da fad'in hello, jin muryanta da yayi yace waya bata miki rai? Tace babu kowa, yace Mai yasa kike fushi toh? Tace ba fushi nakeyi ba, murmushi yayi tare da fad'in rahma muryanki kawai naji na gane ranki a bace yake, shuru tayi ba tare da tace komai ba, yaci gaba da fad'in ban San inga kina fushi haka yaita janta da fira na soyayya harta manta da komai taji ranta ya saki, inda yake fad'a mata cikin week dinnan yana nan tafe dan yayi kewarta, murmushi tayi tare da fad'in Allah ya kawo ka lafiya.



Kaman yanda Alh Mahmud yace hakan koh akayi sai gashi yazo cikin satin, a gidanshi dake kaduna ya sauka, Washe gari yazo gidansu rahma koda yazo ba ita ya nema ba, gunsu ummi yazo ya gaidasu, nan rahma da y'an uwanta suka cika Mai gaba da kayan ciye ciye amma shi kam idanshi nakan rahma wacce yaga ta kara yi mishi kyau Sosai, su mama sun yaba da hankalinshi Sosai sannan sunyi mishi y'an tambayoyi inda Ya basu amsa cikin nutsuwa, yace zai turo magabatanshi suzo neman auren rahma, su mama cikin jin dad'i suka ce babu damuwa tunda har ta yarda kazo Nasan Kun fahimci juna, rahma ce ta tashi tare da fad'in mama bana son wannan auren, kowa dake wajan kallon mamaki yake mata musamman alh Mahmud da lokaci d'aya yana yinshi ya canza......







     *vote*
*Comment nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now