33

478 35 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 33




Magajiya da Aneesa ne zaune a falo suna fira, saiga Abubakar nan yazo wucewa, Aneesa ta bishi da ido tare da fad'in oh magajiya namiji har namiji amma bashi dako sisi, ya kasa tsinana ma matarshi komai, Abubakar yasan dashi take dan haka ya girgiza kai tare da d'an murmushi ya fita ba tare daya ko kalleta ba, Aneesa cikin ranta tace shi wannan wato ya maidani mahaukaciya kenan zanyi maganinsa.


Abubakar yana zaune a office saiga police nan sun shigo cikin office dinshi Wai zasu bincike an sace kud'i har naira million biyar a company din, Abubakar Yace OK Toh ku duba, Aneesa ce tazo itama cikin office din nan gabanshi ya fad'i tare da tsoran Kar ace ta kulla mishi wani Abun aiko yana cikin tunanin yaji ana fad'in ga kud'in nan, da sauri ya dawo cikin hayyacinshi tare da rudewa yana fad'in Wlh ban d'auka ba,  Aneesa tace in baka d'auka ba Mai yasa ba'a gani office din kowa ba sai naka? Shuru Abubakar yayi dan yasan bamai fitar dashi sai Allah kuma wannan shairin aneesa ne, dan Haka yasa yayi shuru ta kalli police din tace ku tafi dashi, haka aka tafi da Abubakar tana ta murmushi yana kallonta, koda labari yakai masu zarah cikin tashin hankali suka nufi station din, amma police sunce bazasu ganshi ba dakyar suka yarda suka basu minti uku su ganshi, Bayan zarah ta isa inda yake tace maiya faru Abubakar Nasan wannan shairin Aneesa ne amma karka damu za muyi billing dinka, yace Aneesa makira ce amma babu komai abunta zai koma kanta insha Allah, wani police ne yazo yace ma zarah ta fito lokaci yayi, haka ta fita Tana kuka, inda sukai ma police magana akan belling suka ce Indai zasu belling dinshi sai sun bada dubu d'ari uku, zarah ta zaro ido domin basu da dubu d'ari uku duk wasu kud'in su a acct din Abba suke sawa gashi kuma yanzu komai na wajan Aneesa, haka suka fito jiki a sanyaye suka koma Gida, suna shiga Aneesa ta Fara bala'i wai ina suka je basu gama Mata aiki ba, zarah ta nufeta tana kuka tare da fad'in Aneesa dan Allah kisa a saki Abubakar Nasan bai d'auki kud'in ba, Aneesa ko kallonta batayi ba saima kiran Sunan magajiya da tayi tana tambayanta akan sarkan data siyo koh tayi kyau, rahma da ranta ya baci ta matsa kusa da Aneesa tace Aneesa tunda na taso ban taba ro'kan wani abu wajan kowa ba dan Allah kiyi hakuri ki saka a sako shi, Aneesa ta daka mata tsawa tare da fadin kar in kara jin wani ya furta min wata magana maza kuje kuyi min aiki khairat kawo min coffee, zarah cikin kuka take kara bata hakuri akan tasa a sakar mata miji, rahma tace zarah kibar ro'kanta domin rashin imaninta bazai sa tasa a sa'ko shiba, kin San bata san miye so ba tunda a titi ta taso Aneesa ta d'aga hannu zata Mari rahma da sauri rahma ta ri'ke hannun tare da fadin  karki sake ki fara duk wannan Abun da kike bazan kara dauka ba, Aneesa tace sake min hannu karki manta nan gida nane komai nace shi za'ayi in kuma kina son zama cikin sa dole kiyi, rahma ta sakar mata hannu tare da fad'in baki isa ba babu wani abunda zaki kara Sani inyi domin yau zanbar gidan nan bazan ci gaba da zama a karkashin wacce bata san abunda take ba mara imani Mai zuciyar kafirai tana gama fad'in haka ta haura Sama inda suke kwana ta kwaso kayanta Amina tace rahma Ina kike kokarin zuwa? Y'an uwanta mata suka tareta tace dukanku bazanji maganan kowa ba yau zan bar gidan nan tana fad'in hakan ta fita cikin fushi Aneesa tace duk Wanda bazai yi abunda nake so ba ya bita tana fadin haka suka haura ita da magajiya, Amina cikin damuwa itama tayi d'akinta domin ita har yanzu a d'akinta take kwana, su khairat da sukai jigum suna jimami yanzu Ina rahma zata tafi? Ina zata wata sani? Wannan tunanin suke tayi, ita kam zarah abubuwa sun taru sun mata yawa tama rasa abunyi na farko ga mijinta a station babu kud'in billing ga rahma tabar gida wanda basu San inda zata ba, gaba d'aya komai ya had'u ya jagule mata wani irin hawaye ne ya silalo mata Mai zafin gaske, zainab da cikinta yake ta girma ta karaso dakyar tana fad'in zarah kiyi hakuri insha Allah zai fito, zarah tace zainab rahma ta tafi ko Ina zata oho, yanzu itama ta gujemu kenan Wlh Ina takaicin abunda tayi, khairat dake gefe tace zarah kiyi mata hakuri hala akwai manufar yin haka ne, zarah bata kara cewa komai ba ta tashi ta had'a kayan wanke wanke ta nufi waje danta wanke.



Zarah duk ta rame tayi duhu ba komai yasa Mata haka ba sai damuwa, Ummi ce ta shigo ta sameta tana Shara a kitchen ummi cikin tausayin y'ar tata ta kira sunanta, tare da fad'in zarah, d'agowa tayi ta kalli ummi tare da fad'in na'am ummi, Ummi ta ciro kud'i a Leda tare da mi'ka ma zarah tace gashi kije kiyi billing din mijinki, cikin jin dad'i tace ummi Ina kika sami kud'i haka? Ummi tace Abun hannun da mahaifinku ya sai min Kafin ya rasu Shina saida, zarah cikin kuka tace ummi Mai yasa kika saida Bayan Abba ne ya siya miki? Tace zarah bazan iya kallonki haka ba ina shiga damuwa Sosai zarah ta rungume ummi tana fad'in nagode ummi Allah ya biyaki, suna cikin haka saiga Aneesa ta shigo ta fisge kud'in a hannun zarah da sauri suka waiga suna kallonta dan basu ga shigowanta ba sai dai ganin kwace kud'in da tayi, zarah tace Aneesa miye haka bani kud'in, zarah tace komai dake cikin gidan nan ba naku bane nawa ne harta kayan da kuke sawa dan haka bazan bada kud'in ba Tana fad'in haka ta fita tabar kitchen din.....






     *vote*
*comment nd share*

*maryam obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAOnde histórias criam vida. Descubra agora