28

484 39 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 29




Faruk tuki yake yana tunanin mai zai fad'ama Abba Idan akaje banki akaga bai sa kud'i ba, haka yaita tunani harya karasa gida, koda ya shiga gidan d'akinshi ya nufa inda Ya sami farida zaune ta zabga uban tagumi, kallo d'aya ya mata yaga ta rame tayi d'an duhu, abunda yake kanshi a halin yanzu yafi karfinshi dan haka ba tare da tambaya ba ya sami waje ya zauna, ganin ya zauna yasa ta nufeshi tare da kiran sunanshi tace faruk na maka wani laifi ne? Dan Allah Idan Nayi maka laifi kayi hakuri Wlh rashin bani lokacinka yana sakani shiga cikin wani hali, faruk ko dan ban haiyu bane har yanzu yasa kake canza min? Kallonta yayi sannan yace farida plz ina bukatar hutu yanzu bana son damuwa, jin haka yasa wani hawaye Mai zafi ya zubo mata da sauri takai hannu zata goge dan karya gani, amma ya riga ya gani da sauri ya tashi tare da riqe hannun nata yasa nashi ya goge mata, yace farida bakimin komai ba, kawai Ina damuwa ne akan yarona shi yasa gashi Abba yasa yayi nisa dani, farida tace abunda Aneesa tayi shi yasa Abba ya koreta amma insha Allah komai zai daidaita, yace Ina fatan haka, farida zama tayi tana tunani tare da ro'kan Allah akan ya bata ciki itama,.



Alh Ibrahim ya tura aje a ciro kud'i akace babu kud'i, Abubakar ya kira yace yaba faruk yakai, koda alh Ibrahim ya tambayi faruk kasa magana yayi saida yaga alh Ibrahim yayi fushi Sosai sannan ya fara bashi hakuri tare da fad'a mishi Abun da yayi da kud'in, ran alh Ibrahim ya baci Sosai inda yace a ina ya siyan musu gidan? Fad'a mishi yayi, ranan alh Ibrahim daka office direct gidan ya nufa inda Ya samesu ita da magajiya suna fira, basu ga shigowanshi ba sai ganin shi sukai da yaro, da sauri suka tashi ya kalli Aneesa yace saboda wannan yaron kike bata ma d'ana tunani, toh daka yau zai koma gidana Aneesa kasa magana tayi har Alh Ibrahim Ya fita, sai a sannan ta bishi da gudu amma Kafin ta karasa ya shiga mota ya tafi, ihu ta saki tare da komawa gidan da gudu ta dauki wayanta ta kira faruk amma bai d'auka ba haka taita kiranshi bai dauka ba, jifa tayi da wayan, alh Ibrahim gida ya nufa da yaron kowa tashi yayi yana kallonsa domin abun ya basu mamaki,kwala ma faruk kira yayi wanda yasa ya fito da sauri shima ganin yaron yasa mamaki ya kamashi, alh Ibrahim mi'ka Mai yaron yayi yace saboda d'anka kuma jikana kake mu'amala da Aneesa har take kokarin canzaka Toh gashi nan daka yau ya dawo nan kenan, sannan tana kokarin ta nuna kaiba d'ana bane inna mutu baka da gado, bari kaji tun ranan da naji kuna magana harna koreta duka dukiyata Nayi signing ya koma naka dan nasan ko Bayan Raina zaka ri'ke iyalina, kuka faruk ya fara yana bashi hakuri akan ya yafe mishi, alh Ibrahim yace babu komai, daukan yaron yayi yai sama dashi dan yakai ma Farida sannan ya kara Aneesa yaji ya hakan ta faru, mama ta kalli alh Ibrahim tace Anya abunda kayi kana ganin shine dai dai kuwa? Alh Ibrahim yace name mama? Tace Taya zaka mallaka mishi dukiyarka duka yaranka fah, murmushi yayi tare da fad'in mama ina sane dasu ban manta dasu ba, mama Ina son y'ay'a na Sosai yanda bakya zato bazan taba yi musu abunda zai cutar dasu ba, na tabbata koda Bayan raina faruk zai kula dasu Sosai bazai Bari susha wahalan rayuwa ba, mama tace toh Allah ya taimaka ya amsa da Ameen tare da tashi ya haura sama, koda faruk ya haura yaga misscall din Aneesa da yawa kiranta yayi ta dauka cikin kuka take mishi bayani hakuri yaita bata akan gobe zai kawo mata yaron tare da fad'a mata kyautar da alh Ibrahim yayi mishi inya mutu, sallama sukai akan gobe zai zo.



Washe gari kaman yanda faruk ya fad'a haka Ya shirya shida yaron ya fita, alh Ibrahim da tun jiya yaji wayan da yakeyi yasa ya bishi a baya, wani waje ya nufa inda ake Gina gada amma ba'a gama ba motoci basa bi, a nan suka had'u da Aneesa da magajiya inda Ya bata yaron tana ta murna ganin alh Ibrahim ne yasa duka sukai shock, domin basu zata ba, alh Ibrahim yace faruk ban zaci haka daka gareka ba Banyi zaton zaka bijire ma magana taba, tun jiya da naji kana waya na canza ra'ayi a kanka na fasa mallaka......  Faruk yace abba kayi hakuri tare da matsowa kusa dashi yana zuwa alh Ibrahim ya wankeshi da Mari alh Ibrahim yana kokarin matsawa aiko ya fad'a amma Allah ya soshi  ya riqe wani karfe magajiya da Aneesa suka saki baki faruk da sauri ya riqeshi yana kokarin ya janyoshi amma ina ya kasa alh Ibrahim ya fad'o daka katuwar gada Mai nisa Sosai, faruk kuka ya saki Aneesa tace faruk ka kashe mahaifinka da kanka zo mubar nan wajan, faruk babu abunda yake sai kuka ya kasa ko motsi dakyar Aneesa taja shi suka bar wajan cikin sauri...





     *vote*
*comment nd share*

*maryam obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now