15

731 46 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 16




Magajiya ce ta cinye abincin ita kam Aneesa sai Maltina tasha, shima tana gama sha ta Fara amai kaman zata fitar da hanjin cikinta, magajiya sai faman sannu take mata, ganin yanda tayi amai din Sosai gashi ta kasa cin komai yasa magajiya tace kota kira faruk ne? Kai ta girgiza alaman a'a tace bari sai munje mun tabbatar da ciki gareni sai inyi magana dashi, magajiya tace toh kodai zamu yanzu ne? Aneesa tace gobe da safe zamu ranan dai bacci rabi da rabi Aneesa tayi na farko ga daukin taga gari ya Waye taje asibiti na biyu jikinta baya mata dadi haka dai har gari Ya Waye suka nufi asibiti, koda tayi ma Dr bayani ya tambayeta taci wani abu?  Tace a'a scan yayi mata saida ya gama yace madam congratulations kina da cikin wata d'aya da sati biyu, wani irin ihu ta saki na murna Dr yanda yaji tayi ihun saita bashi dariya, Dr Ya bata magani tare da fada mata saita dinga kula, godiya suka mai sannan suka wuce, suna tafiya Aneesa na fadin magajiya yau nafi kowa murna nice da ciki Kai Alhmdlh wannan cikin nawa shine jarina shine silan samun arzikin mu, dariya magajiya tayi tare da fadin wannan haka yake, suna tafiya taga mai waina saida ta tsaya suka siya ita sai magajiya tace baza taci ba abincin hotel za taci🤣



Alh Ibrahim ne zaune da iyalan gidanshi suna cin breakfast, Bayan an kammala ya kalli ummi yace ya kamata ku Fara siyayya,ummi tace hakane naji dama bakai magana ba, yace anjima inna fita office zan turo faruk da kudi Ya kawo sai kusan abunda zaku fara siya sannan in zaku kuje da Yaran Su zabi abunda suke so, Amina tace ni kam wani siyayya za'ayi tunda naga ita zainab a nan zasu zauna sai dai ita aysha din, Abba yace hakane amma ai a canza ma zainab din kayan d'akinta koh? Amina ta tabe baki tare daci gaba da cin abincin ta, tashi Alh Ibrahim yayi suka fita shida Abubakar da faruk dan tafiya office, koda suka fita faruk yaso ya zarce wajan Aneesa amma babu dama haka ya hakura dole akan in sun tashi daka office, Bayan sunje office baiyi ko awa biyu ba Alh Ibrahim ya bashi check yace yaje bank ya ciro saiya kaima ummi, hakan ko yayi saida ya fara zuwa bank sannan ya wuce hotel din daya sauke su magajiya, koda yaje magajiya ce ta bude mishi kofa, a kwance ya sami gimbiyar tana wani kashe ido irin nasu Na yan duniya, kallonta yayi yace baki da lafiya ne?  Mai makon ta bashi amsa sai ta kanne mai ido d'aya lokaci daya jikinshi ya fara amsawa amma saiya dake tunda magajiya na wajan, yace Aneesa kiyi magana mana maike damunki? Kuka ta saki ta Fara fadin yanzu faruk duk da nayi aure Allah ya shirya ni sai Ayi ta bina da shairi, ban taba tunanin mahaifinka zai min haka ba, Idan da nayi rayuwa mai muni yanzu ai na shiryu tunda na daina, amma saida yasa ka sakeni, gashi yanzu Ina da ciki dole zubarwa zanyi tun....... Yace ciki Aneesa kina nufin kina da ciki ciki na?  Kai ta d'aga tare da fadin hakane amma zan zubar dashi Dan zan koma rayuwa ta tabaya tunda mahaifinka baya bukata ta Kaga kam bazai so had'a zuri 'a dani ba, faruk yace haba Aneesa har gobe Ina sonki sannan karki kuskura ki zubar min da ciki kiyi hakuri kiban lokaci kad'an komai zai daidaita, sannan zan siya muku Gida koda karami ne Kafin musan Abun yi, cikin kukanta na makirci tace a'a ka barshi kawai zamu nema da kanmu, yace Aneesa plz kibar wannan maganan zuwa gobe ko jibi insha Allah zamu sami Gida koda haya ne Kafin Abba ya sauko, tace toh shikenan, kudi Ya dauka ya kara basu tare da fadin zai kara biyan kudin d'akin sannan yace mata in zai dawo mai zai kawo mata, tace ice cream yace shi kawai? tace eh sallama ya musu ya fita saida Ya biya kudin d'aki na sati daya sannan ya nufi Gida inda yakai ma ummi kudin ya koma office cike da farin ciki zai zama uba shima.



Anata hidiman bikin su zainab, amare suna tashan gyara Sosai duk inda suka gifta sai kaji kamshi domin wata mata hindu ta tauko musu daka borno take musu gyaran jiki ciki da waje, zainab na kwance wayanta yayi kara dauka tayi dan tasan mai kiran domin ringing dinshi daban ta ware mai, dauka tayi tare da sawa a kunne tayi shuru, cikin muryansa mai dadin ji yace baby yakike? Bata amsa ba sai dariya da take kunshewa, yace hello, uhm tace murmushi yayi tare da fadin yau sarautan ya tashi kenan?  Murmushi tayi tare da fadin ka taba jin dan Talaka da sarauta ai sarauta sai wanda ya gada, yace aike a cikin zuciya ta kinfi mai sarauta mulki ni bawanki ne Kece sarauniya ta, zainab na rasa mai yasa nake sonki da yawa, da zan iya nuna miki irin son da nake miki da Kinji tausayi na koda sau daya kince min I love you yazeed, dariya tayi Sosai yace eh mana baki taba cemin I love you ba fah, tace Kai haba? Yace dagaske mana, dariya tayi sannan tace uhm, yace plz say it, tace a'a yace shikenan nan da kwana biyar zan saka ki kice min ai, uhm tace sannan tace taya zan ce maka? Yace sanda akace an daura min ke kin zama matata a ranan zan saka ki kice, bama sai nace kice ba da kanki zaki cemin, tace ni kam bazan ceba, dariya yayi yace ni kam Nayi alkawari sai kin fad'a min haka, canza maganan yayi da fadin an dai hanani ganin matata koh ance Kar in kara zuwa sai ranan da aka kawo ki, Wai miye sirrin Abun ne? Nifa a matse nake ina bukatar ganin ki, tace ba yanzu ba dole hakurin za kayi, yace Anya zan iya kuwa? Murmushi tayi tare da fadin saura kwana nawa Ya rage ka ganni in kayi hakuri kaman yanzu ne fah, yace hakane, tare da fadin anjima zan aiko a kawo miki sa'ko sai Ayi min Lalle da kitso mai kyau, kashe wayan tayi tana dariya, saida tayi mai isarta sannan ta fita zuwa d'akin khairat Dan daka yau can zata koma kwana dan za'a kawo kayan d'aki yau, cikin d'akin khairat ta sami yan uwan nata suna ta tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, sun dade suna ta tsara yanda za suyi hidiman bikin, wayan zainab yayi kara dauka tayi dan tasan ko Waye, yace kisa aje waje a anso miki sa'kon Kar kije da kanki Dan ban yarda a ganki ba, dariya tayi tare da fadin Toh, kashe wayan tayi sannan ta kalli khairat tace danje waje ki amso min sa'ko, khairat ta amsa da Toh sannan ta fita, bata dade ba sai gata ta dawo da akwati trolley ajiye ma zainab din tayi, Bayan ta ajiye zainab ta bude kudi ne masu yawa da d'an kunne da sarka Na zinari sai kaya Kala biyu masu tsadan gaske duka dinkunan gown ne kayan kana gani kasan na event ne, wanda bridal zata saka, kiranta yayi ta dauka tare da barin d'akin dan yan uwan nata suna ta magana akan haduwan kayan, Bayan ta fita suna magana yace kayan shi zata saka in za suyi mothers day dayan kuma ranan bridal shower, yace plz tasa kayan Dan yasan may be anyi mata Wanda zata saka a gidansu, mum dinshi ce ta bada a kawo mata kayan, dan tace baza a sasu a akwati ba wannan kyautar tace ta musamman, zainab tace Allah sarki mum dina plz ka tayani godiya Sosai a wajanta, yace zan fad'a mata sunyi d'an fira kadan sannan sukai sallama, koda ummi taga kayan tace su zata saka da event, ummi tace kudin naira million uku ne tace sai Asa a account domin wata rana zaiyi amfani hakan ko akayi.



An fara hidiman biki an kawo akwati ko wacce guda 6, an cika su da kaya makil, yau za Ayi mothers day, amare anyi musu kwalliya na Kece raini Kalan kayan da yazeed Ya kawo ma zainab shi jamil ya kaima aysha Dan haka anko sukayi sai dai colour din daya banbanta, mother day din ya hadu an kashe naira Alh Ibrahim yayi bazata domin ya bada kudi Sosai a bikin, Washe gari kuma akai bridal shower, shi wannan kawayen amare ne kawai sukayi, Anci ansha taro ya watse, yau Friday aka daura auren jamil da aysha sai yazeed da zainab akan sadaki naira dubu d'ari d'ari, Anci taron biki wajan 7 aka tafi da aysha malali amma ba'a nan zata zauna ba gidan mijinta na katsina inda iyayenshi ke zaune amma sukan zo jefi jefi kaduna, za su danci amarci ne anan Kafin su tafi can, yazeed kam abokananshi ne suka kawo shi inda suka musu yar nasiha sannan suka fita, ya rage daka zainab sai yazeed.....  Muje zuwa muga ya abubuwa zasu kaya cikin gidan Alh Ibrahim yanzu.








     *vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ